← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 28

Sashe 5

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai principal ta tsara komai dan kuÉ—in da muka bayar ba da wasa ba,ya ci sunansa kuÉ—i,bayan gudanar da bikin raba kyautuka inda naci har guda biyu,punctuality da kuma zama ciki head na top 5 É—in aji,Anisa kuwa guda uku ta samu,na aikin da ta gudanar da tana prefect da na zama ta biyu cikin top 5,da kuma na gayu,bata wasa ba da aje karin guga a kaya,iyaye suka fara fita kafin mu,muna fita na rungume Anisa ina tayata murnar kyautukanta,da murnar itama ta tayani har tana tsokanata tana cewa"na kwace mata head of top five but ta bar mun".

A haka muka riske iyayenmu a wajen gurin,ban mamakin ganin su tare da yan gidan su Anisa ba,ina zuwa Hauwa'u ta É—ane ni tana faÉ—in"congratulations love,yayata ta zama graduate"kowa sai da abun ya bashi dariya wanda ya saka naji kunya musamman ganin Yaya Halil yana darawa sosai,

"Sauka a jikina ni ji yadda ki ke kunyatani kamar wadda na gama University , secondary dai nagama"na faɗa ina mai ƙin sake haɗa ido da Yaya Halil wanda rabona da shi har na manta,zan iya cewa tun Muna primary,shekarun kam da yawa,ya sake kyau da Haiba abin sa kamar ba yayan Anisa ba dan ya fita kyau sosai.

Gaishe da iyayen Anisa nayi inda ta gaida nawa wanda suka amsa mu cikin soyayya,Daddyn Anisa ne ya dafa mun kaina ya ce"my daughter head of best five cikin class of 25, you're blessed,Allah ya Miki albarka,naji daɗi sosai"godiya na mishi ina mai jin Yaya Halil na kirana da Brainy ,ƙanwata kuwa batayi ƙasa a gwiwa ba wajen cewa:"ai Guruwa ka ke ji Yaya Halil,tana bacci ma tana karatu".dariya mukayi.

"Daddy atleast ka ce congratulations tunda ba na ashirin da biyar É—in naci ba".Anisa dake gefen Yaya Hibba ta faÉ—a.

ENEN ce ta yabeta ta hanyar cewa,"kin san muna alfahari dake ,shi yasa muna san kasancewar Zunairah a rayuwarki,Allah ya sake haÉ—a kan ku ya kawar da shaiÉ—an tsakanin ku".

"Amin"muka amsa a tare ,bouquet É—in Naira É—ari É—ari Hauwa'u ta bani tana mai cewa"gashi nan na 10k Ni da Muhammad,and I made it with love "ganin ina mata kallon ban yarda ba ya saka ta rumtse Idanunta ta ce"naji Baba ya cika mana amma ai zamu biya sa na faÉ—a mishi bashine so don't give me that look,".

Dariya Anisa tayi wanda ya Saka Nima ɗin nayi kafin na ƙarɓa bouquet ɗin da chocolate a wani ƙaramin box, Hauwa'u kenan akwai sai ire iren waɗannan abubuwan, hotuna muka ɗan yi kafin muka yi haramar kama gaban mu,gayyatar mu taron walimar da za a yi ma Anisa iyayenta suka mana amma Baba ya basu haƙuri kan Nima walimar zasu haɗa mun,sun so a haɗa amma Baba ya ƙi,haka nan suka haƙura.

Bayan kowa ya É—auki hanyar motar su na koma Hall dan nayi matuwa,ina jin Anisa na faÉ—a mun ita kam ta tafi mu haÉ—u wajen school.

Slum book É—ina na manta wanda dukkan wani detail na yan ajin mu yana ciki sun cike .

