← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 28

Sashe 21

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin wuce mu tafi wallahi kafin na saɓa miki"Yaya Halil ya faɗa ganin zata masa haukan da ta saba gaban iyayensa,a wannan point ɗin ya yarda idan aka kai Zainab asibitin mahaukata babu ɓata lokaci zasu bata gado.

"Ja matarka Halil ku wuce gida "Enen ta faÉ—a tana mai mamakin É—abi'ar Zainab,babu musu ya fincikota suka fita tana ta ihu tana zage zage har suka bar cikin falon baki É—aya.

"What madness "Daddy ya faɗa,yana ƙoƙarin juyawa Zunairah ta ce "Daddy gurinka nazo".

Juyowa ya yi "Ni?"

"Eh Daddy taimako Nazo kayi min dan Allah ,idan kayi min ba zan taɓa mantawa ba,and wannan abin da Matar Yaya Halil ke faɗa babu gaskiya ciki,babu abin da ya haɗani da Yaya Halil bayan mutunci ".

"Kada ki damu da wancan abin tukunna dai taimakon menene ki ke so,wani ne baya da lafiya ko mene?".

"Daddy Baba ne,yana state CID sun kullesa akan case ɗin satar waya tun jiya sunƙi bari kowa ya gansa?".

Zama daddy ya dawo ya yi yana mai cewa"to mene ya faru garin yaya?".Labarin abin da ya faru na bashi cike da mamaki yake mayar da abin,kowa a falon na bashi tausayi daga kallonsu, tausayin nake so na basu a taimakawa Babana,dan naji ance idan aka kaika bompai sai Allah zaka dawo daga nan idan ba kayi wasa ba Abuja za a wuce da kai,idan kuwa aka kai Baba Abuja mun shiga uku mun lalace.

"To su haka kawai sai su ambaci sunansa babu wani ƙamshin gaskiya kuma?"

"Daddy!!!! Please kafi kowa sanin Baban Zunairah mutumin kirki ne just help him na san zaka iya daddy"Anisa ta faÉ—a tana mai zuwa inda yake jin abin da yace,duk da naji Haushi sai na danne tunda naima nake .

"Wallahi Baba baya sata Daddy ,abu na karshe da Baba zaiyyi shine sata kawai dai tsautsayine da ƙaddarar da bawa baya iya tsallake mata".

Shiru Daddy ya yi kamar yana nazari kafin daga bisani yace"ki je gidan zanje chan É—in,zan kira commissioner of police".ban masa musu ba na tashi na tafi gida,lallashina Enen ta ringa yi har ta haÉ—a ni da driver muka wuce tare a Anisa wadda Idanunta ya kaÉ—a saboda Kuka da ta sha.

Da mukaje gida a ƙofar gida muka tarar da Yaya Halil,ji nake kamar na mishi shegen duka ko uban me yazo ya yi mun oho,ina fitowa kai tsaye na shiga gida Anisa ta tsaya dashi inda take faɗa mishi abin da ya faru,wucewa ya yi shima station ɗin cike da damuwa mutuƙa,da ta shigo take faɗa mun yaje station ɗin.

Mun gama saka rai haka Mama ta dawo wai har yanzu ba'a sake su ba,kana kallonta ba sai an faɗa maka gwiwowinta sun sage ba,cike da sarewa take faɗa mana wai kuto za a tura su washegari,Anisa ta fara kiran Daddy wanda ya shaida mata kada ta damu case ɗin ba zai kai har aje kotu ba,mu dai shiru kawai mukayi dan a wannan gejin kukan ma yaƙi zuwa.ɗaki Mama ta shiga ba dai tace komai ba.

Da kulawa Anisa ke faÉ—a mun"Zunairah komai zai zama dai dai babu abin da zai faru da Baba".

"Allah ya sa domin idan wani abu ya faru da Baba ina mai tabbatar Miki Anisa Mama zata samu damuwa idan Mama ta faÉ—a wani hali kuwa Kinga Asirin mu ya gama tonuwa".

