← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin yaƙe nayi ina ƙokarin danne abin da ya taso mun a ƙirji kafin na sake salon maganar "manta da wannan maganar yanzu dai dama ina san miki magana kan jiya,ba wai dan kiji haushi ba amma Anisa yadda ki ke taɓa Khalipha bai kamata ba,i mean he's not your Muharram ,Muna fakewa da soyayya muna kama hannun juna wallahi babu kyau, sannan ni gani nake ba sai kin zama loud bane zasu gane kin waye ba,ba wai kuma dan na ɓata Miki nake faɗa ba,kinsani ba zanga abin da zai cutar dake nayi shiru ba ".

Maganar ta ɓata mata rai dan ya nuna a fuskarta amma sai cewa tayi"naji nagode ,Allah ya saka da Alheri zan gyara".daga haka bata sake cewa komai ba dangane da abin da na faɗa ɗin,da muna tashi makaranta ganin yadda taƙi walwala yasa na ce mata "Ani I'm sorry akan abin da na faɗa Miki I mean no harm ,idan na ɓata Miki rai kiyi haƙuri dan Allah ,ko'ina ina so a ga mutuncinki fiye da kowa su kuma maza abu kaɗan kakeyi sai mutuncinka bar idanunsu".

Murmushi tayi "Zunairah wallahi ba haushi naji ba ,kawai naji kunya ne da kika faÉ—a sai kuma yanzu abin yake dawo mun amma insha Allahu zan kiyaye,Allah ya shirya tsakaninki da yaya Halil".

Bance komai ba ,ban san mene zance ɗinba dan haɗuwarmu dashi baza tayi kyauba,muddin kuma bai nemeni ba bazan sake nemansa ba duk da nasan zan sha wahala domin nayi sabo dashi ta yadda tunanin rabuwa dashi kawai yana sakani shiga mutuƙar tashin hankali, addu'ata Allah ya kawo mun duk wani abu da zai tunkaroni da sauƙi.

Duk haka na wuni bana da walwala a gida,da Mama ta tambayeni mene ke damuna ce mata nayi kawai kaina ke ciwo na gaji,na iddar da sallar isha'i aka aiko wai ana kirana inji Halil,sai da na gama adduo'ina kafin na tashi na fita ina mai sake danne ɓaccin raina,tsaye yake jikin motarsa yana danna waya ,sallama na mishi inda ya ɗago da idanunsa yana kallona kana yace"yan mata".

Kamar ya sake tunzurani,wai yan mata,cikin ɗacin rai nace "sannu ,ka aika a kirani Allah yasa lafiya".Bai amsani ba illa kallona da ya tsaya yanayi kamar wanda ya ga wani abu a jikina ko fuskata wanda bai taɓa gani ba.

"Kin Kirani ɗazu Allah yasa lafiya shi yasa nazo naji"ya faɗa yana mai mayar da hankalinsa kan wayarsa,tunda shekarar ta shiga ba'a taɓa raina mun hankali kamar yadda Yaya Halil ya raina mun ba yau,cikin tawa sigar ta rainin wayau ɗin nace"aikuwa ban san na kiraka ba ,kilan na kwanta bisa wayarne ta shiga contact ɗin tayi dialing,kasan waya na haka amma ni kam ban kira ka ba"misafar Who is she ɗin da nake san mishi ma sai na kasa illa tambayarsa da nayi idan da wani abu idan babu kuma zan koma gida ,abun mamaki sai cewa yayi babu zan iya wucewa,kafin ma na wuce ɗin ya rigani shiga motarsa ya mata key ya bar gurin bai sake ko kallona ba hawaye kawai naji suna zubar mun a kunci da haka na juya nima na shiga gida Amma fa abin duniya ya mutuƙar damuna.

Koda Mama ta tambayeni har ya wuce ɓoye mata nayi nace yazo ne dama kawai mu gaisa,har na shiga ɗaki ina jin tana yabansa.

