← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 28

Sashe 4

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anisa was not expecting that dan tunaninta ƙokarin zunairah science zata kaishi,burinta bai wuce ta zama Doctor ba domin a tunaninta itama Zunairah haka ne dan har ta fara tunanin yadda za su fafata a Wannan fagen amma wai aikin jarida,haka nan ba dan tana so ba itama ta zaɓi Art ,abun da ke ƙona mata rai shine idan Zunairah ta ce mata wai ba purpose ɗinta bane,yo ai ta daɗe da aje wani purpose da kowa ke tunanin, purpose guda ta riƙe wanda shine wuce Zunairah a rayuwa.

A ƙofar gidan su Adam driver ɗinta ya faka ta fito,kai tsaye ta shiga tana mai share gateman ɗin dake gaida ta ,shi kuma kamar masifa Indai zai ganta sai ya gaisheta.

Kai tsaye tana shiga ta murɗa handle ɗin kofar falon ta shiga tana ƙwala mishi kira,jin bai amsa ba kuma tana jin motsi a sama ya saka ta haura ,duk takunta nishin da take ji yana kusanto ta,daga ɗakin yaya Adam ne,kai tsaye ta isa ƙofar ta murɗa,ba tayi mamaki ba ganinsa tayi kan mace yana ta aiki ita kuma tana ta faman surutai,basu ma san ta buɗe ƙofa ba dan haka ta koma dan jiransa dan ta san last abun da za tayi shine katsesa,iyayen Yaya Adam sun tafi vacation dan haka gidan ya zamana a hannunsa shi kaɗai yake sheƙa ayarsa.

Bayan wasu lokuta taji suna saukowa suna ƙananun dariya,macen ta fara ganinta ,cike da tsoro ta dafe ƙirjinta dan bata yi tunanin ganinta ba dalilin hakan ya saka ta tsorata.

Tsaki Anisa tayi tana mai bin su da kallo,yaya Adam ne ya sauko yana faÉ—in"sis Ani yaushe ki ka zo,You should have call me".

Wani kallon ta masa kafin ta saka hannu cikin jakarta ta ciro wayar ta miƙa mishi ta ce"Zunairah taƙi karɓan wayarka Sannan ta ce dan Allah ka rabu da ita and Nima da nazo gidan nan na goyi bayan ta domin da ace na san kana fucking Yaya Hibba ba zan bada gudunmawa ta ba".

Da sauri Hibba ta matso inda take tana cewa"innallahi cousin sis ta yaya zan fucking Yaya Adam?he's my cousin for God sake,Allah ya kiyaye, besides ni ba mazinaciya bace kada ki sake dangantani da wannan harkar ".

Dariya Anisa ta saka sosai kafin ta sake miƙa masa wayar da yaƙi karɓa yana kallon ta"yaya Adam ka karɓa na wuce dan Allah,dan naga alamun yarinya ake san mayar Dani,for your information Yaya Hibba kina wannan Surutan na shigo baku ma san na shigo ba and ni a samanki naga Yaya Adam and it doesn't seem like yana koya Miki assignment ne".

Shiru duka suka yi ,ganin ya ƙi ƙaraɓar wayar ya saka ta aje mishi kan kujerar ta juya ta fita ,biyo bayanta Hibba tayi tana mata Magana amma tayi mata banza.

Hibba yarinyar ƙanwar Mahaifiyar Adam ce,bangaren Anisa kuma yarinyar ƙanwar mahaifintan ce, tunda mamanta ta rasu ta baro Nassarawa ta dawo gidan su Anisa ,duk yadda mutanen ƙauyen Aila na ciki Benue suke mitar ta dawo ta zauna da yan uwan mahaifinta abun bai iyu ba dan a cewar Mahaifin Anisa Hibba baza ta iya zaman ƙyauye ba tunda ko iyayenta ɗin cikin Lafiya na Nassarawa suke da zama,tun lokacin ya dawo da ita gidansa.

