Sashe 20
Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Munsha kuka iya kuka,daga bisani Mama tace ai wannan kuka ba zai mana ba kowa yaje ya yi alwala ya yi Sallan Nafila ya faÉ—awa Ubangiji Mai kowa mai komai halin da muka faÉ—a duk da yana kallo kuma yanaji.
Da su Uncle Abdulbaƙi suka je duk yadda suka so basu dawo da Baba ba saboda yadda case ɗin ya yi girma dan ko ganinshi ba'a bari sunyi ba amma an faɗa musu abin da ya faru,lokacin da suka kama Baba sai ya bada number ɗin maƙocinsa Malam Bello wanda shi ya sanar da Uncle Abdulbaƙi abin da ke faruwa.
Dayake ƙwana biyu baya fita da mota ta samu Matsala sai yake hawa motar haya,to yana dawowa ranar sai ya ke dan rage ta daga gidan Gwamna duba da kuɗin dake jikinsa basu da yawa kafin ya hau abin hawa,kwasam sai yaga motar yan sanda har guda biyu sun kamo wasu a ciki suna bin wani dake ta tirƙar gudu kamar dai ƙwace musu ya yi,yana zuwa daidai saitin Baba suka cimmasa,Baba ya gama ruɗewa sai ya kasa gudu ya tsaya,ganin hakan ya saka wannan yaro da suke bi ya riƙe Baba Tsam yana faɗin "Oga ba haka muka yi da kai ba,kace duk rintsi baza ka bari a kamamu ba".
Still Baba ya yi a gurun yana kallon yaran da ke kallansa cikin ido yana faɗa mishi maganar da bai ma san ina ta dosa ba,kafin Baba ya farga sai gani ya yi shima an daɓa mishi anƙwa tare da wannan yaro,.wai sai da suka je CID yake jin wai barayin wayane da suka damu yankin Tarauni aka kama sannan a cewar barayin Babane shugaban su,idan sun saci wayar shi suke kaiwa ,shine yake saka su yana biyansu wani abun,kuma wai Baba ke basu Layar ɓata.
Abin Mamakin shine yadda duka yaran shida suka amsa sharrin na farkon akan abinda ya faÉ—a gaskiyane Baba ne ogansu,duka suka bada shaida guda É—aya,ba a fara tuhumar Baba da ya mutu a zaune sai da aka ciro abubuwan dake jikinsu na tsubu,wai sai cewa sukayi Baba duk ya basu.
Ɗaukar Baba akayi aka kai ɗakin DPO wanda yake san magana dashi ta san fahimta,suna so kada ya basu wahala suma kada su basu wahala a kaisu kuto a yanke musu hukunci,cike da rashin jin daɗin al'amarin DPO ɗin ya kalli Baba ya ce"Malam Buhari Muhammad daga kallonka dai kayi zubin mutane masu kamala na yi mamaki da ka saka kanka cikin irin wannan ƙazamar harkar,gaka dai aikin gwamnati ka ke yi gidan Gwamna ma amma kuma kana bada gudunmawa wajen ɓata mana tarbiyyan yara,saboda Allah yaran nan duk zaka haifesu amma ace kai kake goya musu baya wajen ganin ɓarna ta yaɗu?ka san yaran nan har kisa sunayi?ko da yake ai ba sai na tambayeka ba tunda kaine Uban gidansu,yanzu dai Bama wannan ba ka faɗa mun dalilin da ya saka kake goya musu baya ka ke saka su, bana san ta kaimu da sai an taɓa maka lafiya".
Kuka kawai Baba ya fashe dashi Yana sake jaddada musu Wallahi ƙarya suke mishi hasalima shi bai san waɗannan yaran ba".
Duk yadda suka bi da Baba maganarsa guda É—aya ce,hakan ya saka DPO sawa a É—auke Baba aje a bashi kashin tsiya,Allah sarki Babana,duk wannan Azabar bata saka ya amsa laifin da bashine ya yi ba,bayan sun masa matsiyacin duka har da karaya aka watsosa É—akin da aka kulle yaran cikin Azaba,yanaji É—aya daga cikinsu na cewa"Amma kamalu baka kyautawa tsohon nan ba,kalli yadda kwalawan nan suka mishi ragaraga fa".
