← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 28

Sashe 6

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ƙwana huɗu da gama makarantar mu,ina zaune ina gyarawa Mama egusi seed kafin ta dawo daga Barka da taje unguwa uku gidan wata ƙawarta,so nake nayi na gama na ɗora mata tuwan dan na rage mata aiki,na san halin Mama bata so a sa mata hannu a egusi ɗinta shi ya sa ban ma yi attempting ba Illa gyarawa da nake,ina san Miyan Egusi ɗin Mama daɗi kamar kada ka daina sha.

Hauwa'u da Muhammad tare suka wuce islamiyya babu ɗan tayani hira sai sabuwar wayata da na ƙunna Haddar da zan bada ina ji lokaci guda kuma ina aiki,ƙofar aka ƙwanƙwasa kafin Kuma Muryar wani yaro ta bayyana inda yake cewa "wai ana sallama da Zunairah ".

Wani irin faɗuwa gabana yayi dan sabon abu ne,Ni dai na san bani da wanda zai zo gurina dan ni ba saurayi gareni ba saurayi kuma shine kawai zai tsaya ƙofar gida yace ana sallama

"Zunairah kuwa?"na tambaya jin yaron bai bar gurin ba.

"Eh wai inji Halil"ya bani amsa yana mai barin gurin,da Mamaki nake sake maimaita sunan,wane kuma Halil?kamar ba zan fita ba sai kuma dai na aje tray ɗin na shiga ɗaki na ɗauko ƙaton hijab ɗina na fita,Turus nayi lokacin da idanuna suka sauka kan nasa,jingine ya yi jikin mota hannayensa naɗe bisa ƙirjinsa,baƙin yadin da ke jikinsa ya saka haskensa ya bayyana, Murmushi yake watso mun wanda yake bayyana haƙoransa,gira guda ɗaya ya ɗaga mun gannin na tsaya ni ban koma ba ni ban ƙarasa ba.

"Ko ba a maraba dani na koma?"

"A'a Yaya Halil ina dai mamaki ne yadda ka san gidan"takowa nayi ina mai bashi amsa har na isa inda yake ina mai yin ƙasa da kaina na gaishe da shi cike da girmamawa.

"Lafiya lau yan mata sanin gida kuma ki daina mamaki ai mai san ɗaukar abu a guri baya bari ya yi ƙasa a gwiwa,well ranar graduation ɗin ku na bi ku a baya,I'm sorry idan nayi ba dai dai ba i just can't help it,like I promised na ce zan zo sai yau Allah ya bani iko".Buɗe gidan zaman baya ya yi ya ciro wata leda ya miƙa mun yana mai ƙarawa da cewa"ga kyautar ki,kamar yadda ki ka gargaɗeni a wayau ban sai waya ba,yanzu tunda ga waya a hannunki sai ki saka mun number ɗin ki".

Kallan wayar dake hannuna nayi kafin na kalli leɗar,kamar ya san zan kawo uzurin da zan ƙi karɓa ne ya ce"bana san a mayar mun da kyauta, dan ke na siya kuma zaki karɓa idan ba so ki ke na je na faɗawa Mama ba,dama ina so na shiga mu gaisa".

Hannu na saka na karɓa ina mishi godiya kafin na faɗa mishi Mama bata nan ni kaɗaice a gidan,ganin yadda nake ta jin kunya haka nan ya saka bai ja ni da surutu ba ya mun Sallama a kan za muyi waya,haka nan naji ni cikin wani irin nishaɗi da ni kaina ban san ya akayi na faɗa cikin ba,wani irin burgeni kawai na ji ya yi,idan za a tambayeni zaɓina dangane da namiji,zan iya cewa ina san mutum kamar Yaya Halil dan ya haɗu ta ko ina ,ɗan gayune sosai .

Leɗar na buɗe dana shiga gida ,kayan ƙwalliya ne da Turaruka sai kayan cimma na ƙwaɗayi,wani ɗan box ne a wrapping wanda ke ɗauke da note ɗin da ya saka gabana Faɗuwa sosai,I LOVE YOU ZUNAIRAH,na karanta ya fi a irga ,buɗewa nayi ina mai zaƙuwa da san ganin menene a ciki,wani zobe ne wanda aka saka kalmar Z a cikin glass ɗin sa,ni dai ba sanin zobe mai tsada nayi ba amma daga gani mai tsada ne yadda yake ta ƙyalli abin sa,to na dai karɓi kaya ban san ta yadda zan faɗa ga yan gidan mu ba,zance na ɓoye ma bai taso ba Mama kawai zan fara faɗawa,da haka na yanke shawara da Zuciyata na kai kayan ɗaki na aje.

Na gama ƙwashe tuwo na saka a leda kenan wayana ta hau ruri,number ce wadda truecaller ɗin ke Bayyana Halil Ibrahim, murmushi na tsinci kaina da yi kafin na ɗauki wayar bakina ɗauke da sallama,ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce"har na fara jin tsoron baza ki ɗauka ba".

"Saboda mene ni kam zan ƙi ɗauka?na buɗe kaya nagode duk da sun yi yawa Yaya Halil".

Ƙaramun murmushi yayi wanda ina jin sautinsa kafin yace"I guess kinga rubutun ciki mene amsa ta?".

Wani irin kunya naji ina ji kamar wanda yake tambayata a gabana,tsintar kaina nayi da cewa "Allah ya sa ba tsaddaden zobe bane dan bana san in fita dashi a hannuna a sace ni".

