← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 28

Sashe 11

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na juya zan shiga gida ya danƙo hannuna ,yin hakan da ya yi yazo mun a bazata,kalle kalle na fara gudun kada wani ya ganni hannu guda kuma ina kiciniyar hannun da ya damƙe da ƙarfi ya ƙi saki,kamar haɗin baki sai ga dannowar Motar Halil,sake kallon hannuna cikin na Adam nayi kafin na mayar da hankalina kan motarsa ina faɗin"ka sake ni dan girman Allah".maimakon ya sakeni ɗin sai ya mayar da dubansa direction ɗin da nake kallo,wata irin dariya ya saka yana cewa "ki ce Romeo ne ya zo well Kinga ya tarar da majnun ya riga da zuwa".

Riƙon da ya mun akwai azaba amma azabar bata dameni ba ,damuwata guda ɗaya kada Yaya Halil ya tadda mu cikin wannan situation ɗin dan ko da wasa ban taɓa faɗa mishi na san Adam ba,duk roƙon da nake ma mitsiyacin nan bai sake ni ba har sai da abin da nake gudu ya faru,tsaye yaya Halil ya yi a kan mu yana kallon ikon Allah yana mai faɗin"mene yake faruwa anan?kai Adam mene hakan ka riƙe mata hannu besides me ka ke yi a nan?"yana maganar ya saka hannunsa ya fincike riƙon da Ya Adam ya yi mun.

Dariya ya Adam ya yi irin mai shaƙar da wanda ake yi wa ya ce"kaji mun wata tambaya da Halil,i mean ka kalli Wannan yarinyar da kyau,ka kalli haɗuwarta fa,Nima ka dubani,ka ganni bakin gidansu ,sai ka tambayeni me nake yi?ni Adamu?,well it's understandable tunda kana tunanin kai kaɗai ake bawa ka ci,to Nima ina ƙwasar abin da ka ke samu ne".

"Innallahi waina illahir rajiun Ya Adam ka ji tsoron Allah "na furta hawaye na bi mun kunci kamar suna jira musamman ganin Ya Halil ya zuba mun ido,dariyar da Adam yake ce ke shigar mun ƙwaƙwalwa kamar zata Haukatani ga kallon da nake ƙarba daga gurin wanda nake so fiye da komai domin da ace kallo na kisa da tuni a wannan gurin na mutu,hannu na ɗaga na zabge algungumin da mari kafin na ce"duk Ku bar ƙofar gidan nan idan babu wanda yake da gadonsa".ina kai karshen maganata na juya na koma gida har ina haɗa hanya,ina jin Ya Adam yana dariya sosai ya wuce motarsa ya bar Yaya Halil A gurin wanda Allah kaɗai ya san abin da ke cikin zuciyarsa domin ni banace ba musamman da irin kallon da yake bani wanda na kasa fassara abin da yake nufi.

Da na shiga gida Mama bata nan su Hauwa'u ne inda na barsu,ina ji tana tambayata abin da ke faruwa nake kuka, banza na mata na shiga cikin ɗakin mu ina bakin ƙoƙarina wajen ganin na shanye kukan amma ina shiga ya ƙwace mun,mene na yiwa Adam a duk faɗin duniyar nan da ya nemi ya ɓata mun Alaƙata da Ya Halil a Wannan gejin da muke kan saɓani?.Tambayar da nake ta yiwa kaina kenan ,I'm sure akwai mata da yawa da zasu bashi kan su waje ba sai ya sha wannan wahalar ba ,mene ya saka ya zaɓi da ya ɓata tawa rayuwar bayan ya san ba zai taɓa samun abin da yake so daga gareni ba,1 minute ya ce yana sona,1 minute ya nemi ya maidani mutuniyar banza gurin mutumin da ke ganin kimata da mutunci na,tunanin hakan kawai ya saka kuka na ya kasa tsayawa baki ɗaya.

