← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 27

Sashe 25

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan sun gama breakfast ne Daddy ya tashi ya wuce wajen aiki, Mr-Fauzan shima mik'ewa yayi gami da gyara necktie d'in shi yace.
"Ki same ni cikin motor."
Ya fad'awa Khairat haka, Jin haka yasa Khairat ta ajiye cup d'in tea d'inta ta wuce d'akin ta cikin hanzari.
Gele ta yafa a k'irjin ta ' ta d'auki side back d'in ta ta fito, Khairat parlor ta dawo ta sallami Mummy tukunna ta fita.
Koda ta fito cikin motor ta sami Mr-Fauzan zaune, Hakan yasa ta bud'e front seat ta shiga ta zauna tare da cewa.
"Yaya, Na shirya."
Nan take Mr-Fauzan yayi dialing number d'in Hafiz.
Ringing d'aya tayi Hafiz yayi receiving.
"Babban Mutum!."
Cewar Hafiz.
"Hafiz, Am on my way coming to your house now ' ka shirya tare zamu je ta'aziyyar."
"Shit!... OK to sai ka iso."
Nan Mr-Fauzan yayi ending call d'in ya tada motor suka nufi gidan su Hafiz.
B'angaren Hafiz, Bayan ya gama waya day Mr-Fauzan ne ya tashi ya fad'a bathroom yayi wanka, Sannan ya shirya cikin milk d'in yadi mai tsada.
Hafiz shiryawa yayi tsaf ' ya fito parlor yayi breakfast a tsaitsaye, Hajia na lura da hakan.
Hafiz harya kama hanyar fita ne Hajia ta dakatar dashi da cewa.
"Hafiz lafiya kuwa? Ina zuwa haka?."
Hafiz juyowa yayi ya fuskanci Hajia tare da cewa.
"Akwai inda zamuje ne nida Fauzan, Banaso yazo ban gama shiryawa bane."
Aleeza dake gefen Hajia a zauna gaban ta ya fad'i da sauri ta juyo ta kalli Hafiz.
"Oh shine yasa kake ta abu baga baga kamar zaka tashi sama?."
Hafiz juyawa yayi ya fice cikin walwala tare da cewa.
"Eh mana."
Aleeza tashi tayi zata wuce kitchen Hajia ta tsai da ita da cewa.
"Ina kuma zakije Auta?."
"Hajia, Kitchen zanje zan yiwa mai aiki magana ne."
To kawai Hajia tace, Sannan Aleeza ta wuce kitchen, Iske 'yar aiki tayi tana goge goge.
"Yawwa, Don Allah inason kimin wani abu ne."
Cewar Aleeza.
"To."
"Kije harabar garage ki tsaya, Akwai wani abokin yaya Hafiz da zaizo ' da zarar yazo please kizo ki fad'amin."
To kawai 'yar aikin tace ta cigaba da gogen ta, Hakan yasa Aleeza tayi saurin ansar tsumman tare da cewa.
"No! Kije kawai, Bara na cigaba kafin ki dawo."
Haka 'yar aikin ta wuce harabar garage ta tsaya wajen flowers, Shi kuwa Hafiz na zaune k'ark'ashin rumfa rik'e da wayar shi yana jiran zuwa Mr-Fauzan.
Aleeza jefar da tsumman tayi nan wajen ta dawo parlor ta fara safa da marwa.
Hajia na zaune gefe tana kallon ta, Aleeza tana cikin haka wayar ta dake saman three seater ta fara ringing ' hakan yasa tayi sauri ta je ta d'auka.
Ganin Dr Khalil ne yasa tayi receiving cikin fara'a, Bayan sun gaisa ne kamar kullun ' Dr Khalil yace.
"I hope kin shirya ma zuwa ko?."
"Insha Allah."
Nan suka cigaba da hirar su, Hafiz na zaune yaji hone hakan yasa shi yin saurin mik'ewa tsaye tare da cewa.
"Yawwa, Bud'e gate d'in da sauri."
Hafiz ya fad'awa gate man haka.
Bayan gate man ya bud'e gate ne kamar yadda aka umurce shi, Mr-Fauzan ya shigo da motar shi ciki.
Bayan yayi parking motar shine ya fito, Cikin fara'a Mr-Fauzan da Hafiz sukai hands shake.
Ganin haka yasa 'yar aikin ta juya ta koma da sauri.
Aleeza na cikin wayan ne 'yar aikin ta shigo cikin parlor gami da cewa.
"Gaya cen ya zo."
Jin Hakan yasa Aleeza tayi saurin cewa Dr Khalil.
"We will talk later, Babye."
Abinda tace kenan tayi ending call.
Aleeza wajen window ta koma tana lek'en su Mr-Fauzan.
"Wa kike lek'e ne wajen?."
Cewar Hajia.
"Ohhhhhh! Hajia bafa kowa! Naji kamar tsayawar mota ne shine fa nake dubawa."
