← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 28

Sashe 14

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa tayi tana kallona tayi murmushi kafin ta ce"well I'm all ears ,mene decision É—inki?".

Ɗan shiru nayi kamar ba zan magana ba,zura mun ido tayi,cikin dan dakewa nace"Anisa look here babu inda addini ya haramta alaƙata da Yaya Halil,ni dake kamar yan uwa ne,kada ki bari wani code na Bature ya yi mun katangar ƙarfe da farin cikina,Wallahi a tare da Yaya Halil nake ganin Rayuwata nan gaba ,ina san sa ina san kasancewa dashi,bayan relationship ɗina na baya da Ma'aruf ke shaida ce yadda nayi ta fama,idan na rabu da Yaya Halil zan faɗa cikin hali mafi munin na baya ,ba zan zaɓa tsakanin Ƙawance ko Soyayyata ba,duka nake so koda za'a Kirani mai san zuciya,ki yi haƙuri".

Wani irin kallo take bina dashi ranta a mutuƙar ɓace,cikin yanayi na ɓacin rai tace"haka ki ka zaɓa Zunairah?".

"Im sorry"shine Abin da na furta ina mai jin babu yadda za'ayi ta sake mun tunanina ,zan iya bar mata komai nawa amma ba zan bari na cutar da kaina ta yadda zan illata kaina da kaina ba,bayan na gama sakankancewa da tayi fushi ta kwashe da wata irin dariya,sosai take dariyar kamar wadda ta zare inda ni kuma nake kallonta fuskata babu yabo babu fallasa,matsowa tayi kusa dani ta dafa kafaɗata kafin tace"saki ranki mana mene hakan?God Kinga yadda ki ka zama serious kamar wadda tayi wani babban laifi?well kin cinye jarabawar da nake san miki dama ina son gwadawa ne naga kin chanchan,Yayana,and kamar yadda nake expecting kin cinye, welcome to the house,ki saurareni da kyau,ni da ki ka gani well wisher ɗinki ce ,duk abin da ki ke so idan ban nema Miki ba ba zan ƙwace Miki ba, ballantana ma sai inda karfina ya ƙare wajen nema Miki farin ciki,ke nifa ko Khalifa ki ka ce kina so ni mai bar mikice".

Dariya na saka jin wai zata bar mun Khalifa ,as if"kece zaki bar mun Khalifa,da anyi ruwa da ƙanƙara,balle ma ba zan taɓa having interest kan Khalifa ba,shi naki ne nima kuma ina da mai bani Zazu".

"Sai dai abin da ya fi Zazu,ni dai ga yayana na baki amana kada ki ci amanarsa domin duk abin da Yaya Halil ke so nima ina so ina kuma taimaka mishi wajen ganin nima na so wannan abin fiye da tunanin mai tunani,yanzu dai muje kada mu makara".

Tsaye nayi bakin wata dallekiyar Mercedes ina mai jin Zuciyata bata bani goyan baya ba da na shiga ba,buɗe murfin baya Anisa tayi ta tura nii tana mai cewa ,nace miki za muyi latti,Khalifa dake zaune kujerar mai tuƙine ya mun murmushi yana mai cewa"Barka ƙawarmu,ina wuni?".

"Ina wuni ya gida,ya Aiki?"

"Álhamdulilah mun gode Allah".

Da wata irin siga ta shagwaɓa Anisa ta ɗora kanta bisa kafaɗarsa tana mai kamo hannunsa kana ta ce"i miss you Chocolate ",wani irin kunya abun ya bani musamman ganin yadda Khalifa ke ƙoƙarin ɗagata daga jikinsa idanunsa kuma na gareni ta mirror,saurin ɗauke ido nayi ina kallon gefe lokacin da idanunmu ya sarƙe a na juna,ji nake kamar na buɗe na fita dan ban san wane iskanci ke damun Anisa ba kuma.