Anisa ta ji daÉ—in zuwanta dan dama bata da yar uwa Yaya Halil kuma ba mazauni bane ,idan ma ya zauna ba hirar da take sakewa ba suke, its always about school da abin da take so a siya mata ,babu zaman wannan gossip É—in na mata,amma Hibba kuwa zasu zauna su É—an tattauna abin su duk da cewa Hibba É—in ta bawa Anisa kusa shekaru huÉ—u.

Abin da ya ɓata mata rai da abin da ta Kama suna yi da Adam shine ɓata mata Rayuwa da yake,ta san Yaya Adam baya ji amma bata taɓa tunanin zai bi ta gida ba ,a hakan ko Zunairah a wannan gaɓar dai bata fatan mata ya lalata mata rayuwar,Hassadar da ke tsakaninsu bata tunanin a Zuciyarta ta kai wannan stage ɗin,wani lokacin idan tana irin wannan tunanin sai tama rasa ina ne ta dosa a tafiyar,shin har yanzu tana san Zunairah ɗinne kamar farko ko kuwa competition,idan competition ne mutane kan bin ko wane irin logic domin gannin sun cinye amma a Wannan gejin ta fi son Free and fair competition,bai kai deep ɗin da zata so Adam ya lalata ta ba dan haka dole Ya manta da Batun Zunairah.

Tana shiga gida a falo ta tarar da mahaifiyarta tana kallo,abun da ta tsana ta tambayeta shine abin da ya fara fita bakinta bayan sun gaisa,wai ina Zunairah.

"Tana lafiya"ta bata amsa a taƙaice kafin ta yi ƙokarin shiga ciki domin Cire kaya.

"Ya kamata dai ta kawo mana ziyara ".

Tana jin Muryar Enen na mata maganar tayi mata banza ta wuce ciki, enough Zunairah drama for the day,sai a jira na gobe (Enen da Idoma shine sunan da Anisa take kiran mamanta,ma'ana Mama).

Bata jima da dawowa ba Hibba ma ta dawo a tsarge domin duk a tunaninta Anisa ta faɗa abin da ta kamata tana yi,idan kuwa ta tona mata Asiri ta shiga uku dan ta san ƙarshen zancen sai ta koma Benue ,ganin sun gaisa da Enen faran faran ya saka ta doshi ɗakin Anisa,kwance ta tarar da ita kan cikinta tana danna waya,zama tayi gefenta,ko kallonta Anisa ba tayi ba ta cigaba da taɓa wayar cike da tsoro ta fara magana .

"Nisa I'm sorry Mana,it's not like Ina bin maza ne,Ni da Yaya Adam muna soyayya ne and bana tunanin big deal ne dan mun ƙarama soyayyarmu ɗanko ,i just want you to understand Aurena zai yi".

Da Mamaki Anisa ke kallonta kafin ta ce"shi Yaya Adam É—in ya ce zai Aureki?".

"Eh".

Wani dariya tayi ƙarama kafin ta tashi ta zauna ta kamo hannun Hibba."yaya Hibba you deserve better than Yaya Adam, he's a user and definitely yana using ɗinki ne kawai dan ya biya ma kan sa buƙata amma there is no way on earth da Yaya Adam zai yarda ya Aureki bayan kin bashi jikinki,wallahi ƙarya yake,I'm not judging you tunda abin da ya faru ya riga ya faru amma gaskiya ki fita harkarsa If not zaki barni da rashin zaɓi na faɗawa Enen".
"Insha Allahu ba zai kai nan ba ma Neesa na rabu da shi I'm sorry".ta faɗa cikin zaƙuwa da san Anisa ta yarda da ita amma babu ma yadda zai iyu ace wai ta rabu da Adam zadai ta zama careful gaba kada a sake kama su."
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)

