Sashe 17
Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A yadda na zabura ko ban bata amsa ba ta san maganar ta dakeni,wani irin kuka na sake fashewa dashi ina cewa"shikenan abin da wasu zasuna faɗa kenan,amma Anisa ke kin fi kowa sanin halina,duk zafin soyayyar da nake ma namiji ba zan taɓa iya bashi jikina ba mene ya saka wannan zai ɗarsu a zuciyarki?haka ake faɗa a gidanku ko? wallahi babu abin da muka taɓayi ko taɓa hannuna ban taɓa bari ya yi ba ki tambayesa Indai akwai saura imani a zuciyarsa ba zai mun sharri ba".
Ganin yadda na ruɗe lokaci guda ya saka ta rungumeni tana kuka tana bani haƙuri tana cewa ta yarda dani ta tambayane kawai saboda tsoron abin da zai je ya dawo.
Cornflakes ta ɗauko a kitchen ta haɗa mun , kaɗan nasha,shima sai da tayi ta mun magiya sannan,maganin da ta ɓalla mun nasha,tanata lallashina kamar karamar yarinya,Anisa na sona,Nima ina santa bazan bari abin da Yaya Halil ya yi mun ya ɓata tsakanina da ita ba,na saka hakan a raina,ga wani irin girmanta dana ƙara gani,ban tsammanin zata iya barin bikin yayanta tazo kula dani ba har ta goya mun baya.
"Mene ki ke ta kallona?I hope ba tunanin Yaya kike ba?"ta tambaya tana mai nufar mudubinmu ta É—auko kibiya da mataji a gurin da muke ajewa.
"Kawai ina jin daɗi da Allah ya bani ke matsayin ƙawa,ina jin daɗin yadda ki ke nuna damuwarki kaina, Nagode Allah ya bar mu tare ya tsarkake alaƙarmu"na faɗa ina murmushi,tunda aka fara abun nan sai zuwanta na samu nutsuwar dana samu na amayar da abin da yake raina.
Murmishi tayi ta fara mun tsifa tana cewa "kada ki manta kafin Yaya Halil ya zama ɗan uwana Namiji aka fara haifarsa,dan haka zan zaɓeki a kowanne irin situation domin kafin na zama ƴar uwarsa mace aka fara haihuwata,Kinga kuwa babu yadda za'ayi kina mace ina mace na zaɓi ɗan uwana Namiji daya cutar dake dan kawai yana ɗan uwana,ba'ayin rayuwa a haka ko nace bana rayuwata haka because akwai masu zaɓan ɗan uwansu,amma ni i choose you,so chill kiyi kukanki yadda ki ke so kina da kafaɗar ɗora kai,I'm sorry lokacin Ma'aruf we were just minors ban iya baki kulawar da ya kamata ace na baki ba,but in tambayeki mana,da Yaya Halil da Ma'aruf wane yafi baki one blow seven die?".
Dariya na saka wadda na ɗauka ba zan ƙara ba,Anisa kenan a duk halin da ake sai ta samo abin da zatayi da zai sakani dariya.
Ban bata amsa ba itama ta tayani dariyar tana dawo da lokacin da nayi ta kuka Ma'aruf É—in da zan Aura ya yaudareni,har cewa mukayi lokacin zamuje gidansu dan hauka,Anisa kuma na faÉ—in sai ta saka yan zaman banza sun karya mata shi ta basu kuÉ—i ,a wannan zagayen koda zuwan da tayi ta zauna da ni kawai ta barni dashi na gode mata it means alot to me .
Tana ƙarasa tsefe mun kitson karshen cikin huɗun dake kaina wayarta ya hau ruri,tana ɗagawa Muryar Yaya Hibba ya bayyana tana cewa"Anisa an ɗaura Auren gashi tun ɗazu Yaya Halil na nemanki ".
"Nayi Mishi mene?kice nace Allah ya sanya Alheri ni nayi nisa"amsar da ta basu kenan ta kashe wayar tana mai cigaba da mitar da ban taya ba,shiru kawai nayi amma a Zuciyata tunanine kala kala,na kasa yarda wai Yaya Halil ya yi Aure da wata ba dani ba,Yaya Halil dai danake kira ,Baby Habibi,Ina san Sanin mene nayi mishi ya yi mun wannan É—anyan hukuncin mai firgici,sanin koda na tambayi Anisa ba sani tayi ba ya saka ban tada zancen ba nayi shiru ina auna yadda zanyi dakon wannan cin amanar da ya ziyarceni.