"To Habu dan Allah idan kwalawan sun shigo kace sharri nayi mishi kagani,ka dai san Oga bamaiyi zai kuɓutar damu ko? to idan muka ambaci sunansa aka zo aka kamashi mu wanene zai cecemu?shi wannan tsoho Eh mai sunan Daraja Allah yayi zai ɓara gyaɗar da bai soya ba ya kuma fige kazar wahala,kaddarasa,idan za ka ja eh banƙareren bakinka ka ja ka yi shiru".
"Sai da kai mataimakin Oga,wanda ya bi wani bayanka Uwassa,Hubule na Atikar farm Centre mai shikafa da waken yan gata Allah wallahi "É—aya daga cikin yaran ya faÉ—a.
Ɗan sanda guda ɗayane ya leƙo ya ce"baza kuyi mana shiru ba ko ai mun saka ku?".
"Sai Oga,ka huce haka nan"cewar Habu,Baba yana jin su bai ma iya faÉ—in komai Azabar dake ratsa tsohon jikinsa kawai ta ishe sa.
Da safe Labari ke iske mu inda Malam Bello yace Mama tazo suje,suna maganar ne naji yana cewa Uncle Abdulbaƙi da ace wani babban zai shiga da abun yazo da sauƙi,da Mama suka wuce duk da Muna cikin tashin hankali haka nayi ta lallaɓa Su Hauwa'u suka wuce islamiyya duk yadda Hauwa'u ke nacin dan Allah kada na musu dole amma ganin rashin amfanin zaman da zamuyi mu haɗa kai muyi ta kuka gwara suje ɗin.
Bayan wucewarsu abin duniya ya isheni,wane muka sani mai kuÉ—i mukam?duk inda tunanina ya kai na rasa wane zan kamo,ina wannan tunanin Anisa ta faÉ—on mun,ko wanka banyi ba na doshi gidansu na san idan naje daddynta zai taimakawa Baba.
ð—–ð—œð—¡ ð——ð—¨ð—¡ð——ð—¨ð—¡ð—œð—¬ð—”
ð™²ðšŠðšžðšðš’ðš˜ðš—ðšŠðš›ðš¢ ðšðšŠðš•ðšŽ
Na
ð—”ð— ð—œð—¡ð—” ð—ð—”ð— ð—œð—Ÿ ð—”ð——ð—”ð— (chuchujay
EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ 15:
*ð˜¡ð˜œð˜•ð˜ˆð˜ð˜™ð˜ˆð˜*
Ganin nake kamar mai adaidaita sahun da na hau baya sauri,tsaki nayi har yafi a irga,tun yana tambayata lafiya ina ce mishi ƙalau har ya mun banza shima,daga gani na kaishi maƙura tsakin da nake ta bugawa,ban ji baƙin ciki ba sai da na sauka wai babu chanji.
Da mugun takaici nace "amma mai keke sai da na faÉ—a maka É—ari biyar ce a hannuna kafin na hau ko?".
"To Hajiya ki yi haƙuri a samu mana haba dan Allah,mutum ya yi ta tsaki kamar bashi da lafiya,Allah ya sa ba dani ki ke ba,yauwa abokina ɗan raba mun mana"ya maida zancensa kan ɗan uwansa mai adaidaita sahu,ni dai bance Mishi komai ba dan idan na biyesa ba ƙaramun faɗa za muyi ba a yanayin yadda nake jina,miƙomun chanji na ya yi yana mai cewa"Ƴar wahala".
Na gefen dana sauka ne ya ce "dan Allah bawan Allah mu wuce ke kuma kiyi haƙuri kada ki biyesa".
"Zaka samu daidai kai ne a gaba, wallahi"daga haka ban sake cewa wani abu ba na shiga layin su Anisa ,ni nake tafiya amma ji nake kamar ƙafafuna basu sauri duk irin saurin danake,sai da naje bakin gate ɗin gidansu sai ƙafafuna suka tsaya ,idan na shiga mene zan ce musu?after abin da Yaya Halil ya yi mun ya kamata ace nazo neman taimako su?take naji wasu hawaye sun fara zubar mun a kunci lokaci guda kuma maganar da mai Napep ɗin ya faɗa mun na ƴar wahala ya fara dawo mun,sai kawai naji maganar tayi mun wani ciwo da ta bada gudunmawa wajen sake fashewa da kuka na mara sauti,Aikuwa Ƴar wahalar ce ba komai ba,idan ba haka mene zai kawoni ƙofar gidansu Anisa neman taimako,ina self respect ɗin?
