← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 27

Sashe 27

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Around 4:00pm*
Bayan Mr-Fauzan ya maida Hafiz gidane ' tukunna ya koma gida ya aje Khairat, Sannan ya juya zuwa company.
Khairat ko data shiga ciki, Iske Mummy tayi a main parlor zaune sanye da medicated glass a idanun ta tana filling out wasu takaddu.
Da sallama Khairat ta k'arasa inda Mummy take ta zauna.
"Har kun dawo?."
Cewar Mummy.
"Eh wallahi Mom."
"Ina shi Fauzan d'in?."
Mummy tayi tambayar kanta akan takaddun da take filling.
"Aje ni kawai yayi ya juya wai he got many things to do."
To kawai Mummy tace, Sannan Khairat ta tashi zata wuce side d'in ta Mummy ta tsaida ita.
"Khairat?."
Cewar Mummy.
Khairat dawowa tayi ta zauna tare da cewa.
"Na'am."
"Ya ita yarinyar?."
"Oh Aunty Safna? Lafiyar ta k'alau, Amma saidai Mummy suna da buk'atar taimako sosai ' gaskiya na tausaya musu."
Jin hakan yasa Mummy cire glass d'in da ke idon ta.
"Kar dai Fauzan dangin talakawa ya nemo!."
Cewar Mummy.
"Haba Mummy don Allah."
Khairat ta fad'i haka.
Khairat tashi tayi gami da bubbuga k'afa da gunguni ta wuce side d'inta.
Mummy k'wafa tayi ta cigaba da abinda takeyi.
B'angaren Hafiz, Tunda ya koma gida ya kwanta yake bacci abinshi.
Aleeza kuwa safa da marwa kawai takeyi bata d'aki bata parlor.
Hajia ce ta shigo cikin parlon ta iske Aleeza tsaye tamkar wacce ke jiran tsammani, Kwalliya kuwa tamkar wata amarya ' fannin ado kam ba'a magana.
"Auta?."
Cewar Hajia.
Aleeza dake fuskantar window, Juyowa tayi ta kalli Hajia.
"Na'am."
"Akwai wanda kike jira ne?."
Hajiya tayi tambayar.
Aleeza waje ta samu ta zauna, Sannan tace.
"Hajiya dama, Wannan Doctor d'inne yace zaizo mu gaisa, Shine naji shi shuru."
Ta fad'a tare da nuna damuwa.
"Wane Doctor kenan?."
"Hajia, Doctor Khalil mana... Wanda ya duba ni."
"Ohwoo... Allah sarki, To ki sake bashi lokaci mana, K'ila akwai abinda ya tsayar dashi ne."
Abinda Hajia tace kenan ta mik'e zata koma part d'inta Aleeza taji k'arar bud'e gate.
Hakan yasa tayi saurin tashi taje wajen window domin dubawa.
"Shine..."
Aleeza ta fad'i haka tare da kama hanya zata fita, Hajia tayi saurin dakatar da ita.
"Ke Auta! Meye haka? Bazaki aji ba?."
"Hajia zanje na taroshi ne fa."
Hajiya zaunar da Aleeza tayi ta fad'a mata yadda akeyi, Sannan Hajiya ta wuce part d'inta.
Koda Dr-Khalil yayi parking motar shi ya fito, Sai da yayi 5minutes a tsaye a wajen banda missed calls da ya dunga yiwa Aleeza.
Aleeza saida taja aji tukunna ta fito garage ta nufi inda Dr-Khalil ya tsaya jiranta.
Aleeza sanye take da wata had'ad'd'iyar gown blue ' kanta kuwa rufe yake da blue tie sai kuma high hill bak'i a k'afar ta.
Bayan ta isa gare shine taimashi sallama, Dr-Khalil d'ago kai yayi ya kalle ta.
"Ya Salaam!."
Abinda Dr-Khalil ya furta kenan yana k'arewa surar jikin Aleeza kallo.
"Baza ka ansa sallamar tawa ba?."
Cewar Aleeza.
Nan Dr-Khalil ya amsa sallamar but still idanun shi na kan fuskarta.
"Mu shiga daga ciki ko?."
Aleeza ta fad'i haka.
Haka suka nufi cikin gida suna taku.
Bayan shigar su parlor ne, Aleeza ta umurce shi daya zauna ita kuma ta wuce kitchen ta d'auko drinks ta kawo mashi, Sannan ta koma ta zauna.
Haka suka sha firar su Dr-khalil yana yi yana kora drink a baki.
*35minutes later...*
Bayan sun gama hirar tasu ne Dr-khalil ya tashi domin yin haramar komawa, Haka Aleeza ta tashi itama suka fito harabar garage suka tsaya inda yayi parking motar.
"Let's get in ' ko?."
Cewar Dr-Khalil.
"Okay."
Aleeza ta fad'a sannan suka shige cikin mota.
Bayan shigar sune Dr-Khalil yaja dogon numfashi yace.
"Na gode da tarba mai kyau Aleeza."
"Anytime..."
Ta furta a tak'aice cikin fara'a.
Nan Dr-Khalil yasa hannu a aljihu ya ciro d'an k'aramin box ya mik'a mata.
"Please take it."
Aleeza kai ta girgiza mashi alaman a'a.
"I said please... Ba don ni ba."
Ya fad'i haka with sounds of pleading.
Aleeza karb'a tayi ta tsaya tana kallon box d'in.
"Open it."
Dr-Khalil ya fad'a.
Aleeza bud'ewa tayi taga necklace fari mai hasken diamond.
"Wow..."
Ta furta a hankali.
"I love you Aleeza..."
Jin maganar tayi ta doshi cikin k'wak'walwar ta tayi saurin kallon shi.
"Yes Aleeza, Ki amince dani."
Aleeza harta bud'e baki zata yi magana sai kuma ta tuna da maganar Hajia, Cewan ta dunga jan aji.
"Thank you for the splendid visit..."
Abinda ta fad'i kenan ta bud'e motar ta koma cikin gida cikin sauri.
Dr-Khalil ajiyar zuciya yayi tare da yin k'wafa yace.
"Zaki shigo hannu."
Nan ya tada motar shi ya wuce.
Aleeza tana tsaye wajen window tana kallon shi wucewar, Ganin ya tafi ne yasa ta buga uban tsalle cike da farin ciki ' ta fara rawa.
"Rawa da girgiza... Zanyi gaban ka in jujjuya! Zanyi maka albishir kayi dace da mai tarbiyy..."
Bata kaiga k'arasa wak'ar ba taji kamar motsin Hafiz zai shigo cikin parlon.
Hakan yasa Aleeza tayi saurin hayewa sama ta nufi d'akin ta.
Aleeza koda ta isa cikin d'akin k'arar shigowar text taji cikin wayar ta.
Hakan yasa tayi saurin d'aukar wayar ta duba, Ganin Dr-Khalil ne yasa tayi smiling.
"Ina sonki Aleeza, Ki amince da soyayya ta ' ke kad'ai nake buk'ata a halin yanzu."
Aleeza wurgi tayi da wayar saman gado, Ta haye gadon Tare da rungume pillow tana sakin murmushi mai d'auke da sak'onni iri iri.

