← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 27

Sashe 9

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

B'angaren Safna kuwa ' a zaune take a wajen zaman su babu abinda takeyi inba kuka ba, Muneeba ce tsaye a kanta tana tambayar abunda ya faru.
"Wai don Allah meye ne? Nifa na fara gajiya da wannan koke koken naki, Don karki samun ciwon kai."
"Don Allah Muneeba ki kyaleni! Ki barni inji da d'aya mana ' ku baku tab'a damuwa da damuwar wasu sai dai taku kuka sani, Na rok'eki ki barni inji da wulak'ancin da mutumin nan kemin."
Tab'e baki Muneeba tayi, Ta koma taja kujera ta zauna ta cigaba da danna wayarta.
Safna sai da tasha kuka har kanta ya fara ciwo, Tukunna tayi shuru ta fawwalama Allah komai.
Saida ta dad'e a zaune, Sannan ta tashi ta nufi toilet d'in mata ta wanke fuskarta, Tukunna ta fito ta wuce office d'in Sir-Kamal kai tsaye.
Tana isa wajen ta bud'e k'ofar ba tare data jira anbata izni ba, Sakamakon ciwon kanda take fama dashi.
Safna kai tsaye ta shige ciki ta samu waje ta zauna a gajiye, Sannan tace.
"Sir, Na dawo."
Sir-Kamal lura yayi da yadda idonta ya kunbura ' yasan cewa babu makawa Safna kuka tayi.
"Safna Akwai abunda ke damunki ne?."
Ta girgiza mai kai, Alaman a'a.
"No you better tell the truth!, Because daga ganin idonki kinyi kuka."
"Sir-, Koma menene ya riga ya wuce ' maimaita maganar batada wani amfani."
Girgiza kai kawai yayi ' sannan ya mik'e tsaye yaje d'auko wata leda dake cike da kaya a jikinta ya mik'awa Safna, Tare da cewa.
"Ansa ki bud'e ki duba ki gani, Idan sunyi miki saiki sanar dani."
Safna karb'ar ledar tayi cike da son ganin abunda ke ciki, Bayan ta bud'e ne ta fara d'aga kayan tana dubawa cikin jin dad'i.
Abayas ne masu kyau ' kuma masu tsada, Ko wannen design d'inshi dabam zasu kai kala goma.
Safna murmushi kawai ke bayyana daga lips d'inta, Cikin nutsuwa tace.
"Sunyi kyau! Gaskiya kayan nada kyau sosai."
Sir-Kamal komawa yayi ya zauna ' zuciyar shi cike da farin ciki, Yace.
"Alhamdulillah! Wannan kayan nakine na baki kyauta!, daga yau inason ki ruk'a sanya su, Banason insake ganinki cikin wannan kayan na jikin ki."
Cikin fara'a Safna tace.
"Nagode."
"And, Ki duba takalman dake ciki idan sunyi miki ' ki sanar dani."
Cikin zumud'i Safna ta fara d'aga takalman tana gwadawa, Cikin sa'a kuwa duk sunyi mata kasancewar su flat-shoes ne.
"Sunyi."
Ta furta, Kanta a sunkuye.
"Good!, Ki d'auka ki tafi dasu wannan shine gift d'ina na farko."
"Na gode ' na gode Sir, Allah ya saka da alkairi."
Safna tashi tayi tabar Office d'in nashi cikin jin dad'i, Ta wuce side d'insu sam ta manta da ciwon kanda take fama dashi ' ai tuni taji ta warke.
Bayan ta isa bakin store ne taja kujera ta zauna ' gamida ajiye ledar kayan nata ta fara tunane tunane kala kala a zuciyarta.
"Meyasa yakeson farantamun rai a kullun? Gaskiya Sir-Kamal yana da kirki, Ni duk na k'osa in nunawa Umma wannan kayan."
Tana cikin wannan tunanin ne Muneeba tazo wajen..
"Lafiya daiko? Kika zauna ke kad'ai kina murmushi."
"Uhm! Lafiya k'alau Muneeba."
Muneeba kallon ledar dake gaban Safna tayi.
"Meye a cikin wannan ledar kuma? Don naga dai bada ita kikazo ba."
Safna cikin fara'a tace.
"Kyauta Sir-Kamal yaimun."
Nan Muneeba ta had'e rai ta sami waje ta zauna, Tukunna tace.
"Kyautar menene?."
Nan Safna ta fad'a ma Muneeba komai da duk irin halaccin da yake mata.
"Wow! Ashe dama akwai irin ku a duniya? Marasa wayau?."
"Ban gane abunda kike nufi ba!."
"Yes da sannu zaki fahimta ai, To bari kiji Safna you have to shine your eyes! So yake kawai yaja ra'ayinki da irin wad'an nan abubuwan domin at the end kinga idan ya buk'aci wani abu daga gareki bazaki k'i basa ba."
"Yes niko insha Allah ' inhar Sir-Kamal zai buk'aci abu a wajena zan bashi, Muddin inada shi."
Muneeba tab'e baki tayi gamida jan tsaki, Tace.
"Koda kuwa jikin ki ya buk'ata?."
Nan Safna ta had'e rai tare da mik'ewa tsaye cike da tunani.
"A'a, Gaskiya Sir-Kamal bazai taba kasancewa haka ba Muneeba, Kinyi masa mummunar fahimta ' kuma ina rok'onki da kibar fad'amin haka domin kuwa alhakinsa kawai zaki d'auki."