Aleeza ta fad'i haka cikin shagwab'a.
"To ai shikenan, Ba sai naji duka ba kuma."
Aleeza murmushi tayi tare da karkad'a kai ta koma ta zauna kusa da Hajia.
B'angaren Mr-Fauzan bayan sun gama gaisawa da Hafiz ne yace.
"Hajia na nan ko?."
"Eh tana nan, Kuma na fad'a mata zuwan ka."
"To bari Khairat taje su gaisa."
"Oh! Dama tare da Khairat kuke? Shine ta lafe cikin motor?."
Hafiz ya fad'i haka, Sannan yace.
"Bari naje nayi mata magana da kaina toh."
Haka Hafiz ya zarce wajen motar ya bud'e, Da sauri Khairat ta d'ago kai ta kalle shi tare da sakar mashi smiling.
"Ina kwana?."
"Kina nufin da bazaki je ku gaisa da Hajia ba kenan?."
Khairat kunya ce ta rufe ta yasa sunkuyar da kai gamida cewa.
"A'a dama ina da niyyar yin haka."
Abinda ta fad'a kenan ta fito daga cikin motar, Hafiz ya nuna mata hanyar shiga ta wuce ' Hafiz binta yayi da kallo harta shige ciki Sannan ya koma wajen Mr-Fauzan.
Bayan sun zauna ne Hafiz ya fara tsarawa Mr-Fauzan yadda suyi.
"Aini matsala ta da kai shegen girman kai."
Cewar Hafiz.
"Hafiz, You know me very well ' bani son raini at all... and you know that."
"Just admit it ' kana son yarinyar nan... Meye a ciki? Ni banga abin raini a ciki ba ai..."
"Shikenan... Naji I love her and I admit that... Yanzu meye abin yi? What if tak'i yarda dani?."
Hafiz dogon numfashi yaja, Sannan yace.
"Idan tak'i yarda da kai sai ka barta kawai don ba'a so dole, Although nasan Safna na sonka ' sai dai idan kak'i bata hak'uri."
"Oh come on... Meya kawo maganar bada hak'uri? Hafiz babu abinda yake bani wahala irin in bud'e baki in bada haku'ri, Musamman ga mace!."
"You see your life? Aiko hak'uri ya zama dole ka bata, Because ita mace 'yar tarairaya ce."
Mr-Fauzan nuna gamsuwar shi yayi game da maganganun Hafiz, Nan suka tashi suka nufi mota.
"Af! Wannan taje ta shantake, Let me go and call her."
Hafiz ya fad'i haka, Sannan ya nufi cikin gida domin kiran Khairat.
Mr-Fauzan kuwa cikin motor ya shiga yayi zaman shi.
Hafiz koda ya shiga ciki a parlor ya iske Khairat tare da su Hajia suna fira.
"Toh, Ke muke jira fa."
Hafiz ya fad'i haka.
Jin haka yasa Khairat ta mik'e tayi sallama da su Aleeza, Hafiz fita yayi yaje ya shige motor.
Aleeza rakiya taiwa Khairat har wajen motor, Sannan sukayi exchanging number tukunna Khairat ta bud'e back seat ta shige.
Aleeza harta juya zata wuce taji ance.
"Madam babu gaisuwa ne?."
Aleeza wani farrrrrr taji cikin ranta, Cikin sanyin jiki ta juya ' Ganin Mr-Fauzan tayi yana kallon ta a cikin mirror d'in jikin motor.
Hakan yasa Aleeza k'arasawa side d'in da yake tace.
"Ina kwana?."
Mr-Fauzan kasa ansawa yayi, Sakamakon ganin bandage d'in da ke forehead nata.
"Meya faru dake haka?."
Yayi tambayar with cares.
"Oh! Wai goshi na? I had an accident."
"How comes?."
"Well... Bayan na bar Company d'in ka abin ya faru dani."
"Hafiz kaga irin ta ko? Shiyasa banaso ana barin k'ananan yara suna driving by their selves, I don't like that at all..."
Aleeza tsuki taja Mara sauti cikin ranta tace.
"Ji rainin hankali don Allah! K'aramar yarinya ma yake d'auka ta kenan mtsw."
Nan Aleeza ta juya ta wuce rai a b'ace.
Mr-Fauzan kallon wucewar ta yayi ta glass sannan ya tab'e baki ya tada mota suka wuce.

```MY FACEBOOK FANS, NA GODE SOSAI DA ADDUAR KU GARE NI THANK YOU SO MUCH, YOU GUYS MEAN A LOT TO ME.```

*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS.*

[12/16, 8:10 PM] 0mmer Farouk: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_UNIQUE WRITERS ASSOCIATION_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*
https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/

*_FAN'S KUYI HAK'URI DA JINA SHURU DA KUKAYI, BANJIN DAD'I NE..._*
*48-49*
Chapter 25 · 0% Book details