"Hope ƙanwata ta ga abin da take nema".

a tsorace na juyo dan ban yi tsammanin sa ba."Yaya Halil?"na faÉ—a cikin sigar tambaya,kan desk É—aya ya zauna yana mai É—aga mun gira É—aya kana ya ce"hala ba kiyi maraba da ganina ba,dama na zo ne na tayaki neman abin da ki ke nema,Allah ya sa ban laifi ba".

Murmushi nayi ina mai girgiza mai kai kafin na ɗaga slum book ɗin ina mai nuna mishi,karɓa ya yi,kamar ya buɗe sai kuma ya nuna yana murmushi ,hannu ya saka ya ciro bandir na kuɗi ya miƙa mun,kallon kuɗin nayi kafin na kalleshi,zuba mun ido ya yi Nima na zuba mishi,ki ƙarɓa tunda ban siya miki komai ba kuma kun ƙi yadda da zuwa gidan mu so wannan ne kyauta ta.

Girgiza kai na fara ina faɗin"Nagode Yaya Halil amma ba zan karɓa ba Allah,dan Allah kada kace sai na karɓa"ganin da gaske nake duk na ruɗe ya saka ya mayar aljihunsa ya ce"na ji amma zan siyo Miki kyauta na kawo Miki har gida amma sai kin karɓa".

Murmushi nayi ina mai yin ƙasa da kaina ban iya faɗin komai,wayarsa ya miƙa mun,kallon wayar nayi na kalleshi,."ki karɓa ki saka mun number ɗin ki,I'm very sure kin san ba zan gane gidan ku ba sai na kira ki".

"Yaya Halil ai bana da waya"na faÉ—a mishi ina É—an murmushi.

Da mamakin faÉ—in bana da waya É—in da nayi ya buÉ—e baki kafin ya ce"ki ce dai baza ki bani number É—inki ba saboda kada yayanki yace yana sanki".

Haka nan sai naji kunyar maganar sosai da ya saka na kasa haÉ—a ido dashi illa sake tabbatar mishi da nayi wallahi bani da waya,ya yi mamaki wanda ni ban ga abun mamaki ba ,haka nan muka jera a tare yana mai ce mun zai dai zo ko ya ya ne amma dole zai kawo min gift.

"I'm sure yanzu ina komawa gida zan tarar da waya Baba ya siya dan dama ya ce ba zai siya mun waya ba sai na gama makaranta".na tsinci kaina da faɗa Mishi gudun kada ma ya siya mun waya dan na san kaɗan daga aikin sa kenan ni kuma Allah ya san ba zan taɓa karɓa ba.

kawar da zancen ya yi ta hanyar nuna burgewar tsarin Baba,haka ya yi ta jana da wasa yana mai sake tabbatar mun ko da waya ko babu zai zo gida kuma muna da magana mai girma ,da haka muka yi sallama,already su Anisa sun wuce hakan ya saka ya wuce motarsa bayan ya sake sallama da su Mama.

Da muka koma gida ƙaramar walima suka haɗa mun ,mama Ta yi mun abinci mai daɗi da kaza Baba kuma ya bani kyautar waya ƙirar Infinix smart 10, Murna kamar zan yi mene,addu'a na ɗinga bin Baba da shi dan sosai naji daɗi wanda bana iya misaltawa,murnar da Hauwa'u da Muhammad ke tayani sai ka rantse su aka siyawa wayan,ina kan wannan murnar ban fita daga ita ba Baba ya sake kasheni da wata,hannunsa da ke miƙa mun Laptop nake kallo,nuna laptop ɗin nayi kafin na nuna kaina ina mai kallan Baba ,ƴar dariya ya yi ya kaɗa mun kai kafin ya ce"ga system nan saboda makaranta da assignment da ɗan abun da baza a rasa ba".ban san lokacin da na rungumesa ba ina kuka.

Haka ranar ta kasance mun ranar farin ciki da jaddada soyayyata da sake tabbatar da muddin na rasa dangina na shiga uku.

