← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 28

Sashe 28

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sai a wannan lokacin ta kula da Anisa dake kwance baki É—aya ta sauya kama lokaci guda,mayar da kallonta tayi kan Enen wadda babu abin da take sai aikin hararar Zainab,cike da borin kunya tace"Enen ashe Anisa ce rai hannun Allah ai ban sani ba,ya jikin nata,na zata wallahi Halil tare yake da yar iskar nan duk da bana lamuncin hirar da na tarar sunayi".
"Álhamdulilah Zainab da ki ka san Anisa ranta a hannun Allah yake ba a naki ba,nayi imani da Allah da ace ranta a hannunki yake da tuni kuma wannan haukan ki ciresa,ace ke a rayuwa baki da aiki sai bala'i,kada fa ki saka kiyi abin da zai dameki dan Allah na gaji da Lamuni".
Haɗe rai tayi wanda ya nuna Maganar Enen tayi mata Zafi sai wani cije baki take, kai wannan da ace namiji ce ba ƙaramun shiryayye za ayi ba,wallahi duk tunanina ba zata kuma cewa wani abu ba ganin Enen ta mata kashedi,wai sai cewa tayi "mumze a huce amma gaskiya ni bana san kina mun magana a haka,babu wanda na taɓa idan nayi faɗa akan abuna a ɗaga mun ƙafa kada a danne mun hakkina".
"Aw Halil É—inne abun ki?"Enen ta tambayeta baki buÉ—e,sake tsuke baki Zainab tayi kamar ka saka almakashi ka datse É—an banza.
"To Enen mene ki ke so na faÉ—a".
Jin furucin da tayi ya saka Yaya Halil da Yake binta da kallon Mamakin kama hannunta ,sai da yaje bakin ƙofar ya ɗaɗa mata duka a baya kafin ya watsata waje ya saka key,duka ƙofar ta fara tana yan ihunta kafin lokaci ɗaya kuma muka ji shiru.
Tsaki ya yi ya ce"masu tsaron asibitin sunyi gaba da ita, wallahi Zainab sai da haka,idan tana wani abun kamar bata da hankali".
"Anya Halil yarinyar nan bata ƙwaya kuwa?"Enen ta faɗa cike da alhini.
"Babu wata ƙwaya baya ga iskanci wallahi,kamar a kanta aka saukar da dukkan wani iskancin duniya kullum kuma abun nata sake gaba yake".
"A dai bincika dan wannan yarinyar ban yarda babu sharrin ƙwaya ba, kana kallon cikin Idanunta kamar an tsaga rashin kunya?gaskiya da sakel ace duk duniya Zainab tayi maka matsayin mata?".
Ganin za su wuce suyi maganar da bai dace gabana ba ya saka na sauya zacen nace"yanzu Enen yaushe suka ce zata farfaÉ—o".
"Ƴata yi haƙuri ina nan ina mita ga Anisa da likita yace kada a cika ta da hayaniya, ya dai ce zata farfaɗo bai faɗi lokaci ba,Nagode sosai da ki kayi saurin kawota asibiti Allah ya yi Miki albarka ".
"Amin Enen ai yima kaine,bari dai na wuce in yaso ko da su Mama sai mu dawo tunda ban faÉ—a musu ina nan ba ".
"Ai kada ki damu,ki huta idan ta tashi na faÉ—a mata kin wuce amma kada kice zaki damu kanki wai ki dawo anjima,ai nayi admitting É—in mu har ayi mata aiki idan yaso gobe idan da hali sai ku zo É—in ,suma ai ba a tasosu ba zato ba".
Ba dan na so ba dai na ɗauki maganar Enen,Yaya Halil ya yi tayin kaini gida,ban ƙasa a gwiwa ba na ƙiya sanin mene sakamakon binsa a motarsa,ƙila dai ƙarshe so yake matarsa ta ƙoneni kowa ya huta,duk yadda naso aka kada ya mayar dani gida haka Enen ta saka baki dole muka jero a tare muka fito.
"Baki da wata tambaya da za kiyi mun?"muryarsa ta katsen saƙesaƙe zuci.
"Yaya Halil ya kamata nayi maka wata tambayar ne ban sani ba?I mean mene ya kamata na sani?".
ÆŠan sosa kansa ya yi da yatsa É—aya kafin yace"akan Zainab mana,baza ki tambayeni komai ba?".
"Yaya Halil mene ya saka zan tambayeka abin da ya shafi gidanka?ko wane gida da nasu kai shine na gidan ka ina maka fatan Allah ya sassaita maka,matarka ce kana santa tana sanka atleast zaka iya nuna mata daidai,ni Alfarmar Abu ɗayane dama shine ka faɗa mata babu abin da ya taɓa shiga tsakanina da kai dan Allah ta daina kawo mun hari".
Gani nayi ya tsaya daga tafiyar da yake,juyawa nayi na kallesa,ganin kamar maganar ta masa ciwo a yanayin fuskantarsa ya saka na cigaba da tafiyata,ganin da gaske bana da lokacinsa ya sa ya tako sai da yazo inda nake yace"mai yasa ki ke san denying abun da muke dashi a baya?".
"Bakaji kace a baya ba,kai kana ma ɗaukarsa baya amma ni kam Yaya Halil na binne wannan,zaifi idan kaima ka binne tunda dama ai abu ne da ka ƙi.".
Kafin ya yi wata maganar na hangi Khubayb,wallahi baki É—aya na manta tare muke dashi,yana tsaye jikin É—an sahunsa yana kaÉ—a mukulli,kallon direction É—in da nake kalla yayi kafin yace "wane wancan É—in?".
"Wanda ya kawo mu Asibitin all thanks to him ƙilan da Bamu san mene zai faru ba".
Takawa nayi yana biye dani,sosai naji daÉ—in ganin Khubayb atleast ya sakar mun mara nayi fitsari,da muka isa gun Khubayb da damuwa yake tambaye lafiyar Anisa amma wai abin haushi Yaya Halil sai cewa yayi "maigida nawane kuÉ—inka?".
Kamar nayi ta kifa mishi mari haka baki,wai maigida nawa ne kuɗinka,murmishin yaƙe nayi nace mishi"Yaya Halil ɗan uwan mu ne banyi zaton yana jirana".
"Aw Sannu"shine Abin a ya iya faÉ—a,yan kallo muka bar gurin,muna fita cikin asibitin na sauke ajiyar zuciya,a nan ne nake faÉ—awa Khubayb jikin Anisa ,yaji tausayinta sosai inda yake mata addu'ar samun sassauci.
Da naje gida nake faɗawa Mama ,ta shiga damuwa sosai inda take cewa goben insha Allahu za suje,da tunanin Anisa na ƙwana baki ɗaya na rasa mene yake mun daɗi,ban taɓa tunani Anisa bata da lafiya har haka ba,sai nake jin kamar ban zamar mata ƙawa ta kirki ba tunda har ban iya gane bata da lafiya har haka ba.

