← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai a wannan karan ta kalleni kafin ta ce"idan ban sani ba sai nace Soyayya ku ke, dan yadda yaya yake kallanki wallahi sai wani ya rantse soyayya kuke ke da shi"dariya ta sake fashewa da shi tana mai faÉ—in baza ta iya misaltawa ba kafin ta ja hannuna muka shiga ciki bayan ta shaida mun Ene bata nan.Kallan É—akin nata nayi ganin yadda aka canza komai,kamar ta fahimci kallon da nake ta zauna gefen gadonta tana mai cewa:

"Kina kallon sabon design É—in É—akina hala?wallahi Yaya Halil ya canza mun komai,zo muje ki ga cikin wardrobe É—in har da kaya".

Fito da kayayyakin ta fara tana mai nuna mun,sunyi kyau sosai haka nan sai na jini cikin farin ciki kamar ni aka sauyawa kaya,ɗayan wardrobe ɗin ta buɗe tana mai cewa "ga nan waɗancan har da wanda sawa ɗaya nayi mishi,kin sanni bana da yawan maimaita kaya,har Enen ta ce za a fita dasu a kai gidan Marayu na ce ta aje Zunairah ta zo sai ta zaɓa".

Wani irin zafi na ji a ƙirjina lokacin da ta faɗi maganar amma na danne ɓaccin raina na yi faɗa da shaiɗan ɗin da yake san hassalani na gwasile Alherinta,cikin mutunci na ce"aikuwa da kin bar Enen ta kai kayan nan gidan Marayu dan ba zan ɗiba ba , besides ai kin san cewa jikina da naki ba iri ɗaya bane".

Kallo na tayi na daƙika kana ta ce"hope ba ɓata Miki rai nayi ba,I'm sorry ni wallahi ba da wani abu na ce ba,zo ki zaɓa cikin sabon ma dama inda da niyyar ɗiba miki wasu".ta ƙarasa zancen tana mai aje doguwar rigar da ta ɗauko tana buɗa mun ta nufi sashen sababbin,dariya reaction ɗinta ya bani, kafaɗarta na kama na juyo da ita ina mai faɗin"Ani I mean it ba zan karɓi kayan ki ba,and ba wai na ɗauki maganar da wani abu ba,kyauta ce fa ki ka mun ta hanyar san Faranta mun, it's just that kada ki manta kin fini jiki na fiki tsayi,Kinga kuwa kayan ki ba za su mun ba,yanzu bama wannan ba ya jikin ki mene yake damunki?kin san yadda ki ka tada mun hankali kuwa?mama na ta mun faɗa wai ban tsaya na ji mene yake damunki ba tun a waya".

"Okay fine kin yi winning,jiki na da sauƙi,dama ƙoda ne ta sani gaba but I'm okay, although abun ba daɗi kwana biyu ɗin chan but yanzu ba Matsala,bari ki ga gifts ɗin da Khalifa ya kawo mun"ta ƙarasa maganar tana mai kwace hannunta daga nawa ta nufi ɗaya gefen wardrobe.

Shan gabanta nayi cike da tashin hankali"ciwan ƙoda Anisa har ki kwanta asibiti amma ki kasa faɗa mun?rabu dani da wasu gifts abeg ya ki ke yanzu,ya jikin ?".

"Stop being a drama Queen best friend,I'm okay and ni na hana Enen faɗa Muku,kin san na fi so a ganni a best halittana."kamo hannuna tayi wanda Idanunta suka sauka akai,cike da tsantsan Mamakin da bata yi yunƙuri wajen ɓoyewa ba ta ce"wane ya baki wannan zoben mai shegen tsada da aka yi engraving sunanki ciki piece of diamond?".

"Diamond kuma?ba dai diamond ba".na faɗa ina mai mayar da hannun baya,kamo hannun tayi tana mai sake kalla lokaci guda kuma tana san cirewa daga hannuna wanda ban ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ban bari ta cire ba,amma fa jikina ya yi sanyi,wai diamond menene haɗin Zunairah da diamond?""

"Wallahi diamond Zunairah,zan kasa gane diamond ne ko zan Miki ƙarya?Wane ya baki?ina ki ka samu? Mu gani dan Allah".

Gyaran murya nayi ƙarama kana na ce"zoben Alƙawari ne ,saurayina da nayi ya bani although da na san diamond ne ba zan karɓa ba"take ta rikice tana mai sake tambayata cikin ƙaguwa,wanene wannan guy ɗin?aikin mene yake,?,a ina ku ka haɗu da shi?,mene sunansa?,Dariya ta bani jin lokaci guda tana san sanin baki ɗaya Waɗannan informations ɗin a bakina,how wish zan iya faɗa mata,amma maganar zoben da ta tashi sai na ji ina san magana da shi kafin na sanar mata da yayanta ne dan haka na ce da ita zan sanar mata cikin ƙwanankin nan.

Duk yadda ta yi nacin san sanin wanene ban iya faɗa mata ba ,a haka ta haƙura tayi respecting decision ɗina kan idan na shirya na faɗa mata wannan saurayi da nake ta ɓoyewa ,fatanta ɗaya Allah yasa ba ɗan yankan kai bane , murmushi kawai na ɗinga yi,har na hango fuskarta lokacin da ta san Gaskiyar,duk da rashin sanin wanene ɗin bata ɓoye irin farincin da take tayani ba har tana tsokanata na fito daga kogin san Ma'aruf zuwa ga mysterious guy,cikin hirar da muke ne na ce"yauwa Anisa,so nake na ƙarɓi Draft na littafaina especially Love Scenery ɗin nan".