"Mene ake da self respect bayan wanda yake riƙe mun respect ɗin danake taƙama dashi yana chan a kulle akan tuhuma mafi muni da ƙasƙanci"ina tsayen nan ina so na ƙwanƙwasa aka buɗe,Yaya Halil ne ya fito bayansa biye da Wata mata da ba sai an faɗa mun matarsa bace,
Saurin matsawa nayi a kiɗime na ɗauke kaina ina jiran su wuce,tsaye yayi yana kallona,ganin yaƙi fita ya saka ta fito tana cewa"kaga malaika ne da ka Maƙale a gurin nan ko.."ɗaukewa maganar da take niyar yi tayi tana mai kallona kafin ta kallesa ganin ya yi mun ƙuri ya saka ta gano wacece ni,cike da sigar tambaya ta ce"Zunairah??"kallonta nayi a karo na farko ban dai amsa mata ba,Kama hannunta ya yi kamar wadda za tayi mun wani abu yana mai cewa"No Zainab bana san fitina".
"Aw fitina Halil?fitina?da wannan yarinyar ka ke cin amanata ko ?shegiya ki ke yawo da wani tsayi kamar daren mutuwa,to wallahi karya ki ke,yanzu ubanki ki ka zo yi gidan nan dan Uwar babanki,Shegu matsiyata masu bin maza har gidan iyayensu"
Rasa abin yi ya saka na fashe da kuka,na juya zan bar gurin ya rugo ya riƙe hannuna yana mai faɗin"mene yake damunki Zunairah?i can see it a idanunki wani abu na faruwa,menene ya faru? ".
Ƙokarin ƙwacewa nake ganin Zainab na faman huci,cikin rasa wani abu da Zanyi nace Mishi gurin Daddy nazo ni ba gurin ka nazo ba".
"Ka barni ni sai na tambayeta matsiyaciya yar iska".
Ganin ta sake tunkaroni ya saka ya mayar dani bayansa ,ban ƙokarin Matsawa ba kula da nayi kamar bata da hankali,hannuna ya kama yayi gidan dani yana mai ƙokarin tare Zainab daga tunkarata,gyalen jikinta ta cire ta ɗaura a ƙugu ,tana mai yin wani shewa,ganin haka ya saka muna zuwa ƙofar na shiga da gudu inda tayi wani kukan kura ta yo ƙofar gidan itama amma sai ya tareta cikin zafin Nama,da gudu na shiga gidan ko sallama banyi musu ba na banka cikin falon ina zazzare ido".
A tare suka taso suna tambayar Lafiya?,kuka kawai na fashe dashi,Anisa ta taso tazo inda nake ta rungumeni tana tambayar menene cike da damuwa,kafin na bada Amsa Yaya Halil ya shigo yana tare Zainab da ke rugowa da gudu tana faÉ—in wai sai ta kasheni.
Enen ce ta tareta"menene hakan Zainab?".
"Enen ki barni nayi maganin damuwata,wai yarinyar nan ashe har yanzu cin amanata suke da Halil,Kinga yadda suke magana da ido tsabar shaiÉ—anci?".
Cike da jin haushinta Yaya Hibba ta ce"Wai ke kam mene damuwarki Aunty Zainab? Shi ya faÉ—a Miki wani abu ke tsakanin su".
"Kada ki raina mun hankali Hibba,wa zaku mayar É—an iska?ku dai da ku ke danne abin da yake zahiri saboda munafurci ku cigaba da yaudarar kan ku amma ni babu wanda zai Hainceni na yafe".ta faÉ—a cike da masifa tana mai tunkarar Zunairah da ke gefen Anisa tana ta kuka,ita ba wannan ma yake damunta ba,damuwar dake Zuciyarta tafi wannan haukan da Zainab ke gwadawa.
Daddy da ya ji hayaniyarsu ya fito dan dama gama sallama da su Zainab kenan ya koma ciki kasancewar weekend,cike da mamakin faÉ—an da ake ya ce"mene ke faruwa ne ?".
"Daddy Zina Halil yake ".Zainab ta tarwatsawa kowa kunne.
A tare suka maimaita kalmar ZINA,?
"mene ku ke maimaitawa kamar anyi mishi ƙarya,idan ba haka mene tsakaninsu shi da Zunairah,Daddy sigina suke ga juna ".