A haka muka ɗauke watanni uku da Yaya Halil yana nuna mun halin ko in kula,zai kira sau ɗaya yace wai ya kira yace mun sannu, gidanmu kuwa ya daina zuwa,wata kalmar soyayya kam nama manta yaushe rabon da ya furta mun ,da ace zan iya da tuni na daina ɗaukar wayarsa,amma Zuciyata ta gaza yin mubaya'a dani atleast yana tare dani yana kirana a kullum koda sannu yace mun sai na ɗan samu peace of mind,koda mama ta tambayeni yanzu baya zuwa sai ce mata nayi an mishi transfer zuwa Lagos ne shiyasa,ban bari tayi zargin wani abuba na cigaba da dakon soyayya da ban san ina muka tsaya ba dan ina saman tekune bisa gadar sarƙa,a haka har muka zana jarabawa duk da banyi wasa ba ban bari abin da ke gabana ya hanani nuna ƙwazona ba,na dage nayi karatu na rubuta,ranar da muka gama jarabawar washegari ranar juma'a wadda zan iya kira da bakar rana gareni ,ina zaune ina yima Hauwa'u kitso Enen da Aunty Hibba suka yi sallama,rabon Enen da gidanmu har na manta,zuwanta yanzu kuwa na tabbata abu mai muhimmanci ya kawota,har nagama sawa a rai magana tace da Yaya Halil, farin cikin ganinsu naji sosai,cike da kunya na gaishesu ta amsa mini tana kirana yarinyarta tana mai saka mun albarka,tare suka shiga falon Mama tana mai musu maraba kafin ta kira Adavize ya ƙarbo musu minerals gidan Maman Baba maƙotanmu,hanawa Enen tayi ta ce ruwa ma ya isa a hanya suke ,sweet ta miƙawa Mama da invitation card tana mai cewa "sweet ne da invitation card ɗin bikin Halil juma'a mai zuwa ,dalilin zuwa da kaina kuwa ɗaya ne ba biyu ba,dan Allah Maman Zunairah kuyi haƙuri an rasa mai zuwa ya faɗa muku,ita Anisa wai kunya take ji can na barta gida tana kuka bakiji ba wallahi har zazzaɓi tace mun ya kamata ,ɗaki na barta kwance,ta saka abunne a ranta".

Murmushi irin na dattaku Mama tayi kana tace "to Enennisa (maman Anisa )ni na kasa fahimtar inda tashin hankalin yake, Aurena fa za'ayi ba mutuwa akayi ba,shi kansa haƙurin na gaza gane ta inda muka cancanta,ai abun mu haɗune mu nuna farin cikinmu ga shi Halil mu yi mashi addu'a Allah yasa abokiyar Alherinsace" ..

Maganar mama ta mutuƙar bama Enen kunya,daurewa kawai tayi ganin tazo ɗin ya saka tace"Mama Zunairah,shi Halil ya yi leading Zunairah har ta ɗauka suna soyayya ne ,nima kuma da ya fara faɗa mun wallahi na yarda dan ce mun ya yi ita yake so,to da ya kawo maganar wannan Auren ne na damu nake tambayarsa Zunairah fa,sai yake faɗa mun ƙawance ke tsakaninsu dama, although da sun fara da soyayya abun kuma bai working out ba, still dai naji ya kamata nazo na baku haƙuri,Abu ne Allah bai ba".

Ko Mama bata faɗa ba ranta ya ɓacci tunda ai baki da baki Yaya Halil ya shigo har gidan nan har falonta ya kalli tsabar idanunta yace yana san Zunairah yanzu kuma sai yace wai abokantaka ce?

"Bakomai Enennisa ai ba laifinsa bane ,laifin ita Zunairah da ta bari har abokantaka ya shiga tsakaninsu duk da ta san babu abota tsakanin mace da namiji,muna dai Amfani ne da zamani amma babu komai ai Ubangiji ne baiyyi ba".ƙwala mun kira tayi, hannuna yana riƙe da gashin Hauwa'u dana kama ina kitsawa,ni ban kitsa ba ni ban saki ba,ba niyata na ji abin da suke faɗi ba dan bama kusa da gurin ma Amma maganar da suke ba wai ƙusƙus bace,itama Hauwa'u batace na saki ba duk yadda na damƙe mata gashi ,jin Mama ta kira sunana ya saka na saki gashin wanda ya saka Hauwa'u yin yar ƙara,sai a lokacin na kula i was hurting her ita kuma ba zata iya katseni ba sanin halin da na faɗa.

