← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 28

Sashe 13

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan mun gama dukkan wani activities na school muka fita don tafiya gida,muna tsaye muna jiran keke ta ce mun"Daddy zai siya mun mota Kinga mun huta na aje ki gida nima na wuce,bana san driver yana kawoni makaranta ,I need my space ".

Murmushi nayi nace"Allah ya tabbatar da Alheri"wayarta ta ciro ta fara nuna mun hotunan motoci,wata Prado mai kyau ta nuna mun ta ce irinta take so a siya mata,sai na tsinci kaina cikin mutuƙar farin ciki har inda tsokanarta wa ya ganta gaban mota.

Haka muka sha hirar mu ,ni aka fara saukewa ina ƙokarin bashi kuɗi ta hanani ta hanyar cewa "ki bari zan bashi"cike da naci nace gaskiya ta bari na biya amma ta ƙiya har mai adaidaita sahun ya kunna ta leƙo da kanta tana kallona kafin tace "Besty i will appreciate it idan ki ka kawo ƙarshen Puppy love ɗin dake tsakaninki da Yaya Halil dan bana goyan baya bazan bada goyan baya ba kuma,sai dai idan zaki zaɓi soyayya sama da ƙawance da muka daɗe muna ginawa ni dake,Code ɗin basa da yawa,Don't date my brother and don't date my ex ".

Kafin na fita daga sukar da maganarta ta yi mun ta umarci mai Adaidaita sahun da ya ja su wuce,kamar wata bebin roba haka na tsaya ina bin hanyar da kallo har suka ɓacewa ganina,ban taɓa tunanin wai Anisa zata ce na zaɓi ita ko Halil ba, shin mene ma ya haɗa ƙawance da kuma abin da nake dashi tare da Ya Halil?shi kuma wannan sababbin abin da ba zai saɓu ba da take kira code daga ina aka samo su?.

"Aikuwa Wallahi Aunty bata isa ba, wai ki zaɓa ko ita ko Yaya Halil, wannan ɗin wane irin banzan Code ne?"

Juyawa nayi jin Muryar Hauwa'u,cikin ɓacin rai nace"laɓe ki ke mun ko?".

Ɗaga hannunta tayi sama ta ce"wallahi A'a Auntymu Fitowa kawai nayi fa zani shagon dan Fulani na siyo siga na tsinkayi maganar ta ki yi haƙuri".

Raɓawa nayi ta gefenta ina cewa "saura ki faɗawa Mama dan Allah zaki ga ya zamu ƙare ni dake "da haka na shiga ciki ita kuma ta fita,Mama na tarar tana hira da Aunty Muna wata yar Yaren mu da suka tare bayan layinmu,tunda taji ana kiran mu gidan Ebira ta shiga jikinmu ,take kuma sai ta samu shiga ,abunka da anga yan yare guda sai ya zama kamar yar uwarmu,dan wasu ma cewa suke muna da alaƙa dama,gaishe su nayi Mama ta mun sannu da zuwa inda take cewa akwai Kunun gyaɗa a kitchen naje na ɗauka na sha ta saka mun siga tuntuni ta aje mun,su kuma su Hauwa'u ta basu suje su siyo.

Tasan wani lokacin ina shigowa gida ina kukan yunwa shi yasa takan fara aje mun Abu mai ruwa ruwa,kunun na ɗauko na shiga ɗaki ,duk yadda nake san kunun gyaɗa sai naji na kasa sha,Anisa ta Shammaceni,ashe duk share zancen da take tana jirane mu zo rabuwa kenan ta faɗa mun bata yadda ba,to amma dole sai ta yarda zan soyayya i Zunairah?bansan yaushe wannan dokar ta shiga tsakaninmu ba,gaskiya zan amince da komai banda barazana da abin da na gama sawa rai,bana wasa da soyayya musamman a yanzu da na samu wanda nake so yake sona,dole ne idan Anisa na sona da gaske kamar yadda ta faɗa tayi Farin ciki da farin cikina,ban taɓa kin abu idan tace ba sanin ba zata cutar dani ba,amma a wannan karan kuwa dole ne Anisa tayi haƙuri ta Barni da abin da nake so dan bana tunanin zan iya ɗaukar wani heartbreak ɗin a karo na biyu,nayi nisan da idan aka mun haka zan samu matsala ainun.

