← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 28

Sashe 25

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun wuce ne Mama kecewa "ai kin mun dai dai da kika nuna masu ke jininace,yar banzar yarinya mai kama da Mayu".

"Maman Inya ki daina biyewa ana haka dake oo"Baba ya faÉ—a.

"Abeg Baban Zunairah ka barni na faɗi abin da ke cikina tunda ai ba a gabansu na faɗa ba,ba ayi mun dai dai ba nikam,kaga yadda yarinyar nan ta yagar mun fuskar yarinya ne?wallahi taci darajar masu daraja da ni da kaina zan mata wulaƙanci".

Ni dai bance komai ba amma tunanin yana kan Yaya Halil,ina jin tausayinsa har rai na,na san mutane da yawa idan suka ji Labarina zasuji haushin tausayin da nake mishi amma i can't Help it mutum ne da muka yi soyayya dashi dole ne sauran tausayinsa ya tsaya mun a ƙirji domin duk wanda aka haɗa Aure da mutum kamar Zainab a yadda na fahimceta sai ta saka mishi ciwan zuciya.

Da bayan sallar isha'i ina zaune ina fama da kaina wai aka buga ƙofa ana Sallama da Zunairah,abun ya bama kowa mamaki , Mamace tace ma wanda ya shigo ɗin yaje yace nayi bacci,naji daɗin hakan duk da ban san wane ba,ina jin Mama nata faɗa akan anzo ban gama fama da abin dake damuna ba za ana mata passing na neman yarinyar kamar tace nema mata saurayi take,Mama kenan idan ta rikice baka gane mata ko kaɗan,Ni dai ina ji ban ce komai ba ina dai mamakin wanda yazo nemana ne.

*****************************************

Duk yadda na kawo zanji kunyar zuwa makaranta wayewar garin ranar sai naji ba haka bane musamman da Mama ke nuna mun kada na bari wani abu ya kaini ƙasa ko menene shi,idan nace zanji kunyar kallon mutane bisa abun da ya faru to tabbas mutane sune zasu na bani ra'ayoyin da zan rayu da su dan haka na shirya tsaf cikin shirina na makaranta,da fari ina tunanin na saka niƙab saboda ciwan dake fuskata amma sai rashin amfanin yin hakan ya fi amfaninsa yawa.

A inda muka saba zama ni da Anisa muka zauna,kallona take yi tunani ko bazan mata sallama ba ,ban iya gaba ba bazan fara da Anisa ba,ina dai cikin ɓacin rai kuma na faɗa mata cikina,duk kus kus ɗin da ake a aji ina ji na zaɓi dana share ,Sallama nayi mata kana nace"ya kuka je gida jiya?".

Kamar dama jira take na kawo wani abun da zai haɗamu magana ta washe haƙora "lafiya lau wallahi ke Kinga yadda Malam ya ci mutuncin Zainab,wallahi duk zatona babu mutumin kirki gidansu ganin yadda yayanta Yunusa ya ɗinga ma Yaya dariya ranar da tayi mana Aljanu,wannan da ke tare da Baban nata ai shine yunusan".

"Allah sarki Allah ya shiryesu"na faɗa ina mai taƙaita maganar gudun kada ta shiga inda ban Kaita ba duk dan mu shirya,.Wani course mate ɗinmu ne da ya fi kowa zarra yazo har inda nake,kan desk ɗin mu ya hau yana mai cewa"Zunairah baby ,kin san fa na dade ina sanki but idan za muyi soyayya touchy touchy love za muyi".

Dariya abokansa suka saka daga baya suna masu faÉ—in" Enoch & Zunairah,hope dai baza ta baka ciki ba first encounter dan ga dukkan alamu itace zata ma namiji ciki maimakon ya yi mata".

Marin da Anisa ta ɗaukesa dashi ya saka na ɗago kai,ya shigesa sosai babu ƙarya dan yadda ya tashi kamar zai shige jikinta abin ya bani tsoro,hannu ta saka ta turasa baya inda yake cewa"i will join you "yana mai dukan kirji itama tana mayar masa tana cewa idan ya fasa.