Juyowa tayi ta kalleni tana mai yin murmushi kafin ta ce"da ace baki dating da na shaƙa miki,sai Allah ya saka kin fita sahun yan nema, Chocolaty ka san Zunairah da Yaya Halil soyayya suke,kasan har tazo gidanmu ya mayar da ita gida bata faɗa mun ba ashe ni suka maida bi ta chan suna pretending,Besty kin iya munafurci, tsakaniki da Allah lokacin baku tare?kada ki ji kunyar Baby"..

Yaƙe kawai nake na kasa cewa komai,kana kallo ka san a takure nake musamman jin maganar da ta ɗakko gaban Khalifa,shine ya katse ta hanyar cewa"Ayya Allah ya sanya Alheri,ki ce muna da biki nan kusa".ƙwace hannunsa ya yi da ya kai ƙarshen maganar cikin sigar dabara amma da yake ƙawata ta iya zubar da mu ta sake kamowa tana cewa"Who knows a fara yin namu,cos nan da wasu watanni ina jiyo ƙamshin Aure".

"Allah ya amsa Mana ,bari muje kada mu tsayar da Zunairah ko?"ya faɗa yana mai yi ma motar key,ni dai da ban san ina zamuje ba nawa ido,a Zuciyata kuwa ina ta saƙa da warwara,dan dole na yima Anisa maganar yadda take ta taɓa Khalifa wanda ba sai ya faɗa maka baya na'am da hakan ba , gidan babbar yayarsa muka je ,shima nan Anisa tayi ta zaƙewa,ban sani ba ko abin da take ne zai saka su san ta waye ko mene oho,amma nifa a nawa belief ɗin ba dai dai bane, zaƙewa ba shine zai saka a san kai ɗin a waye ka ke ba.

Koda muka tashi tafiya leda biyu ta mana tana ta mana godiya,har Kofar gida suka kaini,ina ƙoƙarin shiga gida ta fito da ledar hannunta tana cewa"wannan ɗin wa ki ka barwa?"

"Anisa mai yasa baki faÉ—a mun inda zamuje ba,ina kuma da magana dake".

Jiki na rawa ta saka mun ledar a hannuna tana cewa"naji muyi magana gobe ,kiyi haƙuri,yanzu Khalifa na jira ki gaida mun da su Mama ".

Bata jira abin da zan sake faɗa ba ta koma motar tana mai ɗaga mun hannu,haka nayi tsaye har suka wuce kafin na shiga gida,ban tarar da kowa ba sanin Mama na islamiyyar da har yanzu aka ƙi gamawa,sau tari nakan tambayeta yaushe zata yi sauka sai dai ta ce mun mene amfaninta ,kullum yi ake,karatun matan Aure kenan haka mukan tsokaneta,ledar na buɗe naga doguwar riga mai kamfala da gyale a ciki,ajewa nayi ina mai niyar bawa Hauwa'u ba dan Alheri bane dama ni ba zan karɓa ba.

Sallar Azabar da aka fara kira nayi kafin na dumduma Egusi dake fridge na dauko Saƙwara dan ban yadda na ci abinci gidan Auntyn Khalifa ba duk yadda tayi ta nacin mu ci ɗin,sai da na samu natsuwa na koma na ƙwanta sai kuma damuwar ƙin naimana da baiyyi ba ,na saba kullum shine ke fara kirana a waya,yau da bai Kirani ba sai na ɗauki hakan da ƙilan yana wani abune sai kuma ga Anisa ta ɗauke mun dukkan lokacina.

Kiran wayarsa nayi a karo na uku bai ɗauka ba, tunanin baya yanayi na ɗaukar wayar ya saka na tura masa saƙon idan ya gama ya ya Kirani ina kewar jin muryarsa,bai mayar mun da saƙon ba kamar yadda nayi tsammanin zai maido, idan har nayi masa dropping message baya ɗaukar lokaci zai dawo mun dashi ya faɗa mun ko yana aiki ko yana wani abun amma zai kirani,haka dai ban ɗauki abin wani abu ba na ƙwanta ko zan ɗan samu bacci bashin na asuba da ban yi ba.