Ina jin motsin Mama nayi saurin goge hawayena,tambayata ta fara lafiya? Hauwa'u na bayanta wanda ita taje ta kira Mama ta ce mata wai ina ɗaki ina kuka dana shigo daga waje,kasa magana nayi sai kukan da nake ta yi wanda duk yadda na so na riƙe na kasa,Mama na ƙokarin zama kusa dani Muhammad Ya shigo da gudu ɗakin yana cewa "Mama Brother ɗin nan dake zuwa Gurin Aunty Zunairah ya shigo wai yana san ganin ki".

Kallona Mama tayi nima ita ɗin nake kallo,"me kuma zan mishi?"na faɗa ina ƙokarin tashi ina ƙarawa da "Mama bari naje na sallameshi".mayar dani tayi ta zaunar ta ce"Ni yake san gani ba ke ba,idan kuma gaskiyane baki dashi to wannan is another story,if not ki zauna a nan naje na ganshi, Hauwa'u je shiga dashi falo ina zuwa" .

Kuka na sake fashewa dashi musamman da ban san abin da zai faɗawa Mama ba,bata bi ta kaina ba ta fita a ɗakin tana mai sake jaddada mun kada na kuskura na fito a ɗakin nan idan ba so nake raina ya ɓaci ba.

*******************************************

*𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓*

Tunda ya shawo ƙwana ya ga Zunairah da Adam hankalinsa ya yi mugun tashi Musamman ganin hannunsa riƙe da nata,tambayar da yake ma kansa abin da Adam yake a gidan su Zunairah,dama sun san Juna?sanin sai ya fita zai samu amsa ya saka ya buɗe Motarsa ya fita amma ga mamakinsa sai yaga riƙon da ya yi mata da bawai riƙone da ta yi na'am da shi ba,bai wani tunanin ba ya ƙarasa ya kwace hannunta yana mai tambayar dalilin da ya saka ya riƙe mata hannu da kuma abin da yake a ƙofar gidansu,Amsar da ya bashi ba ƙaramun kaɗa mishi hanji ya yi ba duk da ya yarda da Zunairah ɗari bisa ɗari sannan ya san ƙaryar Adam fiye da tunaninsa dan zai iya cewa babu maƙaryacin da yafi Adam a danginsu,idan ya zula maka ƙarya sai ka fara tunanin baya da ƙwakwalwa ko yana fama da larurar Hauka dan kai mai ji kana sauraro ka san ƙarya yake amma haka zai dage ya yi ta Zillo ta.

Kallon Zunairah yake Bama ya sauraron abin da Adam ke faÉ—a burinsa guda ya gama ya tafi ya gana da ita dan tun maganar da ya faÉ—a mata ya kasa nutsuwa dalilin da ya saka ya biyo baya kenan .

Jin tace su bar ƙofar gidan ta juya da gudu ya saka yaji wani irin nauyi,yana jin dariyar Adam har ya bar ƙofar gidan ,kamar ya tafi amma sai yaji ƙafafunsa sun ƙin amince mai da yin hakan ,baki ɗaya tunaninsa abin da yake bashi ya bita ciki,tsintar kansa ya yi da bin umarnin Ƙafafunsa wajen bin Zunairah cikin gidan,sai da ya shiga tukunna ya farga,Muhammad ne kawai a tsakar gidan wanda yana jin shigowar mutum ya ɗago ya zuba Mishi ido.

Ganin hakan ya saka yace ya yi mashi magana da Mama Wanda shi kansa bai san abin da zai ce mata ba,sai a Wannan lokacin Muhammad Ya gaishe dashi kafin ya tashi ya shiga dan kira mishi Mama

Tunda Hauwa'u ta shiga dashi Falo yake neman abin da zai faɗawa Maman,zuciyarsa ta riga ta faɗa mishi idan har bai shigo ɗin ba Zunairah ta ƙwace mishi har Abada inda shi kuma bai shirya hakan ba,Mama na Sallama ya sauko daga kujerar da yake ya zauna ƙasa,da fara'arta ta shigo ciki tana cewa"Malam Halil ka zauna mana ka sakko ƙasa".