"Mene za ki yi da shi"ta tambaya tana mai nuna interest ɗin ta ,gyara zama nayi ina mai sake yashe baki "Kinga yanzu mun gama makaranta and ina da smartphone ina da laptop so nake na cigaba da rubutu a matsayin Career and Kinga Wannan Love Scenery ɗin?I was told zai karɓu sosai ".

"Inji wane ya ce Miki hakan,i mean beside me wane ya san da shi?".ido ta zuba mun tana neman jin amsata wanda ban ƙasa a gwiwa ba na bata Amsa"wata marubuciya na haɗu da ita mai kirki,ina yawan karanta books ɗin ta kwana biyu da na yi waya so sai na tambayeta shawara because sananniyace and litattafan ta na fita sosai a Ebooks tana samun kuɗi,so na bata labarin idea ɗin da nake da shi especially na Love Scenery and she told me idan na sake shi duniya zata so shi,and she will be there to Guide me,ba ki ji yadda na ji daɗi ba, Although da farko i was beyond Nervous amma yanzu kam ji nake kamar ban taɓa shiryawa ma Rubutu ba yadda na shirya karɓarsa yanzun,i want the world to hear me shi ya sa na zaɓi harshen Turanci duk da zan rubuta Hausan idan tafiya ta yi tafiya but yadda Hausa na bai goge ba ina san na ƙara gogewa duk da masu jin Hausa kawai ne zasu karanta ,but it will worth it dan akwai issue da nake san addressing wanda society ɗin mu yanzu ke fama da shi a hannu ɗaya muma Kinga mun zama Hausawan tunda muna cikin su".

"Kin zama dai amma ni Anisa har ƙwanan gobe Idoma na ke Ba abin da ya haɗani da Hausawa da issues ɗin su"ta yi saurin bani amsa.

Dariya na saka dan amsar nata ya bani dariya,"idan banda abin ki Anisa ai Hausawa sun mana rana tunda muka zo garin su muka Zauna,ki cire cewa Khalifa Yaren Margi ne either ways dukka Muna da matsalolinmu, idan kuma ki ka zauna ki ka duba sai ki ga abun kusan iri É—aya ne,duk yarukan da ke akwai idan mun yadda abu guda ne sai dai banbanci na Al'ada amma abubuwan da ke faruwa in circle guda É—aya ne a matsayin mu na mutane".

Taɓe baki tayi ta ce"ke dai ki ka jiyo,ni yanzu bama wannan ba drafts ɗin ki na littafi babu ko ɗaya da na san inda suke,but since kece ki ka rubuta I'm sure zaki sake har ma ki yi wanda ya fi wancan,i trust you,ko kuma ki sake labari because ba zan ɓoye Miki ba ba wani daɗi ya yi ba,don't take me wrong ita da tace ki rubutu ba karantawa ta yi ba,amma ni as a Bookworm na san irin littafan da ke ɗaukar hankalin masu karatu,Kinga Love Scenery ba zai taɓa ɗauka ba, besides yarinta ya yi yawa ciki which I can understand ya danganta da lokacin da ki ka rubuta shi,"

Shiru nayi ina nazarin maganarta,duk da ina san gamsuwa da batun nata amma sai na yanke shawara kawai zan rubuta shi ta wani salon na daban ba kamar new version ɗinsa tunda na riƙe labarin akai na,a haka ta bani ƙwarin gwiwa da tabbatar mun tana tare dani ɗari bisa ɗari.

Har nayi Haramar wucewa Enen bata dawo ba,na so na sameta mu gaisa ,riƙe jakana Anisa tayi tana mai shagwaɓe mun fuska kan na ƙwana bata gaji da ganina ba, dariya nayi na miƙa hannuna ina mai cewa"bani jakata tukunna"maƙe kafaɗa tayi kamar wata yarinya wanda yin hakan ya saka na ƙara darawa ina mai jinjina ƙarfin halinta,horn ɗin da aka yi daga Chan ya saka a tare muka kalli gurin kafin ta ce"Kinga mu je ya Sauke ki,yadda yake ta haɗe ran nan ba san kai ki ɗin yake ba,na fi tunanin ƙwarjini ki ka mishi wallahi".

Dariyata na ɓoye kafin muka taka ta rakani har bakin motar tana mai sake faɗin"yaya Halil kayi haƙuri dan Allah"ta bashi haƙurin nan ya fi irga, murmushi kawai nake ina mai hango abin da ni kaɗai nake gani a idanunsa.

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da muka fita daga cikin gidan,dariya na saka wanda ya rasa abin da zai ce mun illa tayani da ya shiga yi mun dariya.

"Wallahi za ka dace da actor irin wannan haɗe rai kamar mugembu ya ga Amitha,kai wai a dole an dameka kana hutawarka zaka ma ƙawar ƙanwa alfarma,okay oo in munje last bus stop sai ka aje ni kamar yadda ka ce da fari"na faɗa abin na sake bani Dariya.

"Baby you caused all this,ni kuma bana so a ce na Miki abin da baki so,i will respect your decision,idan da ace zan bi abin da nake so,da zan nunawa kowa ke tawa ce ,idan na fara rawar kai kam,hmm sai kin ce mun ya isa haka,yanzu dai bari na fara kai ki shopping ina san na fake da hakan nayi ta ganin fuskar ki".

Dubansa na yi kafin na ce "aikuwa baza ka kaini shopping ba plus dama ina san nayi da kai,mene ya saka ka siya mun expensive zobe, diamond for that matter?".

Dariya ya sa wanda na kasa gane ta menene kafin ya ce"baby is just a piece of diamond,after all Bama pure bane duka,ki yi addu'a na yi kuÉ—i sosai zan siya Miki abin da ya fi na hannunki don kin yi Worthing more than duk wani abun da ki ke tunani,dan Allah ki daina magana idan na yi Miki kyauta sai ina ji kamar ban iya ba".
Chapter 8 · 0% Book details