← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 27

Sashe 14

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

B'angaren Safna kuwa ' baccinta kawai takesha, Rumaisa da Anisa suna cikin yima Umma tausane sukaji ana sallama ' hakan yasa suka amsa.
Rumaisa ce ta tashi tare da sanya hijabin ta ' ta fita.
Hafiz ne tsaye a k'ofar gidan, Yayi calming hands d'in shi.
"Ina wuni."
Hafiz jin maganar yayi kamar daga sama kasancewar baiga zuwan ta ba, Hafiz kallon Rumaisa yayi cike da tausayawa yace.
"Y'an mata ya kike? Ya mama?."
"Lafiya lau."
"Nan ne gidan su Safna ko?."
Yayi tambayar yana kallon cikin idon Rumaisa.
"Eh nan ne! Yaya tace ma, Bari in kirata."
Rumaisa juyawa tayi ta shige ciki ' Hafiz ya girgiza kai alaman tausayawa.
Bayan Rumaisa ta shige gida ne ' ta fad'a cikin d'aki jikinta na rawa.
"Yaya Safna! Ki tashi wani mutum yazo wajen ki ' mai mota."
Safna cikin magagin bacci ta tsinci maganar, Hakan yasa tayi firgigit ta farka cike da mik'a.
"Wai meye? Waye shi?."
Cewar Safna.
"Wallahi wanine dai ' kuma ba wanda yazo jiya bane."
Rumaisa ta fad'i haka with full of excitement.
Safna mik'ewa tayi ta fito tsakar gida ' ta wanke fuskarta, Tukunna ta dawo d'aki ta sanya hijabi ta fita domin duba wanda ke kiranta.
Safna koda ta fita a tsaye ta iske Hafiz jingine jikin bangon gidansu ' yana kallon mutanen da ke wucewa, Hakan yasa tayi mashi sallama ' shima ya amsa tare da juyowa ya fuskance ta.
Bayan sun gaisa ne ' Hafiz yace.
"Nasan dai baki sanni ba ko?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan Hafiz ya cigaba da cewa.
"Sunana Hafiz Khalif, In short dai ni Abokin Mr-fauzan ne wanda kika tab'ayin aiki a k'ark'ashin Company d'insa."
Sunkuyar da kai tayi ' domin sam batason ta tuna da rayuwar da tayi awajen.
"Safna! Maganan da nakeso muyi dake ' inason ki natsu kuma ki fahimceni."
"Insha Allah."
Ta fad'a a natse.
"Abokina ne ' yace inzo wajenki domin neman wata alfarma."
"Alfarma?."
"K'warai kuwa!."
Ajiyar zuciya tayi ' sannan tace.
"Wace irin Alfarma?."
"Good! Alfarma ce ta yagani yana so kuma yana so ku daidai ' domin ayi maganar aure."
Safna still tayi a wajen ta tana kallon shi ' domin kuwa makamanciyar wannan ranar take jira.
"Ko kad'an banga laifin ka ba, Domin kuwa kai abokinsa ne ' kuma shi yasan cewa bazan saurare shiba shiyasa ya turo ka kai."
Dogon numfashi Hafiz yaja ' yace.
"Ki kasance mai yafiya Safna... Kasancewar bazai iya had'a ido dake bane yasa shi ya turo ni."
"Mutumin da baisan darajar mutane ba? Mutumin da yake kyamatan talaka?."
Cewar Safna.
"Kiyi hakuri ki amince masa Safna, Kuma ki gwada ki gani..."
Tunda kafin ya k'arasa rufe baki, Tace.
"Bazan tab'a iya saka sonshi a zuciyata ba, Balle har na auresa ' domin kuwa tsanarsa ce cike a cikin raina."
"Is OK! Na fahimce ki."
Ya fad'a tare da saka hannun shi cikin aljihu, Ya ciro bandir d'in kud'in da Mr-Fauzan ya bashi ' ya mik'a mashi tare da cewa.
"Ga wannan, Ko zaki sai wani abun."
Safna kud'in ta kalla ta had'iye miyau don kuwa suna cikin buk'atar su, Lokaci d'aya kuma ta kauda kanta tare da cewa.