Ganin abin zai zama faÉ—a ya saka class rep É—in mu ya shiga yace zaije ya kira securities idan baza su bari ba,nuna Anisa yake da yatsa yana cewa"RUN if you see me outside just run".

"Abeg Enoch if you don't kill me outside no be your mama and papa blood you be".

Kamo hannunta nayi na zaunar ina mai cewa"ya isa haka Anisa bai Worthing kulashi ba".

"Ki bari na nuna mishi shi ƙaramin shege ne,yan iska da jira suke wani abu ya sameka su mayar dashi abin wasa ,ya yi messing da wrong person dan Wallahi akan ki zan faɗa da kowa,we might have our differences amma its me and you against the world,I'm sorry akan abin da nayi Miki earlier ki yafe mun banyi dan na ɓata Miki ba kinji?"..

Hmmm Zunairah wawuya a alaƙa tuni na narke a zuciyata naji babu kamar Anisa,harshe da haƙori ma sukan saɓa dan mene ni da Anisa baza mu saɓa ba kuma mu dawo mu shirya?

Murmishi nayi nace "na yafe Miki ya wuce and Nima ki yi haƙuri a kan yadda nayi reacting ban kyauta ba ban ji daɗi bane kawai ".

A haka muka shirya kamar ba abin da ya shiga tsakaninmu ,da muka je siyan gurasa ne take ce mun"Kinga Farouk É—in nan abokin Khalifa mutumin banza ne,and naga taketakensa kamar so yake ya shiga rayuwarki,kin san Allah ba mutumin kirki bane kada ki fara bashi fuska".

"Aikuwa duk abin da ya ƙwaso ya zo gurin da bai kamata yazo ba,ki ƙwantar da hankalinki,ni ai na daɗe da rufe babin soyayya kuma sai dai ƙilan nan gaba,amma ni kam yanzu na bawa namiji lokacin da zai ɓata mun aikuwa sai dai idan ba niba".
Ni baki ɗaya ma Farouk baya cikin irin zaɓina,bai ma kwanta mun a zuciya ba balle mu fara maganar soyayya,haka tayi ta nuna mun illolin Farouk wanda suka ƙara taoratani dashi, babban abin mamakin shine yadda Khalifa ke tare dashi tunda dai tace budurwa da yake tare da ita har ciki ta zubar ,"Allah ya shirya mana mazan Nan kawai amma basa da kama "na faɗa wanda hakan ya kawo karshen maganar Farouk a ranar.
Driver yazo É—aukarta nace ba zan bi su ba dan haka itama tace baza ta shigaba muje mu hau É—an sahu,a bakin inda suke tsayawa muka tsaya muna neman na hanyar mun.
"Malama Zunairah tafiya ne? ".
A tare muka juya muka kalli mai maganar ni da Anisa da mamakin jin yadda aka kira sunana randomly.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ19:Karma comes

*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*

"Khubaybu ɗan Adaidaita?"na faɗa ina san gasgata shi ɗinne dan encounter ɗin mu zan iya cewa ban masa kallan ƙurilla ba amma a ƙwana ɗaya ba zan mantashi ba.

Dariya Anisa ta saka jin sunan da na kira kafin tace"ke kuma ina ki ka san wannan? ".

Ban bata amsa ba na fuskance sa ina mai saka hannuna a Jaka nace"yi haƙuri ashe fa kana bina kuɗi,baka ma faɗa mun nawa bane,kaga har gida ka kaini kuma ni kaɗai".

Murmishi yayi yace"muje yau sai na aje ku in yaso sai muyi lissafi ".

Hannun Anisa da tambaya ya cika mata kai na ja ina ma cewa"to,Besty mu je".bina tayi amma na san tana san jin ƙarin bayani,bai wani ja mu da hira mai tsayi ba wanda hakan ya burgeni,bana san Mutum mai shegen surutu,da muka kusa shiga unguwarmu ne yake tambaya itama Anisa nan take?

