← Book details Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 28

Sashe 10

Cin Dunduniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu na saka na rufe ido ina dariya inda shima ya sa dariya kafin ya zaga ya shiga motar,haka ya dinga tsokanata ina biye sa ,koda muka isa makaranta na so ya ajeni bakin Gate gudun haɗuwa da Anisa amma ya ƙi,haka nan ƙirjina na dukan huɗu huɗu ya shiga da ni,sai da ya je bakin department ɗin mu kafin ya yi parking, kallona ya yi ganin yadda nayi tsuru tsuru yar dariya ya yi kafin ya ce"why are you behaving kamar ni da ke muna aikata abu mara kyau?na kasa yarda kina wannan abun ne saboda Anisa,for God sake ƙanwata ce bata da hurumin zaɓar wadda zanyi soyayya da ,ina sanki babu abin da Anisa ta isa ta yi dangane da hakan,besides za taji daɗine ace yau matar da ƴaƴanta zai Aura ƙawartace sun saba ba sai sun fara sabon shaƙuwa ba, at this point na fara tunanin ba Anisa ki ke ɓoyewa ba,maybe baki san na ɗauki step forward saboda kina tare da wani".

Saurin juyowa nayi ina kallonsa dan ban taɓa tunanin zai zargi ina tare da wani ba bayan shi,"so all this while zargin da ka ke mun kenan?".

"No Baby ba haka bane kawai na fara feeling insecure ne"hannu na ɗaga mishi kafin na ce"yaisa Nagode "buɗe motar nayi na fita ,yana ƙokarin buɗewa ya fito domin biyoni Anisa ta bayyana a gurin,ganina ya saka da Mamaki ta sake kallon motar,kafin ta ce wani abu ya yi ma motar key ya bar gurin,bin motar tayi da ido kafin ta dawo da kallonta gareni ta ce"wannan ba motar Yaya Halil bane?naga kuma kin fito a ciki yana ganina kuma ya juya kamar bai sanni ba ya wuce".

"Mun haɗu a hanya ne ina tahowa shine ya rage mun hanya,amma tafiya da ya yi kam kilan bai kula da ke ba"na bata amsa ina mai kamo hannunta da zummar mu tafi,ƙwacewa ta yi ta ce"he saw me now,sai da na roƙeshi akan ya kawoni makaranta yau driver na baya nan ni kuma bana da license tukunna ya ƙi,yanzu kuma sai na ganku tare?".

Ganin irin kallon da take munne ya saka nayi dariya ina mai gudun kada ta gano ni kafin na ce "babe calm down yanzu taho dani da ya yi ma ai kamar ya yi miki alfarma ne ,na ce miki a hanya na ganshi ya rage mun hanya".

"Wacce hanyar,tunda dai na san daga gida abun hawa zaki hau ta ya akayi ya ganki a hanya ya É—auko ki bayan ba guri É—aya muke ba, ku haÉ—u a hanya kuma abu guda ne,either kin san zai zo ko kuma kun yi communicating"ta sake firing tana zuba mun ido.

Kafin ma bata Amsa mutumin da na tsana fiye da kowa a dangin Anisa ya cece ni,kiran sunanta yake amma yana gani na ya washe baki yana dawowa inda nake yana na faÉ—in"baby!!".

Yaƙe nayi ina mai cewa"ina kwana ya Adam "kafin na matsar da jikina daga inda yake .lasar leɓe yake yana kallona yana faɗin "Masha Allah, watanni kawai kin sake kyau Zunairah ,nayi missing abubuwa da dama gaskiya ".

Sosai Anisa ta haÉ—e rai ta kamo hannuna tana mai cewa "bana so Ya Adam mun yi maganar nan da kai ba sau É—aya ba, ba biyu"da haka ta ja hannuna muka nufa inda na fi tunanin nan ne class É—in mu,ban mamakin yadda ta samu seat É—in gaba ba,Anisa ake faÉ—a muku,a lokacin da nayi tunanin ta bar maganar Yaya Halil a gibar ta kamo maganar munje Sallah inda take cewa "Zunairah kina san Yaya Halil?".

Sarƙewa nayi da yawon bakina dan ban taɓa tunanin zata mun wannan tambayar ba,tambayar ta nayi da wane irin tambayane wannan?.

Ƴar dariya ta saka tana mai san kawar da tambayar kafin ta ce"I'm sorry abun da na san zai wahala ya faru after all na san cewa Yaya Halil ba irin mazan da ki ke so bane ,how dumb of me".

Nima dariyar nayi yadda tayi amma deep down fargaba ta ziyarceni,cikin rashin Sanin nauyin furucina na ce"idan nace ina san shi fa?".

Kamar an ɗauke mata wuta haka komai nata ya tsaya inda na kasa karantar yanayin da furucin nawa ya jefa ta ,dariya na saka kamar wata taɓaɓɓiya ina mai mata dukan wasa ina cewa "babe im kidding ji yadda ki ka saka serious face,kin manta ina da boyfriend"ƙarasa maganar nayi ina mai nuna mata zoben dake hannuna,sai a Wannan lokacinne ta saki jikinta ta ce"well har na so na manta hakan,but mind you duk lokacin da ki ka fara san Yaya Halil ki ka ji kina san dumping waccan boyayyen gayen akan sa,na zama ta farko da zan sani domin nice kaɗai zan iya baki taimakon da ki ke buƙata,dan nafi kowa sanin wanene yaya Halil,duk da macen da yake so baki cikin tsarinta amma zan ƙoƙari nayi 1 or 2 a san ya za a yi".

