← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 28

Sashe 22

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka muka shashantar da maganar Yaya dan dama babu amfanin tada ta.washgari Monday muka yi resuming makaranta abin da nayi missing shine baccin safe,first week of resumption muka koma ni da Anisa, idan kaga dama kira mu Mayun boko,maitar ta saka mu zuwa idan ance yau za a koma ai akwai dalilin komawar koda kuwa revision ne an ɗan tada mana ƙwaƙwalwa ,bayan gama Lecture Anisa ta kira Khalipha ya zo ya ɗauketa,jin hakan ya saka na ce"guess ba tare za mu wuce ba".

"Aikuwa baki isa ba,tare zamu wuce zai fara dropping É—inki gida in yaso mu sai mu wuce"

Sanin koda nayi mata musu ba yarda za tayi ba ya saka nace to kawai,bayan wani lokaci ya kirata akan yazo ,dama muna bakin department É—in Computer science nan muka gama cin Awara,powder ta É—auko a jakarta ta É—an shafa bisa fuska kafin ta shafa lip balm ,ni dai kallonta kawai nake,Anisa na san Khalipha da yawa ina mai mata fatan Ubangiji ya saka su É—in Alherin juna ne dan da ace Khalipha zai ma Anisa abin da Yaya Halil ya yi mun ina ji ita sai mutuwa,.Tunanin hakan kawai da nayi sai da na nemi tsari da shaiÉ—an dake nema ya É—arsa mun haddasa a zuciyata .

"Ya ki ka ga fuskata? All set ko?".

"Kin haÉ—u kilan idan Khalipha ya ganki yau straight waliyansa zai kira yace a É—aura kawai daga nan sai gidansa".

Dariya ta saka sosai tana mai tashi kana ta ce"ana zuwa wannan gurin,soon zamu zo nan i can't wait to have you as my chief bride maid ke nifa kafin na gama Buk nake san kama Khalifa a hannu dan ba zan bari a ƙwace mun shi ba,so nake na samu lokaci na mishi maganar Aure idan zai turo kawai ya turo".

Ni dai murmushi kawai nake ina tsoron bada amsar da zata fito kamar ina baƙin ciki a haka har muka isa inda motar Khalifa take ,yana ganin mu ya fito yana murmishi,cike da shagwaɓa ta ce"Babyna Allah yasa baka jira da yawa ba".

"Ban jira ba idan ma na jira ai gimbiyata abin a jirata ne,ƙawarmu ina wuni"ya mayar da idanunsa kaina.

Kafin na kai ga amsa mishi Anisa ta karɓa"nifa bana gane ƙawarmu ɗin nan da kake yi fa,Zunairah ƙawatace ni kaɗai bana so wannan ai salon ƙwace ne".

"Naji Allah ya baki haƙuri,babu wanda zai ƙwacewa Anisa Zunairah,ƙawar Baby ina wuni".

Nima ina wuni É—in nace Mishi,hannu Anisa ta saka dan buÉ—e gidan gaba ,Khalifa ne ya katse ta,"babe Farouk yana gaba ne tare muke".

"And so,sai ya fito ya dawo baya kasan gaban mota nawa ne".

BuÉ—e motar wanda aka kira da Farouk ya yi ya ce"ran ki shi daÉ—e yau sai dai a koma baya ,ai muna zaman lafiya ki ka taso mu dole yau ki zauna a baya".

HaÉ—e rai tayi sosai tana mai cewa"to Allah yau sai na nuna maka motar Saurayina ce ba taka ba".

A yadda suke yi Khalifa na musu dariya na fahimci Farouk da Anisa basa shiri,kowa na ganin Hanjin juna,ni dai gefe na koma na tsaya Khalifa na musu dariya,ni kaina ba so nake Farouk É—in ya shiga bayan ba,idan ma ba iskanci irin na Anisa ba mene laifi idan ta shiga bayan mun zauna tare?.

Juyawa tayi akan tafiya za tayi idan har Farouk bai bar mata gaba ba, Khalifa ya ci mata yana bata haƙuri inda Farouk ya fito gidan gaban yana mai cewa"ai sai ki zo ki zauna ɗin mara zuciya".