*******************************************

*𝙰𝙽𝙸𝚂𝙰*

Tunda ta shiga Mota wani tuƙuƙi ya tare mata maƙoshi Idanunta da tunaninta sunƙi fita daga bouquet ɗin da Hauwa'u ta bama Zunairah,ta san ba ƙaramun party za'a haɗa mata ba a gida amma ta so itama yadda aka kawowa zunairah money bouquet a kawo mata wanda yafi nata ,ga babban abin da ya sake shaƙa mata shine ganin yadda Daddy ke aikin koɗata dan ta ci na ɗaya,that was supposed to be her place amma ta sace Mata,tunda suka shiga motar take expecting mitar Daddy,ta so ta hau motar yaya Halil amma ya ce shi ba gida Zaije straight ba,har ta cire ran ba zai maganar ba ta tsinci Muryarsa yana mai faɗin.

"Yanzu Anisa baki ko da kunya ba,and baki jin cewa ya kamata ki Bama iyayenki masu sponsoring karatun ki haƙuri ba,i mean ina san sanin menene a upstairs ɗin Zunairah da ke naki upstairs ɗin babu".

"Amma Daddy da 1 mark ne kawai ta wuceni fa,atleast ka ce mun sannu da ƙokari after all babu wanda ya wuce ni bayan ita ".

Cike da spark ya Juyo yana mai cewa"shi 1 mark É—in baza ki iya cinsa bane?".

"Daddyn Anisa dan Allah ka kalli Titi kana tuƙine idan munje gida sai ayi maganar nan"Enen ta faɗa ganin ya mayar da hankalinsa kan Anisa ga kuma tuƙi yana yi .

Zumɓura baki kawai Anisa tayi tana mai jin yadda yaya Hibba ke shafa mata hannu a hankali cikin siga ta lallashi.

Koda suka isa gida bai ƙasa a gwiwa ba ya cigaba,ƙin tsayawa tayi a gurin ta wuce ɗakinta dan idan zata tsaya sauraron Daddy at the end of the day faɗa za suyi,ta yaya ma za a yi tabar Zunairah ta cigaba da winning akan ta idan sun je University?the more suna nuna mata Zunairah ta fita the more tana san ta ga ta buge ta a komai,ba dai winning suke so tayi ba,to yanzu suka fara .

Shigowar Enen ya tsayar da ita daga wankan da ta yi niyyar shiga,wata gown ta kawo mata mai kyau,ajewa tayi kan gado kafin ta isa gareta,riƙe mata hannu tayi tana murmushi kafin ta ce"kinyi ƙokari yarinyana,cin na biyu ba abu bane mai sauƙi,".

Wani irin kuka ta fashe dashi tana mai rungume Enen kana ta ce"mene abin wahala idan daddy ya faÉ—a mun haka?Enen I'm trying ,Ina duk abin da zan yi ganin ban Bama Daddy kunya ba why this? kullum a rayuwarsa ban kai inda yake so ba,shin fault É—ina ne idan Zunairah ta ci Marks fiye dani?".

KaÉ—a mata kai Enen ta fara tana mai cewa"you're doing your best kuma kina yi yadda ya kamata kada ki biye ma Daddy and na san yanayi ne saboda ke, Sweetheart duk abin da ki ka ga iyaye sun yi a rayuwar É—an su dan samun cigabansa ne because mu namu ya wuce,kada ki saka maganar Daddy a zuciya,and baki sani ba idan baki nan yana yabon ki".
"To Enen ego ba zai barshi ya faÉ—a a gabana ba ko,I'm sick and tired ".
Lallashinta Enen ta dinga yi har ta samo kanta amma deep down abin yana cikin Zuciyarta,babu ma yadda za a yi Zunairah ta cigaba da wuceta,idan tana da wani tunanin na Chanza makaranta a yanzu ta sake tabbatar da inda Zunairah ta je nanne itama zata je.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)

EPISODE 5:unknown broken code.

*𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷*
Chapter 5 · 0% Book details