Tsaki Muneeba taja, A zuciyarta tace.
"Ai wallahi baki isa ki fini da komai ba Safna, Talaka dake ma!."
Muneeba na gama ayyana hakan ta tashi fuuuu ta bar wajen.
Wucewar Muneeba ne Safna ta shige cikin store ' ta duba agogon wajen taga *1:30pm*, Hakan yasa ta fara preparing had'a coffee donta bawa mutanen wajen.
B'angaren Mr-Fauzan ' zaune yake da laptop a gaban shi, Amma sam hankalin shi baya kanta ' maganar Hafiz kawai ke dawo masa a rai.
"Hmm how can i even start this rubbishness? Yarinyar nan according to her Education bawani nisan karatu tayi ba!, So ta ina zan fara? Don ban taba jin sonta ba kokad'an."
Yana cikin wannan maganar ne yaji ana knocking k'ofar.
"Come in!."
Abinda Mr-Fauzan yace kenan, Tukunna ya maida kallonshi ga laptop d'in gaban shi.
Safna ce ta shigo tare da yin sallama, Hakan yasa shi amsawa ba tare daya d'ago kai ya kalleta ba, K'arasawa ciki tayi ta aje mashi coffee d'in bisa desk gamida cewa.
"Gashi coffee d'in."
Harta juya zata wuce ya tsaida ita da cewa.
"Banason insake ganin ki da wannan hijab d'in daga yau, Don zaki iya korar customers dake ziyartar company d'in nan, And ni karan kaina ma hijab d'in kyama yake bani! Muddin kinason aikin ki ya zama dole ki cenja dressing!."
Safna shuru kawai tayi idonta na kallon k'asa, Sannan Mr-Fauzan ya k'ara da cewa.
"And look! Idan kud'in siyan kayan sawa ne bakida shi, Why not ki rok'a abaki."
Jin wannan maganar ya k'ara b'atawa Safna rai batuk'a, A zuciyarta tace.
"Hm bana tunani zan juri wulak'ancin mutumin nan, Zan iya jure duk wani abu amma banda wulak'anci."
"Ke!!."
Ya kirata cikin tsawa, Hakan yasa tayi saurin d'ago kai ta kalleshi.
"Ok, Na fahimci matsalarki.
Abunda Mr-Fauzan yace kenan, Ya mik'e tsaye ya ciro wallet d'inshi ya zaro kud'i 'yan dubu dubu ya watsoma Safna dake tsaye tana kallon shi.
"Ko ba kud'i kike nema ba?."
Nan take idanun Safna suka ciko da hawaye, Kasa cewa komai tayi ta juya a guje ta bar office d'in tana matsanacin kuka.
Safna direct ta shige store ' saida tasha kukanta ma'ishi, Sannan ta fito ta d'auki gift d'inda Sir-Kamal ya bata, Harta nufi hanyar fita sai kuma ta dawo ta zarce Office d'in Sir-Kamal.
Knocking tayi sau d'aya aka bata uznin shigowa, Safna ta shiga ciki ' cikin sanyin jiki ta nemi waje ta zauna.
"I hope dai lafiya!."
Cewar Sir-Kamal.
"Nazo ne inyi maka sallama ' kuma inyi maka godiya da irin hallacin daka nunamun, Domin daga yau nabar aiki a k'ark'ashin wannan company d'in."
"Meyasa? Akwai wanda yai maki laifi ne ko wani abu?."
"Sir, Zan iya jure komai amma banda wulak'anci ' ni kuma gaskiya na gaji da wulak'ancin da mai wannan wajen kemin, Shiyasa na yanke wannan shawarar."
"To! Da kika yanke wannan hukuncin ' kina da inda zaki cigaba da aiki ne?."
Nan ta sunkuyar dakai ' tace.
"A'a banda shi, Amma zan nema aikatau inyi ' don shine daidai dani dama."
Abunda Safna ta fad'a ne yayiwa Sir-Kamal ciwo sosai hakan yasa ya runtse idonshi, Domin har cikin zuciyar shi ' ya tsani mace yarinya tayi aikatau.
"No Safna ' karkiyi aikatau please..."
Yayi maganar cikin sanyin murya.
Ita kanta tayi mamaki yadda taji muryar shi ta cenja ' cikin k'ank'anin lokaci.
"Safna ki bari ' ni zan nema maki aiki mai nagarta, Amma kafin nan akwai school d'inda nakeson insaka ki kinji?."
"Sir, Dama kabarshi amm..."
Bata k'arasa ba Sir-Kamal ya tsaida ita da cewa.
"Shhhh… bake kika sani ba! Ninasa kaina so just let me, Yanzu idan kin tafi gida ' *Around 4:00pm* zanzo inyi magana da Mahaifiyar ki."
Safna kai kawai ta d'aga mashi alaman to, Sannan ta tashi ta fita daga Office d'in.
Bayan fitar ta daga company d'in ne ta sake ganin mai keke-napep d'in nan a tsaye, Hakan yasa ta k'arasa wajen.
"Bawan Allah! Koda yaushe kana nan ne dama?."
"Eh hajiya! Ai dama aikina kenan in d'auke ki daga gida zuwa wajen aiki, Haka zalika daga wajen aiki zuwa gida."
"Duk shi Ogan nawa yasaka yin haka?."
Ta fad'a tana murmushi.
"K'warai dagaske hajiya! Yanzu ina zan kaiki?."
Cewar mai na-pep.
"Uhm! Gida zaka kaini."
Haka Safna ta shige ciki ' shima ya shiga ya tada na-pep d'in suka wuce.