Riƙeni tayi ta ce"Auntyna kada kije bari na shiga"murmushin ƙarfin Hali nayi nace ta barshi zan shiga ai ni aka kira,daga kujerar da Mama take naje na zauna ina mai san sakin fuskata kamar babu abin da ke damuna,Mamace ta ce"so Ohunene ga nan invitation card ɗin Halil da sweet ɗin Aurensa I thought na faɗa Miki babu abota tsakanin mace da ɗa namiji?mene ya haɗaki dashi?".

Danne kukan dake san ƙwace mun nayi na bata amsar da na sani ita take san ji a bakina"Mama ai ba abota muke ba,kamar yadda Anisa ta ɗaukesa Yaya nima haka na ɗaukesa,babu komai tsakanina dashi".

"Masha Allah,to ki kalla IV É—in nan nasa sunan matar da zai Aura Zainab dan haka Wannan zoben da ya baki na ajiya ki cire mishi ki Basu sai a wuce mishi dashi".

Tashi nayi na shiga ɗaki na ɗauko ƙaramin akwatin zoben da ya bani na cire daga hannuna ina mai jin zafin ƙirji kafin na rufe na koma falon na miƙawa Enen,ƙarba tayi ta buɗe kafin ta kalleni,nayi murmushi nace "ajiya ne dama ya bani".

Miƙama yaya Hibba tayi wadda ta saka cikin jaka ,ban tashi ba Mama ma batace na tashi ba tace "insha Allahu zamu shigo baki ɗayan mu tun safe,Allah ya sanya Alheri ya rufa asiri".

Sallama suka mana suka wuce Mama ta rakasu har Kofar gida ,suna fita na saka hannuna na riƙe ƙirjina dan ji nake kamar zai faɗi ,Mama na shigowa na miƙa mata hannuna ina kiran sunanta da kyar ,da gudu ta ƙaraso ta riƙe hannuna,wani irin kuka na fashe dashi ina faɗin"Innallahi waina illahir rajiun Mama ƙirjina,Zuciyata zata fashe Mama na shiga uku".

Shigowa Hauwa'u da Adavize sukayi suna masu tayani kuka ganin yadda baki ɗaya na rikice ina mai dafe da ƙirjina ina faɗin zan mutu,ba zan iya fassalta irin ciwan danake ji ba ji nake kamar an zuba mun wuta cikin ƙirjina,rungumeni Mama tayi tana faɗin Allah ya bani haƙuri,ji nake kamar tana ta wanka mun mari,ta ina zan fara haƙuri?ta ina zan fara?ta ina?wane irin cin mutuncine da wulaƙancine wannan,mene nayi mishi da zai mun haka?".

Ranar ji nake kamar alƙiyamata kawai ta tsaya ,koda Baba ya dawo shima haka ya yi ta aikin lallashi ,ransa sosai ya ɓaci amma sanin nuna fushin a fili baya da amfani ya saka ya ce nayi ta addu'a Allah ya bani wanda ya fishi,da zazzaɓi na ƙwana na tashi,ban taɓa tunanin a rayuwata zan iya cigaba da rayuwa bayan cin amanar da yaya Halil yayi mun ba,ta mun suka lokacin guda,baban ɓakin cikin guda wanda shine ban san abin da nayi mishi ba.

Haka nayi satin nan har ya zagayo bana da walwala sai dai na samu kulawa sosai gurin iyayena wanda dalilin hakan ya saka na fara sakewa duk da na san har abada wannan tabon ba zai taɓa barin Zuciyata ba,yana cikin Labarina.
Chapter 15 · 0% Book details