"Ka sauke mu duka gidan su Zunairah "ta bashi amsa kafin na bashi tana mai yin murmushi tana kallansa,wanda ko ba'a faɗa mun ba na san dariyar raini take mishi,na san halin ƙawata sarai ta wannan fannin,sai da ya kaimu ƙofar gidanmu muka sauka,sai a yau na mishi kallon tsanake ta yadda duk ina na ganshi zan gane sa,"mungode mai Napep yanzu duka nawane kuɗinka?".

Murmishi yayi ya saka hannunsa cikin gashin dake kansa wanda aka yiwa dada yace"ni dai Aunty Zunairah ki bar kuÉ—in nan na ranar na yafe amma na yau ku bada É—ari biyu ke É—ari ita É—ari Allah ya saka musu albarka".

Wata irin dariya Anisa ta saka tana mai sake maimaita kalmar Aunty Zunairah kana ta ƙara da faɗin"kai yanzu goɗai goɗai da kai kake kiranta Aunty?and wa zaka kalla anan kace mana daga Buk zuwa hotoro Naira ɗari?da janin wa za kayi kuɗi da shi,abeggi brother shaggi karɓi kuɗinka"dubu ɗaya ta ciro a jaka ta miƙa mishi,bai karɓa ba ya zuba mata ido,sai naji babu daɗin abin da tayi mishi ɗin,kuɗin na karɓa na turata nace "shiga gida dan Allah".

"Gwara na shiga dan ina dariyar nan raina ɓaci yake".shiga gidan tayi tanata mita.

Dawowa nayi na tsaya nace"dan Allah Khubayb kayi haƙuri ba ɗabiarta bace ban san mene yake damunta ba,kayi haƙuri".

Maimakon ya yi addressing abin da nake faÉ—a sai cewa ya yi"sunana a bakin ki daÉ—in faÉ—a,Khubayb,last da naji wanda ya Kirani da sunan dai dai har na manta ".

"Well idan zan tuna kaima da bakinka da ka tashi faɗan sunanka ce mun kayi Khubaybu dan adaidaita ".Dariya nayi kaɗan wanda shima ita ɗin ya yi yana mai kallona ,kuɗin da Anisa ta ɗauko na miƙa mishi da nayi realizing hira nake da ɗan adaidaita sahu kamar wata sakara,mutum da ba saninsa nayi ba,idan ma kidnapper ne ko serial killer Allah kaɗai ya sani.

Kamar ya san mene a zuciyata na tsinkayi muryarsa yana cewa"ni ba serial killer bane ko wani mugu,ni ɗan garin Kaduna ne cirani ya kawoni Kano a bakin Buk kuma sai naga abin da ya tuna mun da yan biyu ta,i was like idan abun nan da Kowaisah yake faruwa fa?da bazan tsaya ba sai inda karfina ya ƙare shi yasa na bada same Energy".

"I was like?"na faÉ—a da mamakin jin turanci a bakinsa.

"Hajaju Turanci Yarene kawai kowa zai iya ,mun É—an tsinta but yadda ki ke curious labarin sai mun sake haÉ—uwa,zan anfani da wannan mu sake haÉ—uwa sai na cigaba da baki labari kada na baki tsoro da surutu, although Nima yau na fara gaban Aunty Zunairah ".

Naira É—arin da ya ce zai É—auka ya É—auka ita É—ari ni É—ari ya bani chanji kafin ya ce mun sai gobe,yaja É—an sahunsa.

Tsaye kawai nayi ina bin adaidaitan da kallo har ya bar layin ,bai bari na sake bashi haƙuri kan Anisa ba,i can't believe wai ni Zunairah ce yau na tsaya hira da ɗan Adaidaita sahu,abun da ban taɓa ba,na san da Mama zata fito ta ganni da sai tace mun babu kamun kai Indai Mamace.
Chapter 25 · 0% Book details