**********
Da safe banje makaranta ba muka wuce tare da Mama,abinci mai kyau Mama ta mata muka wuce, har Daddy muka tarar a asibitin,sunji daÉ—in zuwan mu ,ina zuwa na rungume Anisa wadda tana ganina ta fashe da kuka tana faÉ—in"Kinga halin da na shiga ba".

"Sai ki faÉ—a mata rigimar da ki ka tada mana "cewar Daddy.

Kallona take cikin ido hawaye cike a Idanunta,hannuna da ta riƙe take rubbing a hankali Idanunta a ƙasa ta kasa ɗagowa ta kalleni.

Sai na fara tsoron abin da zanji daga bakin nata,É—agowa nayi na kalli su Enen wanda suma sun kasa haÉ—a ido dani,a tsorace nake tambayar su mene ya faru ina kuka,Mama ma tayani tambaya tayi ganin baki É—aya kamar mun zama surukai dasu.

"Anisa idan har kin ɗaukeni ƴar uwa wadda take ɗaukar damuwarka tata kiyi mun magana dan Allah , Wallahi gabana faɗuwa yake sosai tsoro nake ji".na faɗa ina sake riƙe hannunta.

"Zaki iya bani abu idan na tambayeki?"ya tambaya a yanzu tana kallon cikin idona.

Da sauri na kaɗa kaina ina mai cewa"indai bai saɓawa Shari'a ba bai kuma fi ƙarfina ba Anisa zan baki,abu koda shine ƙarshe a hannuna zan baki ni na haƙura,zan baki ko mene shi".

"ZUNAIRAH INA SO BANI ƘODARKI ƊAYA".

Hmmm to fa kunji dai abin da Anisa ta bukata daga Zunairah.

Shin zata iya yiwa Anisa wannan sadaukarwar ko kuwa zata gagara?

Ƙoda fa

Hmm Nima dai ban san mene zai ce ba.
Domin san cigaba da bin littafin Cin dunduniya kuyi maza kuyi payment É—inku akan Naira 600 kacal domin cigaba da samunsa a telegram ko ku bibiyesa a Arewapen kan handle É—ina mai Suna Chuchujay.
8130229878
Opay
Amina Jamil Adam
Chapter 28 · 0% Book details