Haka muka wuni tare ba ita ta tafi ba sai da Mama suka dawo da Magrib,shima sai da Mama tayi da gaske dan a cewar ta kwana za tayi dani,da ace zata kwana ɗin dana so duk da nasan buƙatata zatayi yawa,bai kamata na kasance mai san kaina ba,tun fari ma bai kamata ace tazo ta bar bikin gidansu ba tunda dai kafin na zama ƙawarta Yaya Halil ne ya fara zama ɗanuwanta dole kuma ya zamo gaba dani.
Da dare kowa ya zauna cin abinci nima na fito daga ɗaki,babu wanda ya yi mun wata tambaya ,zama nayi gefen Hauwa'u dake aiki washe baki,Shinkafe ce da miyar Alayyahu Mama tayi mana,tare dukka muka haɗu a babban tray ɗin da muka saba cin abinci,Mama na saka Mana Nama Hauwa'u tayi saurin ɗaukar nata ta ƙara a nawa Muhammad ma ganin abin da tayi ya saka shima ya ɗora nasa a kan nawa,murmishi nayi nace"to idan na cinye namanku sai kuci mene ?".
"Dukkan satin da ya wuce mu muke cinye naki ,yau ki ci namu"Adavize ya faɗa,kafin na sake magana Baba da Mama sun basu nasu ,murmishi nayi ina mai danne hawayen dake san ƙwace mun kafin na ɗauki naman na ci,kafun na ƙwanta Anisa ta kirani tana mai sake tambayata anya ba sai tazo ba domin ta kasa cire tunanina da halin da nake ciki.
Dariya kawai nayi ina mai cewa"I'm not suicidal Besty,ba zan kashe kaina ba ,na yarda da ƙaddarar da ke tare dani a yanzu ". hira ta ɗanyi mun wadda ta sakani nishaɗi dan labaran da ta bani sun sani dariya,yan gidanmu ma sun shaida dan saida Mama ta shigo taga da ita nake waya,ikon Allah kenan Yayan ya dasan ciwo ƙanwar ta zamar mun Magani
ð—–ð—œð—¡ ð——ð—¨ð—¡ð——ð—¨ð—¡ð—œð—¬ð—”
ð™²ðšŠðšžðšðš’ðš˜ðš—ðšŠðš›ðš¢ ðšðšŠðš•ðšŽ
Na
ð—”ð— ð—œð—¡ð—” ð—ð—”ð— ð—œð—Ÿ ð—”ð——ð—”ð— (chuchujay
EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ 13: newlyweds
*ð˜ð˜ˆð˜“ð˜ð˜“*
Shi É—aya zaune ya nutsu yana kallon zoben Zunairah kamar yana karatun wani abu a jiki, jin an fizge ya saka shi É—agowa yana kallon wadda ta raina shi cikin gidan da ita kaÉ—ai zata iya fizge wannan zoben.
Washe baki tayi ganin Z a cikin zoben ,cike da zumuÉ—i ta zura a hannunta tana ma cewa"Tuntuni Halil ka bani zoben na mene ka ke jira?".
Daga zaunen da yake ya taso ya kama hannunta da ƙarfin tsiya ya cire yace"ai kinfi kowa sanin ba naki bane,bana san irin abin da ki ke mun Zainab".
"Aw ashe baza ka cire wannan shegiyar yarinyar a zuciyarka ba ko Halil?,to wallahi ko ni ko kai a gidan nan,dan Ubanka idan kana ganin za kayi Auren Zaɓi biyu dani kayi tunanin zaka ƙuntata mun bayan nan wallahi sai dai mu ƙuntatawa juna"
Juyowa ya yi ya daskare a gurin yana kallonta"dan Ubana?"ya maimaita cike da mamaki,juyawa tayi ta bar gurin tana gunguni,saboda tsabagen Mamakin da ta shayar dashi bai iya yin komai ba illa bin ta da ya yi da ido har ta shige ɗaki,wai dan Ubansa,kalmar nan ta samu gurin ta toƙare mishi wuya,shin mene ya jefa kan sa shi kam?