Yana ƙokarin buɗe bayan ya kula dani dan ina jin sai a lokacin ya san tare muke,murmishi ya faɗaɗa da ya dora idanunsa a kaina,ganin ya zuba mun ido yasa nima na zuba mishi,buɗe mun ƙofar ya yi ya ce"Bismillah mai kyau da ace na san da ke waccan ɗara wada ɗin take ai bazan tsaya biyeta ta ba,cikin bugun zuciya guda zan dawo baya na zauna kusa da macen da tunda garin Allah ya waye banga mai kyawunta ba,infact na daɗe banga mai kyawunta ba".

Wani dogon tsaki Anisa ta ja tana mai kiransa da Fuck boy kafin ta buÉ—e gaban motar ta shiga ,nima shiga nayi bangaren da Farouk ya buÉ—e mun kafin ya zaga shima ya shiga,Khalifa ne ya ce"ran gimbiya ya huce"kafin ya tada motar ni dai baki É—aya na kasa samun nutsuwa musamman ganin yadda Farouk ya zuba mun ido,

"Dan Allah ki faɗawa bawan Allah nam sunanki ko zan ƙara a cikin Zuciyata na ƙara kaimun bege ki,kinga idan na haɗa da sunanki mai kyau mai daɗi sai abin ya fi armashi".

"Ummm kaji mayaudari,idan ka tashi sai ka faÉ—a mata yan mata nawa ka yaudara"

"Khalifa hold your babe oo,ita ta samu gurin fakewa ni shine zata bata mun rawata da tsalle,kalli nan ƙawarta ki manta da wannan dan kawai naƙi santa kafin ta koma ga abokina shine take baƙin ciki".

Ai kamar jira take ta juyo ta fara masifa tana faɗin"wallahi tallahi kai ka san nafi ƙarfinka,sannan baby ya fika ta ko wace irin siga,i will never choose you over him".hannu ta saka tana mai ɗorawa bisa gemun Khalifa wanda murmishi kawai yake yana tuƙi ,ni dai Allah Allah nake a saukeni na Kama gabana ba wannan nazo yi ba,koda ace Farouk da gaske yake dangane dani sai dai ya yi haƙuri na rufe babin saurayi,ko zanyi ba yanzu ba ,a yanzu karatuna shine Soyayyata dan na kula soyayya bata karɓeni ba.

A haka Farouk da Anisa sukayi ta musayar zance har aka kaini ƙofar gidan mu,ina ƙokarin fitane Anisa ta dakatar dani ta hanyar faɗin"yauwa baby baka yi wa Besty jaje ba,Babane wallahi aka kulle a station akan case ɗin satar waya wai yaran sunce shine Ogansu ,kasan yanzu kuma al'amarin basu tsaya wani bincike ba suka karkarya Baba,har za aje kotu ma Daddy ya yi stepping in abun babu daɗi yanzu haka Baba jinya yake ,Allah ya sa ba akai ga kuto ba da yanzu yana gidan maza babu hakkinsa".

Wani abune yazo ya tokare yawon da nake niyar haÉ—iya,kallona Khalifa ya yi cike da tausayin halin da ta zayyana masa da Baba ya faÉ—a yace"Ya Salam,Allah ya sake kiyaye gaba,Allah ya bashi lafiya ai ban sani ba da nazo na dubashi,kuma laifinkine Anisa da baki faÉ—a mun ba".

"Yanzu ma ai bai ɓacci ba zaka iya zuwa ka duba sa"ta faɗa.

Murmushin yaƙe kawai nake da ya buƙaci shiga duba Baba,fita nayi da zummar zan sanar da Mama kafin su shiga ɗin,kamar wadda laka ta karyewa a ciki haka na shiga gidanmu,ina mayar da Kofar na jingina da gate ɗin ,rumtse Idanuna nayi sai jin hawaye nayi,shin mene ya ɓata mun rai?.