EPISODE 4:when life gives you tangerine

*𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷*

Kamar da wasa muka fara zana jarabawa har ya kai da muna kan rubuta tourism paper ɗin ƙarshe,dukkan yan set ɗin mu kowa uniform ya sha guga ga graduation gown da muka sha Sky blue jira kawai muke mu gama muje mu haɗu da iyayenmu dan ko ni tare muka zo da Baba da Mama,dama su Hauwa'u an basu hutu, Theater Hall ya sha decoration inda nan aka aje iyayen Yara inda mu kuma muke jarabawar ƙarshen mu cikin Rehearse Hall,baki ɗaya papers ɗin a Theater Hall muka yi kasancewar ya fi girma da ya zamana kuma za'ayi amfani da shi sai aka gyara mana Rehearse dan mu yi a ciki.

ZumuÉ—i kawai nake da murnar da ya saka ina gamawa ban tsaya wani Cross checking ba nayi submitting,dama Tourism ba wani wahala ne da shi ba,ina fita Anisa ma ta fito,cike da wani irin ihun murna muka rungume juna muna masu faÉ—in"we are graduates"

Sir Umar Ali ne ya leƙo yana mai faɗin"Mss Buhari and Ms Ibrahim I'm sure kun san wasu basu gama exam ba,so I will appreciate it idan ku ka samu guri ku ka zauna har yan uwanku su fito ku yi making entrance cikin Theater Hall as real graduates".

Ƴar dariya muka yi a tare kafin muka samu guri muka zauna hannunmu cikin na juna ,cike da zaƙuwa Anisa ta ce"best farin ciki nake wallahi na kasa yadda wai yau zamu bar bright scholars,and guess what yau har da Yaya Halil aka zo mun".

Ganin yadda take ta giggling ya tabbatar mun tana cikin farin ciki ɗin har zuci musamman batun zuwan Yaya Halil, he's always absent duba da yanayin aikinsa gashi Anisa na masifar ƙaunarsa kamar ranta.

"Gaskiya dai Yaya Halil ya kyauta da ya samu zuwa"na faɗa ina mai tayata murna.sake damƙe hannuna tayi tace"girl I'm beyond happy,ai ya sani na faɗa masa idan bai zo ba wallahi sai bikinsa zan tsiro zuwa ƙauye,matarsa kuma bani babu ita ta kuma haɗu da ƙanwar miji".

A tare muka saka dariya ina cewa"wa ya ga Anisa ƙanwar miji da kanta".

Muna nan zaune aka fara fitowa kowa da nashi salon nuna murnar,bayan duk mun gama fitowa Principal ɗin mu da taci gayu cikin kaya kalar graduation gown ɗin mu ta shigo tare da vice ɗinta da sauran malamai,cike da murna tayi addressing ɗin mu kafin muka haɗa layi guda,tana gaba crew na kiɗa na baya,a haka muka fita da parade har cikin Theater Hall,abun gwanin sha'awa haka appearance ɗin mu ya kasance ga iyayen mu,sai da muka shiga kafin kiɗan ya tsaya,tafi gurin ya ɗauka ganin yadda duka muka cire hulunan mu maka ɗora so a kafaɗa muna masu musu duƙan girmamawa da kai,kai kace a command muke,gurin muka samu muka zauna banda masu muƙami,dama Ni ba prefect bace,Anisa ce labor prefect ,layi sukayi su shida inda shadow prefect ma su shida,vice principal ne ya sanar da handing over da zasuyi na beret ɗin su,dama abun ka da aka daɗe ana practice kada aji kunya,band ne suka fara ƙida inda prefects ɗin suke parade a hankali suna masu bin ƙidan,umarni commander na parade ya basu da su cire hulunan su su ɗora bisa kafaɗa,suna cirewa suka taka da parade zuwa gaban shadows ɗinsu ko wacce ta ɗora beret bisa kan wadda zata maye gurbin ta,tafi gurin ya ɗauka inda iyaye da dama suka tashi suna ɗaukar hoto da bidiyo, bayan sun gama kowa ya koma ya samu guri ya zauna.
Chapter 4 · 0% Book details