← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 28

Sashe 27

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan ya gama dakin ya ɗauki sassanyan ƙamshin room freshener ,cikinsa da ya fara kukan yunwa ya sashi ya fita domin newa kansa abinci, sai da ya tabbata ya saka key dan yanzu ɗakinsa a nan ne kawai zai samu ƙamshin Rahma.

Baje ya tarar da ita a falo tana cin gugguru tana kallo,riƙe ƙugunsa ya yi ya ce"wai ni kam Zainab mene hakan?ki kalli fa falon nan dan Allah.".

"Aw aw kana so kace mun kawai aiki nazo yi sai na fahimta ,to wallahi bari kaji ni ba boyi boyi bace ba zan Shara ba idan ban niyya ba,duk lokacin da naji ina san yi babu mai jina amma yau kuwa ƙazanta day ce shi yasa ko wanka banyi ba,kasa da hastag ƙazanta day,ka Barni na sarara idan na isheka da wari ka rufe hancinka ni da wanka sai dare "
"Aw ashe ma za kiyi ai ni duk tunanina baki É—aya baza kiyi ba,to ina san ki sani É—aki mun raba ki koma naki ba zai iyu ki mayar mun É—aki kamar na yan iska ba,Kinga falon nan haka wallahi ko shi ba zan É—auka ba ki san yadda za kiyi na dai faÉ—a Miki".
Kitchen ya nufa yana ji tana cewa wallahi bai isa ba,shi dai bai kula ta ba ya shiga kai tsaye,window ɗin kitchen ɗin ya gani a buɗe kudaje nata waƙe bisa ƙwanikan da tayi amfani dashi,daga gani ta shiga tsaminsu ya isheta ta buɗe window ɗin,kai wannan mata akwai annakiyar ƙazama.
Fita yayi ya tarar da ita tana tsince falon, tsaki yayi yace idan kin gama Wallahi ki gyara kitchen ɗin chan aikin banza kawai,ta saka karfi da yaji ya koyi tsaki kamar wani tsaka,kullum wannan matar tashi da sabon salon dabi'u take,kamar wasa ta fara ƙazanta gashi yanzu tana san zama mata dabi'a ko ma yace ta zama.
Car key ya ɗauko,ya juya baya ta biyosa kamar zata dakesa,yana juyowa tayi saurin duƙawa kamar zata ɗauki abu,kaɗa kai yayi yace "Allah ya mun tsari da shaiɗancinki Zainab"da haka ya fita yana jin tana ta dariya kamar ta zare,at this point ya fara tunanin ta zare ɗin ba kaɗan ba shine shima take san ya haukace bayan Allah ya fita.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ20:

*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*

Tafiya nake kamar wadda laka ta fashewa a ciki,yau da kasala na tashi , na san idan na zauna a gidan babu abin da zanyi,ina ƙoƙarin tsallaka titin Adaidaita sahu ya tsaya,daɗi kasheni ,da saurina na ƙarasa nace"BUK".

Ganin Adaidaita sahun Khubayb ce sai nayi mamaki, Khubayb?na faɗa da mamaki dan ban taɓa tunanin nan ɗin hanyarsa bace.

"Barka da safiya Hajiya Zunairah muje ko?".

"Idan har ba za ka É—auka passenger ba zan hau ba".

Dariya yayi wadda ta bayyana haƙoran da ban ƙasa a gwiwa ba wajen hango teeth gap ɗinsa "kada ki damu ai aiki na fito Allah zan ɗauki passenger ".Murmishi nayi kafin na hau Adaidaita ina mai fadi mishi ina kwana.

"Kin tashi lafiya ya kwanan Mutanen gidan?".

"Álhamdulilah ".

"Masha Allah"da haka ya tashi Adaidaita sahun muka É—auki hanya,muna tafiyane yake ce mun ,"mai zai hana ki bani number É—inki idan nazo unguwarku da safe sai na É—aukeki mu wuce makarantar,Kinga kin huta kuma nima gashi daga nan nake lodin passangers,in case kinyi Mamaki kince wannan mene ya zai na kawo shi nan da safe ko kuma ki yi gudun zan latti sha kuruminki a nan tsamiyar boka na samu gurin zama kwanan nan".

Ban ce komai ba illa murmishi da nayi na ƙarbi wayarsa na rubuta mishi numberta,godiya ya yi mun ya kira layina number ɗinsa ta shigo nayi saving da Khubayb.

Bai sake mun wata dogowar hirar ba har muka cika Adaidaita sahun da yan makarantarmu ,da na haÉ—u da Anisa haka nan na ganta kamar wata mara lafiya baki É—aya tayi pale da ita kamar wadda bata da jini,cike da damuwa nace da ita"Anisa baki da lafiya ne?".

Cikinta da ta riƙe take nuna mun tana cije baki wanda ba sai an faɗa maka tana cikin ciwo ba,bata da lafiya idan ba abun Anisa ba mene ya kawo ta makaranta?