Cike da murna da san fahimta ta ya ce"kenan na samu ƙarɓuwa?, look Zunairah I've been having crush on you,tunda na ganki na farko naji kin burgeni,that's of course lokacin da ki ka fara girma,amma a ranar da na sake saka ki a ido a makarantarku,kin tafi da komai nawa da zan iya sauke wuyana ki hau,da gaske ina sanki Zunairah kuma Aurenki nake so nayi,amma ba zan miki dole ba idan ban Miki ba ki faɗa mun kin ji?"..

Idan ance na kwatanta kaina a kan sikeli na ɗari a wannan lokacin ban ma san a nawa nake ba amma fa Yaya Halil ya ƙwamishi zuciyata duk da irin abun nan na mata zai hanani bada kaina da wuri dan haka na nemi da ya bari nayi tunani.

Murmushin ya yi yana mai cewa "na samu karɓuwa kenan,ki ce na gyara zamana ,kin san idan mace tace za tayi tunani yana ɗaya daga cikin alamun nasara,yanzu dai ki ce naje na fara tara sadaki?".

Kunya ta saka na kashe wayar ina mai jin Zuciyata na bugawa da sauri da sauri,na kasa yarda wai na samu soyayya a gurin da bana tsammani,wai ni da Yaya Halil?abun kamar almara,wayata na kunna na shiga last call ɗina da nayi da Anisa,na daɗe da number ɗinta a rubuce dan ta saka na mata alƙawarin ina samun waya number ɗinta zan fara kira,ana siya mun Sim kuwa ita ɗin na fara kira inda ta nuna mun murnarta kamar ma ta fini har tana faɗin itama ƙawarta ta fito fili,Sai da ta gama ringing ba a ɗauka ba,har wani tsuma nake burina na ji na fesa mata soyayyar da na samu daga yayanta,na san ba ƙaramun farin ciki za tayi ba ,ina ƙokarin sake kira kiranta na shigowa,cike da zaƙuwa ta ce"Besty guess what?Ina ta san kiranki ki ka kirani ya I've found love,baki ganshi ba ya haɗu iya haɗuwa,yaran ƙawar mummy ne Khalifa wannan immigration da na faɗa Miki ina having crush a kansa,kin gane sa?".

Da murnar da na kasa ɓoyewa na kaɗa kai kafin na ce "Finally babe crush ɗin da ki ke bai tashi a banza ba,i can't believe this,tell me more".

Cigaba tayi"ina faɗa Miki Walimar da Aka haɗa mun a gida suka zo to cut the story short bai tafi ba sai da ya faɗa mun yana sona and of course na amince,ki fara tanadar duk wani abu da ki ka san Aure ya ƙunsa,we have a wedding to plan".

"To hajiyata ,yaushe aka fara soyayya da har kin fara maganar Aure?"..

"Hmm Ohunene,you see that guy?he's mine and Idan ina kallansa ji nake kamar har mun yi Aure,muna nan da ke Aurena dana Yaya Halil za a haɗa dan daga samun budurwa jiya jiya har ya fara maganar Aure,ke ki ji zaƙewa da Daddy ya tambayesa sun daidaita wai sai cewa ya yi tukunna dai"dariya ta saka sosai a ƙarshen maganar ta kafin ta ƙara da cewa"Allah ya sa ba gaja bace ko wata ƴar talakawan yaje ya ƙwaso dan Wallahi idan bata mun ba ubanta zataci".

Wani irin faɗuwar gaba naji ya sauka min, Chanza shawarar faɗa mata ɗin nayi na ja bakina nayi shiru har muka gama wayar duk da yadda zuciya ke ce mun na faɗa mata ɗan Wannan karan shine farko da na fara ɓoyewa Anisa abu,haka nan sai na tsinci kaina da tsoron faɗa mata nice duk da na san zata ji daɗi atleast ni ɗin aminiyarta ce dan haka na sake ɓalle maɓallin Zuciyata dan adana soyayyar Yaya Halil ta yi yaɗuwa,na san wannan karan ba zan samu karayar zuciya ba.

Da mama ta dawo kamar munafuka haka na shiga É—akinta,doguwar rigar da ta fita da ita take cirewa tana faÉ—in"bari na zo na É—ora miya Allah ya sa baki É—ora mun ba".

"Ban ɗora ba amma Mama na kusa fara ɗorawa idan bana ɗorawa ɗin yaya zan iya?"na faɗa ina mai zama kan carpet da ledar a hannuna kamar wadda ta ƙwaso ganimar yaƙi.

"Shi ya saka ai nake yi tare dake ,tunda komai tare muke yi,so ki ke ki lalatani idan kin fara makaranta ko kin yi Aure na shiga ta kaina,ki dai biyoni kitchen mu yi tare".

Ƙarasa saka hannun rigar ta tayi kafin Idanunta suka sauka akan ledar da nake ta chikukuyewa baki.

"shi wannan É—in mene a ciki?"

"Mama dan Allah kada ki yi mun faɗa ban roƙesa ba haka nan ya kawo mun and sai da na ce mishi ya yi yawa amma ya dage sai na karɓa wallahi ban roƙeshi ba".

Hular dake hannunta ta saka ta ƙaraso inda nake ta zauna tana mai faɗin "taƙaita mun zance?wane shi wane ya baki let me understand "saurin tashi nayi ta kamo hannuna ta zaunar tana mai faɗin "Izewano?(Ina zaki?) Mene a cikin ledar wane kuma ya baki?".
Chapter 6 · 0% Book details