Mutunci Anisa tayi mun saurayinta yayiwa Babana jaje ya duba lafiyarsa Amma dole sai ta zayyana dukkan abin da ya faru da Baba,ba domin Anisa bace sai nace da biyu tayi min,na kasa haÉ—a abun ,sai nake jin zafin da ya kasance gaban abokin Khalifa ne,idan wani ya fahimta wani ba zai fahimta ba,cewa za ayi kilan ma dan Daddy dinta ya shiga ne aka yi siyasa aka fitar da Baba amma da saka hannunsa.

"Auntynmu lafiya?".

BuÉ—e idona nayi na saka su cikin na Hauwa'u dake sanye cikin uniform É—in islamiyya,saurin goge hawayen da ya zuba kan kumatuna nayi ina cewa"lafiya mana,baku wuce ba uku saura ina Muhammad É—in,Mama fa".

Wucewa nayi ina kiran sunan Mama gudun kada Hauwa'u ta gane kuka nake,bina tayi da kallo har na shiga falo ,Mama ke Niyar fita tana kiran Hauwa'u.

Kaina na saka nace"inya ki zo mana kina ji ana kiranki" takowa tayi daga inda na barta a tsaye ta shigo falon,Naira É—ari biyu Mama ta bata:"dan Allah Inya ki bawa Adavize kuÉ—insa ya siya abin da yake so bani da chanji shi ya saka na haÉ—a muku"..

"Cewa yake bana bashi kenan,ni Mama ba sai kin faÉ—a mun Inya ba muna fita zan tsaya shagon Baban chakwai na bashi kuÉ—insa".

"Naji dai Allah ya yi muku albarka ya bada ilimi mai amfani".

Kallonsu nake ina mai ayyana abubuwa da dama da yaso ya mantar dani abin da ya shigo dani gida sai ga Muryar Anisa tana Sallama.

"Wa nake ji kamar Anisa"Mama ta faÉ—a tana buÉ—e labule,shigowa Anisa tayi bayanta Khalifa da Farouk waÉ—anda suka tsaya nan ita kuma ta nufo falo tana cewa "wallahi Mama ina nan ina jiran Zunairah,wai Khalifa ne yazo duba Baba shine nace su shigo jinta shiru ".

"Allah sarki ina nan ina sallamar su Inya ne,maraba shigo dasu mana Bismillah malam Khalifa maraba".

Bance dai komai ba har ta kai mun dukan wasa a kafaɗa,daka bakin ƙofa suka duƙa suka gaida Baba wanda ya amsa musu duk da bai san su wane ba,Kuɗi Khalifa ya ciro a aljihunsa ya aje ma Baba,Mama ta ɗauka ta maida mishi,inda Baba ke cewa ai iya dubasa ma da sukayi ya isa ba sai sun bashi kudin ba,duk yadda ya yi Baba ƙin karɓa ya yi,gidan mu Muna da wadatar zuciya,idan har da kuɗi zaka siyemu zaka daɗe baka samu kasuwa ba.
Ban rakasu ba Mamace dai ta taka musu tana mai sake musu godiya,kafin ta dawo ta mun maganar su na shiga É—aki,tunda nake wannan ne karo na farko da naji zafin Anisa fiye da tunanina.
Duk yadda na guji maganar sai da Mama ta tada mun tana mai faÉ—in wai suna da kirki na sake musu godiya,to kawai nace na cigaba da duba handout É—ina ,ganin kamar bana san maganar ya saka Mama rabuwa dani ta koma gurin Baba,da dare Anisa ta kirani, ina ganin kiran nata amma na kasa É—agawa dan nayi fushi da gaske da ita.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ17: Negative Scene

*𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈*

Tunda Farouk ya fara maganar Zunairah taji baki ɗaya bata da nutsuwa,Farouk yana samu dan har ya fi Khalifa samu yana cikin babban dalilin da baza ta iya barin wata alaƙa ta ƙullu tsakaninsu ba,duk da cewa abin da ya faru da Baban Zunairah sharri aka yi mishi amma sai ta tsinci nishaɗi cikin hakan,atleast sun fahimci su ɗin kaskantune da family ɗinta zasu iya yi mata alfarma.
Chapter 22 · 0% Book details