Sakin jikina nayi na cigaba da hidimomina inda har kirana Yaya Halil ya yi ya shaida mun zai zo,ban saka komai a raina ba ban kuma faɗa mishi ya muka yi da Anisa ba muka sha soyayyar mu ya tafi,kamar ba muyi faɗa ba sai komai ya dawo kamar ranar da muka fara musayar kalmar soyayya,har na ƙwanta ina sake tabbatarwa da kaina ba zan bari wannan damar ta ƙwace mun ba musamman yadda na ga murnar da yake jin nace ya sanar da su Enen abin dake tsakanina dashi,har yana tsokanata da kawai gobe zasu zo. introduction.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
08130229878
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ10.Love or Friendship

*𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈*

Tana jin tashin hankali tana shiga tashin hankali amma wanda take ciki a yau ba ƙarami bane,jin kalmar Yaya Halil na soyayya da Zunairah kawai sai da ya so ya tsayar mata da dukkan wani tunani da take dashi,ina ma hakan zai iyu?ai wallahi ko ana muzuru ana shawo babu uban da ya isa ya haɗa wannan alaƙa ta zuba mishi ido,Yayanta fa wanda take ƙauna,taya za ace ta zuba ido tana kallo Zunairah ta ƙwace mata kashin soyayyarta,ba zai iyu ba ba zai faru ba.

Haka wunin ranar ta yi tana ƙunci duk da ta rasa ta inda zata fara ta kuma rasa wanda zata tunkara da maganar,tana zaune falo tana tunani Muryar Mahaifiyarta ta datseta inda take cewa"Aikuwa Halil kayi kyan kai da ya zamana Zunairah itace wadda ka ke so ,Anisa kinji wani labari mai daɗi kuwa,ko da yake ai wannan labari ma ke ya kamata ki bani karin haske".

Turo baki tayi gaba ta tashi tana mai cewa "aikuwa "cikin ɗaki tayi zuciyarta na mata ɗaci musamman da ta lura da yadda Yaya Halil ke washe baki,aikam zai yi ya gama dan wallahi dole ne a watse,daga ɗaki tana jin yadda Enen ke murna kamar wadda aka bawa duniya ,tayi tsaki yafi a irga ,kwanciya tayi tana ta juye juye kan gado ,ji take ƙirjinta na mata wani irin zafi kamar zuciyarta zata fasa mata ƙirjinta.

Haka ta wuni ranar kafin ta samu kwarin gwiwa da dare wuraren tara ta nufi ɗakin Halil,tsaye tayi tana tunanin ta inda zata fara,kafin ta ƙwanƙwasa ya fito,kallonsa tayi cike da fargaba ta ce"fita za kayi yaya Halil?".

Kallon kansa ya yi kafin ya kalleta ya ce"da daren nan ni kam Nisa ina zanje , besides singlet fa ki ka gani jikina".

Turo baki tayi ta ce"na sani ko gurin Zunairah zaka and ai ba zan mamaki ba idan kaje da singlet É—in maybe ta koya maka abin da bai kamata ba".hannu ya saka ya yi folding yana mai kallonta kafin ya ce"mene maganarki ke nufi Anisa?".

Juyawa tayi tana cewa"shikenan ai yanzu ina magana sai a fassarani,amma ni ka sani brother babu wanda ya damu da damuwarka sama dani".

Cikin rashin sanin inda ta dosa ya kamota ta kwalar rigarta,sai da ta dawo tana kallosa kafin ya ce"me ki ke nufi?wani abu ki ke ɓoye mun?".