Sosai maganar ta yi mun nauyi a ƙirji,sai naji raina ya ɓacci da Yaya Halil, maganar na fara haɗawa guri ɗaya da wadda ya yi mun,ko so yake ya rabu dani dan ya gano ban kai yadda yake so mace ta kai ba?to mene ma yake so ɗin?ban sani ba wadda zan tambaya kuma a yanzu dai a moment ɗin da muke ciki last wadda zan tambaya ita ce.

Kada kuga laifina ina so idan ina soyayya ko ina na cike gurbi gurin wanda nake so,yaya Halil yana nuna mun soyayya sosai,amma fitar maganar nan bakin Anisa sai sheɗan yake ƙara zugani kan maganar da ya faɗa mun ɗazu na kai karshen batun a kan yana san rabuwa dani ne dan ya samu wadda ta fini,baki ɗaya na kasa yarda maganar san kowa ya san muna tare ta kawo faɗan,ya san bana so a sani shine yake amfani da hakan dan nayi fushi nace a rabu.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchu jay)

EËŸËšPËŸËšIËŸËšSËŸËšOËŸËšDËŸËšEËŸËš:8.:first fight

*𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov.

Baki ɗaya na kasa cire Maganar Anisa a raina,har na koma gida abun na damuna musamman da ya ƙi kirana,na duba wayata ya fi sau adadi ko zai kira ni,lokacin da Baba ya kira na haɗa shi da Mama baya samun wayarta jikina na ɓari na ɗauki wayar tunanina shine, atleast ina san na saurari haƙurin da zai bani dangane da ƙazafin da ya yi mun na ina tare da wani daga nan sai na kawo wancan maganar,amma har magrib bai kirani ba,haka na cire rai ina mai jin Zuciyata na mun wani irin zafi,na tambayi kaina ya fi a irga mene yake damuna ?.

Bayan sallar magrib ina yi ma Adavize tilawar hadda wani yaro ya shigo wai ana sallama da ni,wata irin faɗuwar gaba naji ta ziyarceni,cigaba nayi ban tsaya ba inda Mama ta ce yaje yace ina zuwa,har yaron ya fita ban dakata ba,ganin haka ya sa mama ta ce"Hafiza sai ki sauke karatun nan haka Ometere ta cigaba mishi,kinji ai ana Sallama da ke a waje na san kuma kina san zuwa ɗin". kunya ce ta kamani sosai, tashi nayi na shiga ɗaki,ina jin Hauwa'u ta karɓi karatun sai dai tun kafin aje ko ina sun fara faɗa.

Sallama nayi ma Mama kan zan fita tace na kula,na san fitar nan ko mu shirya ko mu sake wani faÉ—an,abun mamaki wannan shine faÉ—an mu na farko tunda muka fara soyayya.

Yana cikin mota bai fito ba ga motar duk tint Sannan ban san shi da ita ba,chogewa nayi na tsaya,horn ya yi amma na yi mishi banza,ai ya san bana zance a mota ba kuma zan fara a motar da take duk duhu ba gefe da gefe ,gaba da baya ganin bana da alamun takawa ya saka shi buÉ—e motar zai fito,ganin hakan ya saka na haÉ—e rai sosai ina mai kashe inda zai fito da ido.

Saurin ja da baya nayi ganin wanda ya fito daga motar yana kaɗa key ɗin sa ,idona na sauka cikin nasa ya kashe mun ido guda ɗaya,ya akayi wannan ɗan iska ya san gidan mu?. tambayar na mayar masa zuwa fili "Ya Adam mene kake a ƙofar gidan mu?"

Yar dariya ya yi yana mai takowa yana cewa"mai san tsuntsu ai shi yake bin sa ya jifeshi".

"Kada ka sake kirana tsuntsu"na faÉ—a cikin rashin zato da tsammani,dariya ya saka sosai jin abun da nace kafin ya ce "kin yadda ina sanki kenan tunda har kin amince ke tsuntsu ce,to forget about that,rashin iya Hausanki bai dameni ba,a haka nake san ki nake san kasancewa da ke matsayin matata,akan abin da ya faru tsakanin mu yanzu nake san gyarawa,dan Allah Zunairah ki kalleni ki manta da wani Halil bai dace dake ba".

Wani irin faɗuwa gaba ce ta kawo mun ziyara,ganin reaction ɗin da nayi da ido ya saka shi kecewa da wata shaƙiyyiyar dariya yana mai ɗaga mun gira ya ce"You heard me,kina tunanin ban san kina Soyayya da Halil ba?I'm not his little Naive sister Anisa ,Adam nake duk yadda ki ke tunani kuma na wuce Nan,ina da kaifin basira,a kallo ɗaya ba sai an faɗa mun soyayya ku ke ba ,ballanta kuma na ji daga bakin da soyayya ake yi da shi',Halil ya faɗa mun so which koda bai faɗa mun ba na san ke dashi kuna soyayya'".

Wani irin duka ƙirjina yake ,haɗe rai nayi sosai kafin na ce"to sai mene idan ka san muna soyayya ni da shi?,after all soyayya kace Muna yi ba iskanci ba,and Ina so ka sani ta ko ina ya fika tunda shi ɗin ba ɗan iska bane kamar ka mai neman duk hanyar da zai bi ganin ya keta haddin mace,kaga information ɗin nan da kake da shi idan kaga dama ka kaishi duk inda ya yi maka bai dameni ba, abu guda ɗaya nake san ka sani,kada ka kuskura ko da wasa ka sake taƙo ƙafar ka ƙofar gidan nan da sunan ka zo gurina,ina roƙonka kafin na sigar da police report kan harassment ".
Chapter 10 · 0% Book details