Kama mata kafaɗa nayi ina mata sannu duk da ban san takamaimai mene ba amma ganin cikin da take nunawa ya saka na barshi a kan cikinta ke ciwo,duk yadda ta so mu gama lecture abin sai ya ci tura,excuse muka ɗauka muka bar hall ɗin ,rasa abin yi nayi musamman ganin ta rike gefen cikinta ta kasa cigaba da tafiya tana kuka,Nima kukan nake dan kaina ya kulle na rasa tunanin mene zanyi, Khubayb ne ya faɗo mun,babu ɓata lokaci na kirasa ,lokaci mara yawa ya ɗaukesa ya zo,tare muka taimaka aka sakata cikin Napep ɗin a wannan point ɗin she's unconscious,pass ya basu a bakin gate kafin muka ɗauki hanya,kuka kawai nake ina kiran sunanta akai akai cike da tsantsan tashin hankali,tunda nake da ita ban taɓa ganinta cikin yanayi irin wannan ba,Yaya Halil na kira na sanar mishi,nan ne yake cewa mu wuce da ita asibitin da suke zuwa na Garkuwa zasu same mu chan,a haka muka ɗauki hanya dan zuwa Asibitin Garkuwa,ban mamakin ganin Yaya Halil a chan ba,kai tsaye aka shiga da ita emergency domin bata taimakon gaggawa.

"Mene ya faru?".yaya Halil ya tambayeni.

"Dama na shigo makaranta naganta wani iri na tambayeta shine take ce mun cikinta,to muna Lectures abun sai yaci tura muka É—auki excuse to muna fitowa kuma shine sai hakan".

Baice komai ba amma damuwace fal ransa,zuwan Enen ce take faÉ—in "Halil kidney É—in ne ko?".

"Wallahi Enen ina gudun abin da muke tsoro shine zai faru,shi yasa nace ayi aikin nan tuntuni ta tsaya gardama ke da Daddy ku ka biyeta".

Ni dai da ba fahimtar inda zancen nasu ya dosa ba addu'ata guda ɗayace Allah ya bata lafiya ya kawo mata wannan al'amarin da sauƙi,bayan wasu lokuta likita ya fito yake mai shaida musu sun samo kanta amma tana bacci,neman yaya Halil ya yi da yana san magana dashi,jin hakan ya saka Enen shiga ɗakin.

Bayan wasu lokuta ni duk lokacin ina waje gudun kada na shiga tunda babu wanda ya mun tayi,Yaya Halil ne ya dosuni,da damuwa na tashi daga zaunen da nake ,da ya ƙaraso gurina ne nake tambayarsa jikin nata shine yake faɗa mun"kidney failure ne,tana fama da ESKD,end stage kidney disease dalilin kidney cancer wanda dole sai an mata transplant,last time na faɗa musu doctors ɗin sunce tana buƙatar wani amma yarinyar nan ta kafe kan a ɗorata a kan maganai".

Rasa abin faÉ—a nayi sai hawaye dake bin kuncina É—aya Bayan É—aya, bakina na karkarwa nace"amma Yaya Halil will she survive it?".

"Abun da muke fata kenan,insha Allahu she will survive it,cikin ni Ko daddy ko Enen I'm sure duk wanda tissue É—insu ya zama compatible zamu bata, she's going to be okay"ya bani amsa kamar bai yadda da kansa ba.

"Zamu iya shiga ciki"ya sake faÉ—a.

"Taje ina munafukan Allah?"

Muryar Zainab Pagal ta Mana sallama, sunan da Hauwa'u ke kiranta dashi kenan,da zafinta ta ƙaraso tana mai cewa"Hala tayi ciki kun zo ku zubar?".

"Ya subhanallah Menene hakan wai Zainab mene yake damunki da a rayuwa baki da aiki sai jawa mutane Bala'i? tukunna ma da kika fito wa ki ka tambaya?".

"Aw sai na tambaya?kai ka É—ako daÉ—ironka kuka zo nan ka tambayeni?'A'a dan haka ka rufe mun baki ba wannan nake san ji ba,uban mene ya kawoku asibiti tare?ai tunda ka taho nake binka a baya ina mamakin abin da kazo yi ashe ga amsata".

Wani irin kaɗa jiki take,ni dai babu abin da nake sai kallon ikon Allah,ace mace kamar yar daba,bata da aiki sai faɗa, Wannan idan aka ce maka tayi shure shure na masifa cikin mamanta ba zaka Musa ba,juyawa nayi na shiga ɗakin da aka mayar da Anisa na barsu su ƙare lafiya,ina ji tana ihun na dawo ko na kasa gane kaina,ban kula ta ba sanin babu amfani biye wadda bata tsoran iyayenta ko kaɗan,da ace tana tsoronsu babu abin da zai saka ta sake kulani,ina ƙoƙarin shiga ɗakin naji an turani cike da faɗa yaya Halil ya ce"wai mane haka Zainab baki ji ko?da ciwon Anisa za muji ko da tijararki?".
Chapter 27 · 0% Book details