"Ka barshi na gode."
"A'a ki karb'a ni da zuciya d'aya na baki."
Safna k'in ansa tayi ' shi kuwa ya nace, Suna cikin haka ne Rumaisa ta fito a guje tana haki ' cikin tashin hankali Safna ta rik'ota.
"Ke lafiya?."
Cikin rawar baki Rumaisa tace.
"Yaya Safna, Umma ne ke aman jini."
"Innalillahi!."
Hafiz ya fad'i haka, Ganin yadda Safna ta shige gida a rud'e ne yasa shi bin bayanta.
D'aki Safna ta fad'a cikin rawar jiki taga Umma rigingine a k'asa tana aman jini, Hafiz d'akin ya shiga shima.
"Subhanallah this is a critical condition."
Safna kuwa hawaye kawai ke zuba daga idonta ' Rumaisa da Anisa ma kuka kawai sukeyi.
"We have to rush to the hospital, Safna ku kamata asata a mota ' akaita hospital."
"To."
Ta fad'a, Sannan ita da Rumaisa suka d'aga suka fito waje Hafiz ya bud'e mata motar suka saka ta a back seat.
"Rumaisa keda Anisa ku tsaya gida ' kafin indawo."
Safna ta fad'i haka tana share hawayen fuskarta.
"Haba, Ya zakice su tsaya gida su kad'ai? Su shiga mu tafi kawai.
Cewar Hafiz.
Haka kuwa akayi ' Rumaisa ita da Anisa suka zauna a back seat kusa da Umma, Sannan Safna ta shiga front ta zauna.
Hafiz zama yayi cikin motar ' yayi saurin tadawa suka tafi, Kai tsaye ya wuce dasu wani babban private hospital ' yayi packing motar shi a ciki tukunna ya bud'e suka fito.
Safna ce ta bud'e inda Rumaisa ke ciki suka fito da Umma tukunna Hafiz yayi musu jagora zuwa cikin hospital d'in.
Bayan shigar sune ' Nurses suka zo cikin hanzari suka anshi Umma daga hannun su Safna.
"Please kuyi admitting d'inta kuma kuyi duk abinda ya dace, Kafin inga Doctor d'in."
Hafiz ya fad'i haka yana k'ok'arin ciro waya daga aljihun shi, Safna ta tsaida shi tayi da cewa.
"Bawan Allah na gode da k'ok'ari."
Ta fad'a cikin rawar murya ' idanu ciccike da hawaye.
"Karki damu babu komai, Yanzu dai kije ki sami waje ki zauna ' kafin inga doctor d'in."
Safna hannun Anisa ta kama Rumaisa na biye da ita suka sami waje suka zauna a wajen.
Hafiz kuwa dialing number d'in Mr-Fauzan yayi ' ringing biyu tayi yayi receiving.
"Hello! Aboki?."
Cewar Hafiz.
"Na'am Hafiz how far? Ya ake ciki?."
"Aiba k'aramar matsala aka samu ba ' in fact madai bata amince da maganar ka ba, And you know what?."
"Kai nake saurare ai."
"Muna hospital yanzu ' Mum d'inta is in critical condition, Yakamata inbaka Safna kuyi magana."
"No! No need of that."
Mr-Fauzan ya fad'i haka cikin gadara.
"Wai meyasa kake haka ne?."
"Hm Hafiz raini ne bana so!!! You know me very well, Kunyi magana da Doctor d'inne?."
Mr-Fauzan yayi tambayar.
"A'a, akwai patients d'inda yake dubawa ne, Idan ya gama zamu sameshi."
"OK then, Duk yadda kukayi dashi ' you let me know."
"OK."
Abunda Hafiz yace kenan ' Mr-Fauzan ya kashe wayar, Cikin sa'a saiga doctor d'in ya fito daga wani Ward.
Nan ya tsaya suka gaisa da Hafiz ' tukunna Safna ta taso tazo inda doctor d'in ke tsaye, Nan ta fara mashi bayanin condition d'in Umma.
Doctor juyawa yayi ' ya nufi ward d'inda aka kwantar da Umma, Hafiz dasu Safna suna biye dashi a baya.
Bayan ya shiga ne ya fara yima Umma y'an dube dube ajikin ta, Sannan yace.