"Insha Allahu babu abin da zai faru,baki yarda da Daddy bane?komai idan aka haÉ—a da siyasa za'a dace,Daddy fa influenced É—an siyasa ne kada ma ki yi tantama akan abin da zai iya"

"To Allah ya zaɓa abin da ya fi zama Alheri "na faɗa ina mai tausayawa rayuwarmu tun kafin ta zama abin tausayi domin da Akwai tausayi

Ita ta dafa mana shinkafa tunda dama gidanmu ba'a rasa miya,Aunty Muna kuma ta kawo tuwo,Anisa ce kawai ta iya ci sai Adavize da Hauwa'u dana titsiye su ci shikafan ko kaɗanne.Tuwon na kai ma Mama duk da na sani zai wahala ta iya cin abinci ni kaina ba dan Anisa ta saka mana tare tana mitar muci ba da babu abin da zan iya ci,. Tunani zata wuce ganin har munyi sallar isha'i ya tabbatar mun kwana ne za tayi,ban dai tambaya ba amma tunanin zata ƙwana ɗin kawai ya saka naji wani irin farin ciki,ina jin daɗi dana Samu ƙyautar Anisa,ita ɗin ƙwace da kowa zai so ya yi Alfahari da ita.

Wuraren ƙarfe sha biyu na dare bacci har ya ɗauke mu naji Knocking kamar a mafarki,ni kaɗai na iya farkawa Anisa kam bacci take sosai ba damar na tasheta,dama su Hauwa'u ɗakin Mama suka ƙwana,wayata ce ta hau ruri,layin Yaya Halil da na mayar da Sunansa zuwa LESSON LEARNED ne ya Kirani,kamar bazan ɗauka ba dan sai da ta katse ya sake kira kafin na ɗauka.

"Muna kofar gida da Baba ki zo ki buÉ—e".

Wuntsilowa nayi daga kan gado,banyi tunanin ko saceni zai yi ba ko ya yi mun wani mugun abin,Babban abu mai muhimmanci shine Babana da ya ambata.

A tsakar gida naga Mama da ƙatuwar fitilar ta tana tambayar wanene,kafin a amsa mata nace Mata "Baba ne ".

Rige Rige mukayi wajen buɗewa,there Comes Baba an Mishi tara tara an kamo shi kamar kayan wanki,ban san ya akayi na fáshe da wani irin Kuka ba.

"Ya mutu ko Halil?"Mama ta tambaya cikin wani irin yanayi da baza ka iya fassara abin da ya ƙunsa ba.

"a'a Mama ya samu karaya ne a ƙafarsa guda ɗaya da hannunsa"ya faɗa yana mai kamo Baba abokin tafiyar nasa yana bin bayansa,sai a lokacin baki ɗayan mu muka kula da ɗaurin da ya sha,ɗaki aka shiga dashi,gado aka ajesa kafin Mama ta Mishi shinfiɗa Sanin jinyar karaya kan gado ba zai iyuba,wani bulo dake kitchen ɗin mu aka ɗauko dan ɗora masa ƙafa,abin haushi duk abin nan da ake Hauwa'u baccinta take shaƙa har gwanda adavize ace yarone.

Godiya Mama ta yi ta musu,ni dai ban iya cewa komai duk da naji daÉ—in abin da suka mun har cikin Zuciyata.

Itafa ƙasar nan tamu ta gado sai Kana da wanda ka sani,bafa wai baza a iya bane lalacine kawai irin namu,yaran da suka wa Baba Sharri babu wanda ya tuhumesu ko ya yi tunanin karya suke,an magana sunce ai rai shida baza suyima mutum guda ƙarya ba,amma menene hikimar bincike?.Baba fa duk Wannan baƙar Azabar bai amsa laifinsa ba amma har ake ƙokarin tura su kuto,mu dai ba bincike aka zo akayi gidanmu ba amma sai cewa sukayi an tara hujjojin da zasu kai su Baba kotu,da Daddy ya shiga a wunin Ranar aka fito da Ogansu Bamaiyyi inda suka ƙaryata kansu suka tabbatar da sharri sukayi wa Baba, bincikene wanda da ace anyi tun farko da ba'a taɓa wanda baiji bai gani ba,sai gashi da sanannen ya shiga anyi abin daya kamata ace anyi,wata shari'ar sai a lahira domin duk inda Baba ya juya ya ji azaba sai ya tsinewa masu hannu da tsaki da suka jefa shi cikin jidali.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ 16:call it a day