_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_

Follow me on wattpad @Seemaluv1
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```      
By
*_Seemaluv👄_*

*24-25*

Bayan tafiyar Safna ne da 'yan lokuta, Sir-Kamal ya baro Office d'inshi zuwa Office d'in Mr-Fauzan.
Sir-Kamal bai kaiga k'arasawa ba ' suka had'e dashi yana fitowa daga Office d'in nasa ranshi a b'ace.
"Sir i want to have a conversation with you."
Cewar Sir-Kamal.
"I don't have time now!."
Mr-Fauzan ya fad'a yana k'ok'arin wucewa.
"Sir, It's about this lady Safna."
Jin haka yasa Mr-Fauzan juyowa ya fuskanci Sir-Kamal.
"Ok! What is it?."
"Tazo mun ne da cewa ' wai ta aje aiki, Am confuse and worried about her Sir ' Yarinyar abun a taimaka mata ne."
"Confused?."
Mr-Fauzan yayi tambayar, Sannan ya cigaba da cewa.
"Worried about her? Thank God data aje aikin, Don koda bata aje ba nizan koreta! Besides ' wannan k'azamar? Duk inda taje bazata sami aiki ba."
Mr-Fauzan yana gama fad'in haka ya gyara bottles d'in suit d'inshi ya wuce.
Sir-Kamal girgiza kai kawai yayi, Sannan ya juya cikin company d'in yana zagaye.

*After Closing...*
Chapter 9 · 0% Book details