Tunda yau Auri Zainab yau sati biyu kenan ya kasa gane gabanta balle bayanta,zai iya cewa sun yi zaman ƙwana goma lafiya although suma ƙwanakin tana ta aikin yaɓa masa magana dan kawai lokacin da suke tarawa ta Auratayya a daren farko su ya kirata da Zunairah,babu irin lallashin da bai mata ba sanin shine baya da gaskiya kuma ya ɗauka amma ta ɗauki abin ta riƙe a zuciya take ta tafka rashin mutuncinta yadda take so,koda yan uwansa na ƙyauye suka zo halin ko in kula tayi dasu amma basu ɗauki abin komai ba a cewarsu baƙunta ne amma shikam sarai ya san iskanci ne.
Yayi soyayya da Zainab sosai kuma ya sota abin da ya raba su shine kule kulen samari da kuma rashin iya magana,da fari ya zata zata bari amma ganin abun gaba gaba yake ya saka suka samu nesantuwa da juna,ranar da ya rabu da ita baki É—aya shine ranar da yaje zance gurinta wani Alhaji yazo tace dashi wai ya jirata,kamar a mafarki ta nufa gurin Alhajin ta shiga motarsa yana tsaye yana mamaki.
Cikin son ya ga ƙarshen ƙarya ya jirata,sai da tayi wajen awa guda yana wajen yana jira kafin Alhajin ya tafi Sannan ta dawo gurinsa ,"kayi haƙuri kawuna ne"shine abun da kawai ta ce mishi ta cigaba da juya rafa na kuɗi daya bata,
"To"yace mata ya shiga motarsa ya tafi bai kuma waiwayenta ba itama kuma bata damu ba sanin soyayyar ta da Halil kamar Tururuwa da gida ne duk inda taje zata dawo ta shiga ta ƙwana,ta sani zai dawo dan dama haka faɗansu yake ,zai daɗe kamar ba zai dawo ba daga bisani kuma sai ya dawo ɗin.
A wannan zagayen ganin ya daɗe bai dawo ba ya saka ta fara bibiyarsa ,nan take tsintar soayyarsa da Zunairah,ta damu dan har ta fara yanke tsammani,kwatsam sai ga kiransa wai zai zo gidan su,bata wani ja mishi Aji ba musamman a lokacin da take neman miji gashi kowa da take kulawa babu na Aure babu ma wanda zata kira tace ya zo su yi Aure ya amince,Zainab yarinya ce da ake kira da Yar malam taƙi halin Malam,Ƙaddarar za suyi Aure ya haɗasu a wurin dinner na abokinsa.
Bai wani ja mata rai ba ya kawo maganar Aure inda babu ɓata lokaci tayi na'am da hakan,basu wani yi bincike mai kyau ba,binciken da sukayi ɗaya ya nuna musu Babanta Malamine ,kuma Malami a irin Matsayinsu dan shine babban Malamin Sanata Hadi madugu,babban Sanata a wannan yankin,sannan yana harka da manya yan siyasa,baya da wani abu da zai ɓatashi,hasalima yana cikin mutane mafi kima a unguwar ,a nasu tunanin indai ƴa tashice ai kamar an tsinci dami a akala ne.
Duk da shi ya kawo maganar Zainab amma dai Daddy ya fishi zumuɗi Ganin haka ya saka ya basu wuƙa da nama,Yana san Zunairah ba zai ƙaryata ba,yana mutuƙar santa fiye da yadda bai taɓa tunanin yana yi ba amma abin da Anisa ta nuna mishi ya danne dukkan wannan son ya rufe mishi idanu,babban abin da ya fi komai ɓata mishi rai shine yadda take kallonsa take mishi karyar ita ta Allah ce,ya riga ya saka ma ranshi ta yaudaresa tayi mishi ƙarya dalilin da ya saka ya yanke hukuncin da a yanzu yake ganin bai bi a hankali ba,ace Amaryar sati biyu har ta fara kallon Ango ta zagi ubansa?