"A'a Mama nan É—in ma ya yi,ina wuni Mama?".

"Lafiya lau Álhamdulilah, ya mutanen gidan?"ta amsa tana mai zama kujerar dake kallonsa .

"Álhamdulilah Mama,dama nace bari na shigo mu gaisa idan da hali kuma na ga Zunairah yadda ta shigo ɗinne na kasa jurewa nace bari na shigo mu yi magana".

Cikin san sanin Abin da Yake faruwa Mama ta ce"fatan dai lafiya?don har yanzu kuka take bana tunanin kuma Good time ne da zaka ganta da kun daidaita ɗin,ku ɗinga haƙuri da juna ita alaƙa irin wannan idan Ubangiji ya haɗa dole ne mu koyi haƙuri,ba zan nace sai naji abin da ke tsakanin ku ba ,amma ku ɗinga haƙuri dan Allah".

Kamar jira yake ya fara Rero mata abin da ke faruwa inda ya sake jaddada mata ko a yanzu ba shine ya ɓatawa Zunairah rai ba dan uwansa ne Adam ,musabbabi ma bai san mene ya haɗasu ba,ƙarawa ya yi da cewa"Mama wallahi ina san Zunairah sosai dan Allah ki bata haƙuri ta saurareni ,kuma ina so iyaye su san da hakan, insecurities ɗin da take dashi a kaina insha Allahu zan ƙoƙari wajen bata tsaro idan shine ya saka bata san yan gidan mu su san muna Soyayya,maybe tana tsoron banbancin Yaren mu,ita Ebira ni Idoma,Mama mazan Yaren mu Muna riƙe mata sannan gidan mu babu ƙabilanci,insha Allahu ba za ku yi kuka dani ba ,itama kuma ba zata yi dana sanin Aurena ba".
Kunyar maganar nasa Mama ke ji sosai duk da ta gamsu da yana san Zunairah tunda har zai cire kunya ya zo gabanta ya furta mata wai yana san Zunairah,bayan ya gama ya tashi ya masu Sallama ya wuce gida zuciyarsa kamar an cire masa wata damuwa duk da bai samu ya ga Zunairah ba.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸËš:9:Cat out of Bag

*𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov.

Ina jin Mama na mishi Sallama tana mai sake jaddada mishi kada ya manta ya sanar da Enen tana gaisheta sosai,yana tafiya ta shigo ɗakina,ina ƙoƙarin tashi ta ce mun "yáàtùû(zauna)ina zaki je?we need to talk.

Zama nayi kamar munafuka ina aikin sinnar da kai,itama kusa dani ta dawo ta zauna tana Nazarina kafin ta ce"Zunairah kina san Halil kuwa?i mean idan ba san shi ki ke ba ya kamata ace kin faÉ—a mishi sai ya daina wahalar da kan sa ya samu mafita,saboda wannan yaron na gani a idanunsa yana san ki ,na kasa gane wane dalili ne zai saka ki ce wai baki so kowa ya sani a gidan su,shin wasa ya zo ku yi ?I'm very sure ba Ten ten ya yazo yace yana so ku yi ba ke dashi ,banga dalilin da zai saka ki ce wai baki so kowa ya san cewa kuna soyayya' ba,dan haka yanzu ina so ki faÉ—a mun menene a zuciyarki dangane da shi,idan baki san shi ne tell me,sai mu san ya ya zamuyi".

Shiru nayi ina mai jin wani irin Nauyi,sai da ta sake maimaita mun tambayar kafin na iya cewa"Mama ina san shi "ina ƙokari wajen sake ƙasa da kaina dan bana so mu haɗa ido,hankali ta mayar kaina sosai kafin ta ce",to let me understand boye boyen na menene?".
Chapter 11 · 0% Book details