Wajen yamma Mama ta dawo take faɗa mun ta tsaya meeting ne nasu na yan ajinsu tunda dama duk inda ƙarfe biyu yake ta dawo gida, kaya da Auntyn Khalifa ta bamu na nuna mata nake shaida mata munje tayi haƙuri ban faɗa mata ba,ko da nace Hauwa'u ta ɗauka mama tace ba zai iyu ba ai babu daɗi a maka ƙyauta ka ƙi sakawa,koda ita bata gani ba ai ita Anisa zata gani taji daɗi.

Naso na dai Bawa Hauwa'u na san kuma zata ji daÉ—i amma abin da Mama tace shima gaskiya ne,na mata ko sawa biyu ne na Bawa Hauwa'un.
Har daren ranar Yaya Halil bai nemini ba,abun da ya bani mamaki shine da na hau WhatsApp na ganshi online, message nayi mashi bai reply ba ,sai abin ya fara damuna a wannan stage É—in na san dole akwai wani abun,to amma menene shi?
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸ11.Fire breakout

*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*

Tunani yana neman ya saka na zauce ,yau Friday ranar da nasan dama dole zai zo gurina da dare,duk da haka da wuri na shirya dan zuwa makaranta duk da period ɗaya garemu Report writing,ko abincin kirki ban ci ba,burina na samu Anisa na tambayata lafiyarsa,Sai da nayi awa ɗaya a makaranta kafin ta zo, straight gurina ta nufa ta zauna duba da class ɗin sai Sha biyu muke dashi ya saka da yawan ɗalibai da dama basu kai ga ƙarasowa ba.

Cikin damuwa na ce"Anisa Yaya Halil fa lafiya ƙalau yake?".

Cire jakarta tayi daga kafaɗarta tana mai ɗan zaro idon alamun tambaya tana cewa"Well last dana tuna ƙalau yake dan shine ya ajeni makaranta yanzu ya wuce and ai kya bari mu fara gaisawa atleast sai ki tambaya ,Anisa ya darenki ?ya ki ka kwana ya kuka rabu da masoyinki?but its okay yanzu bari na fara kiran Yaya Halil".

Kamar Nace kada ta kira amma sai na rabu da ita ɗin dan ƙasan Zuciyata ina san naji mene ne faruwa,muryarsa da nake kewace ta shiga cikin kunnuwana.

"Yayana kana ina ne?".

"Kamar ya ina ina?ke dai ba na aje ki makaranta ba,gida nake san na koma nayi bacci tunda kin katse mun". ya faɗa daga ɗayan bangaren da Alama yana tuƙine.

Matso da wayar tayi kusa dani ta sake cewa"well hala baka Kira Zunairah ba".

"WHO IS SHE? wacece wata Zunairah,dan Allah kada ki dameni kafin ki ɓata mun rai na ɓata miki"yana faɗin hakan ya kashe wayarsa,i was shocked,hawaye naji suna neman cika mun ido,saurin gogewa nayi ganin yadda Anisa ta zuba mun ido,ɗan murmushi nayi nace "well lets talk about you".

Cike da kula ta ce"mene ya faru tsakanin ku?wani abu ki ka mishi?no nama tabbata babu abin da zaki mishi wulaƙancine kawai irin na ɗa namiji,Allah bari naje gida na sameshi,lokacin da yake zuwa yana kalamiyeki da zancen ƙauna ai bai tambayi wace ke ba,lokacin kuma da zai je ya siya miki Zobe mai tsada duk bai san da wannan wacece ɗin ba,zan koma wallahi dole ya jini ko na jisa,wane irin abu ne wannan".
Chapter 14 · 0% Book details