"Za'a dib'i jinin ta yanzu, Akwai blood test da za'ayi mata da Scanning kafin a tantance abunda ke damun ta."
To kawai Hafiz yace ' sannan Doctor d'in ya fita, Hafiz ya sami waje ya zauna kasancewar ba k'aramar gajiya yayi ba.
Safna kuwa idon ta na kan Umma wacce take unconscious ' batama san inda take ba, Bata ankara ba taji wasu zafafan hawaye suna sauko mata.
"Yaya Safna, Ki daina kuka ' ai Umma zata warke ko?."
Cewar Anisa.
Safna jin abunda Anisa ta fad'ane yasa tayi saurin goge hawayen, Tare da cewa.
"Anisa ba kuka nakeyi ba ' karki damu."
Suna cikin haka ' aka shigo aka d'ibi jinin Umma, Sannan akayi settling scanning machine ' cikin y'an lokuta k'alilan aka kammala komai aka fitar da duk wani abunda ke damun Umma.
Hakan yasa Doctor ya kirasu ita da Hafiz ' sukaje Office d'inshi suka sameshi.
Bayan sun zauna ne Doctor ya fara yi masu bayani ' yadda zasu fahimta, Sannan ya k'ara da cewa.
"Ba komai ke damunta illa hunhunta da kitse ya rufe."
Nan gaban Safna ya fad'i, Cikin rawar baki tace.
"Likita ban gane ba!."
"OK!, Ina nufin kitse ya shiga cikin hunhunta, Yayi causing problems da dama ' Sannan kuma aka bata maganin da bai dace da wajen ba tasha! Wanda hakan shine yasa ta fara aman jini."
"Yanzu Doctor meye abunyi?."
Hafiz yayi tambayar.
"Well, Aiki za'ayi mata idan kun amince, Wannan shine kawai solution d'in inba haka ba kuma zata iya rasa ranta ' Kuma wannan aikin yanada buk'atar kimanin kud'i har miliyan d'aya! (1 million)."
Safna zaro jajayen idonta tayi wanda suka rune saboda kuka, Tace.
"Likita ka taimakeni ' ka kuma rufamun asiri, Wallahi ita kad'ai ta tarage mana gashi kuma ba muda kud'i don... "
Bata k'arasa ba Hafiz ya dakatar da ita da cewa.
"Karki damu ' wannan aiba wasu kud'i bane masu yawa."
Safna baki ta saki ' tana kallonshi cikin mamaki, Sannan Hafiz ya maida kallonshi kan doctor.
"Doctor, wannan bazai zama matsala ba ' yanzu dai a d'aurata akan magunguna kafin kud'in su samu."
"Alright, To shikenan ' yanzu na baku nan da sati d'aya ku kawo kud'in."
Cewar Doctor.
Safna da Hafiz tashi sukayi suka bar Office d'in zuwa ward d'in da Umma tace, Safna ta tsaida shi da cewa.
"Amma a ina zaka sami wad'an nan kud'i?."
Ta furta haka cikin sanyin jiki
"Safna kenan! Ai kinada inda zakije ki nemo kud'in."
"Wallahi babu inda zanje abani wad'an nan kud'in masu yawa."
"Akwai!."
Hafiz ya fad'i haka, Hakan yasa ta juyo ta kalleshi ' taga fuskar shi babu wasa aciki.
"Ina kenan?."
"Wajen wanda kika tsana ' kika k'i yarda da abunda ya nema a wajenki, Tabbas zaki sami kud'in wajen Abokina Fauzan."
Ajiyar zuciya ta saki mai k'arfi, Sannan ta fara tuna halin da Umma ke ciki ' da kuma bayanin da Doctor yayi masu.
Cikin Muryar kuka ' tace.
"Amma kana ganin zai bani kud'in?."
"Why not?, Karki damu zanyi mashi bayani ' kuma am very sure zai baki, Yanzu ki koma wajen Ummanki ' zanje indawo."
Abunda yace kenan! Ya juya bar Hospital d'in, Sannan itama ta wuce wajen Umma.

*** *** *** *** *** *** *** *** ***

*AROUND 1:00PM*
Chapter 14 · 0% Book details