Dan kalle kalle ta fara kafin ta rage murya kamar tana tsoran kada wani ya jita kafin ta ce"muyi magana a ciki yaya bana san wani ya ji".bai mata musu ba ya juya ya koma ciki ta bi shi,zama tayi bakin gadonsa kafin ta tattara dukkan kwarin gwaiwarta ta ce"Yaya Zunairah aminiyatace ,babu wanda ya santa fiye dani,and na yi imani da Allah ba matar da zaka Aura kayi alfahari da ita bane,na san abin zai baka mamaki kace daga bakina wannan maganar ke fita,amma ina so ka sani wallahi ba sharri nake mata ba,and ba wai ina cewa bata da hali mai kyau bane,dan har gobe bana da ƙawar da ta wuce ita amma dai Maganar Aure gaskiya bana goyan baya".

Daga zaune kan mudibin da yake ya kura mata ido bai ce komai ba,ganin yana mata irin wannan kallon ya saka tace"yaya baka ce komai ba".

"Uhum ina sauraranki dan baki faɗi maganar da ya kamata nace komai ba har yanzun,ita Zunairah ɗin mene tayi ,tana da mugun hali amma ki ke tare da ita,ina ƙoƙarin na saka maganarki kan sikeli ne na Auna dan ban san taƙamaimai ina ki ka dosa ba".

Ɗan cije leɓenta tayi ta ciro wayarta tana mai cewa"zan nuna maka wani abu amma dan Allah yaya ka rufe mata sirrinta bana san kowa ya sani,and ka san mene yafi damuna,da ace zata canza da tuni ta canza amma bata da tunani na sake ɗabiun banzanta".

"For God sake Anisa idan zaki nuna mun ki nuna min,idan ba haka ba ki bari nayi relationship ɗina in peace"ya faɗa cike da ƙosawa.

Bata tsaya further ɓata lokaci ba ta kunna masa abin da take kira well kept evidence.

*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏 𝘗𝘖𝘝*

Introduction to mass communication shine first period É—in da muke dashi,yau ko da na shiga makaranta na É—anyi latti amma sanin malamin baya da matsala sai abun bai dameni ba,ban mamaki ba ganin Anisa bata jire mun guri ba sannan bata kirani ba,idan ta rigani shiga aji takan kirani tace mun an shiga,zaune take tare da wata course mate É—in mu da suka fara shiri kwana biyu Safina Bala,sai wani Saurayi da ban wayi sunansa ba danni bana da wannan shige shigen.

Class rep ɗin mu Imran ne ya mun guri na zauna har yana tsokanata yau akwai Quiz yana tare dani ya san zamu buge kowa,haka aka yi Quiz ɗin roll ɗin mu muka ci na farko,Use of English ne second period mai ɗaukar mu ya sanar da class rep ba zai samu damar zuwa ba dan haka sai ya zamana 10 mun zama free ,ina haɗa kayana dan tafiya gida Anisa tazo tana mai cewa"ƙawata yau mene ya saka ki latti?".

Dan murmushi nayi ina mai kallanta na amsa mata "ban samu abun hawa bane da wuri wallahi shi yasa nayi latti,and kin san Malam A Bello baya da matsala shi yasa ban damu ba ,da dai A A Garba ne na san Dama ba zan samu aji ba".

Jakata da nake ƙoƙarin ratayawa gefen Kafaɗata ta karɓa ta rataya ,kallonta nayi ,gira ɗaya ta ɗaga mun tana mai cewa"zaki iya amfani dani matsayin mai riƙe Miki jaka indai zaki rakani".

"Ina É—in zan raka ki?".

"Kin san dai ai ba zan cutar dake ba,kizo muje dan Allah"ta faÉ—a tana mai kamo hannuna ,haka nan na bita ina tunanin yadda zata É—auki hukuncin da na yanke ,sai da na bari mun fita daga class nace ",Besty baki tambayeni decision É—in dana yanke kan yaya Halil ba".
Chapter 13 · 0% Book details