Jinya Baba ya fara cikin samun kulawa daga iyalansa, Álhamdulilah ana samun sauƙi dan bakinsa da ya kumbura ya sauka,muna dai shan yan dubiya,kama daga gurin Aikinsu har zuwa maƙota, ranar gidan su Anisa baki ɗaya suka zo sake duba shi,a nan ne Mama ta samu tayi musu isasshiyar godiya , kayan marmari da abubuwan taɓawa suka kawo mishi,fruits kam baya yankewa dan ko bamu siya ba Anisa zata zo takanas tace Daddy da Enen sun aikota ta kawo,sun bamu kulawa yadda ya kamata domin a wannan stage ɗin kallon yan uwa na fara musu ba iyayen ƙawa ba.

Yaya Halil ya kan Kirani mu gaisa Sama sama ,na kasa samun ƙarfun gwiwar ƙin ɗauka mishi Wayarsa sai nake jin wannan Alheri da ya mun ya sanyaya mun Zuciya duk da ban manta yaudarar da ya mun ba,amma kamar yadda ya faɗa sai na ɗauki matsayin Yaya na bashi,akwai ranar da ina tare da Anisa ya Kirani kamar ba zan ɗauka ba amma sai na ɗauka,jin na ambaci Sunansa ya saka ta juyo a ɗari tana kallona.

"Yaya Halil kuma?"

Ban kulata ba sai da muka gama kafin ta sake dawowa kusa dani tana mai faÉ—in"kada ki ce mun ruwa ki ka koma".

"Ruwa kuma?".

"Eh mana,kada ki ce mun Yaya Halil ya samu nasara wajen yaudararki da daÉ—in baki ku dawo Soyayya da shi after duk abin da ya yi miki".

Dariya nayi ganin yadda ta zazzare ido tana san jin amsata,"calm down babe babu abin da ke tsakanina da Yaya Halil bayan mutunci,after duk abin da ya yi mun kina tunanin shawara ce mai kyau na ƙi gaisawa dashi?Anisa wani lokacin ya kamata muna kallon Alheri kafin mu duba sharri,Yaya Halil bai Aureni ba haka Allah ya ƙaddara,duk abin da Ubangiji ya yi shine dai dai, Kingani komai ya zauna a gurinsa mai zai hana a cigaba da rayuwa kamar ba'ayi ba a manta abin da Ubangiji bai nufa ba?".

"Amma Zunairah wannan abin fa akwai haɗari,da kike faɗin ya taimakeki ince Daddy ne kan gaba,mene ya yi Bayan zuwa ya tsaya har abin ya ƙare sai Umarni da Daddy ya bashi ya kawo Baba gida,kada ki bari ki koma baya kan namijin da bai cancanta ba, wallahi idan ki ka ce zaki Auri Yaya Halil Babu abin da zai hana matarsa banka miki wuta ki mutu dan bata da hankali".

Ganin yadda tayi maganar da gasken gasken ya saka nima na saka tawa gasken waje bata tabbaci,"Anisa ba zan auri Yaya Halil ba koda zai rabu da matarsa ,na san you're looking out for me amma ki ƙwantar da hankalinki,irin wannan alaƙar ta yanke tsakanina a Yaya Halil ".

"Da gaske?".

"Insha Allah,yanzu dai ki cigaba da duba mun Draft É—in page É—in nan da zan É—ora anjima kada ki damu idan aka fara bani contract a Dreame zaki dara ".
Chapter 21 · 0% Book details