*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***

*2DAYS LATER...*
```YAU TAKE SATURDAY, RANAR BIKI...```

Gidan su Safna cike yake da mutane, Gaggo Mariya da dangin Mahaifin su Safna ne keta hidima cikin gidan.
Duk da dai dangin mahaifin nata d'aid'aiku ne suka zo, Amma Safna tayi farin ciki matuk'a.
Safna zaune take a k'ofar d'aki anayi mata lalle mai kyau.
Goggo Mariya ce tazo inda Safna take ta zaune.
"Ke kuwa mai lalle kiyi sauri fa, Domin nan *1:00pm* za'a d'aura auren kuma yanzu gashi *12:00pm*."
Goggo Mariya ta fad'i hakane tana yiwa Safna murmushi.
Safna kuwa kunya ce ta rufe ta yasa ta sunkuyar da kanta tana murmushi.
"Safna?."
Cewar Goggo Mariya.
Safna kai ta d'ago ta kalle ta tare da cewa.
"Na'am."
"Safna, Na yarda zan rik'e su Rumaisa kinji ko?."
Safna waro idanu tayi cike da farin ciki.
"Alhamdulillah, Goggo Mariya na gode sosai ' gaskiya bamu da kamar ki."
Safna ta fad'i haka tamkar zatayi kuka.
"Haba.... Yo idan ban rik'e ku ba waye zai rik'e ku?."
Goggo Mariya ta fad'i haka gamida tashi ta koma wajen girkin da suke yi.
Suna cikin hakane wani yaro ya shigo cikin gida.
"Wai ance ana kiran Safna."
Abinda yaron nan yace kenan ya juya yayi gaba abinsa.
"Kinga bar lallen nan, Bara naje na duba wanene..."
Cewar Safna.
Safna tashi tayi ta fita, Ganin Sir-Kamal tayi a tsaye jikin motar shi.
Haka Safna ta k'arasa wajen shi da d'anyen lalle a hannun ta tare dayin sallama ' ya amsa.
"Naga kamar kuna hidima ne."
Safna murmushi tayi ta sunkuyar da kai.
"Eh, Kayi hak'uri bansami damar fad'a maka ba..."
"Me kenan."
"Aure zanyi..."
Ta fad'a a tak'aice.
Sir-Kamal shock yaji at the same time kanshi ya d'aure.
Wani irin tafasa zuciyar shi keyi idan da zaku lura da fuskar shi jijiyoyin shi duk sun tashi.
Sir-Kamal dakyar ya iya bud'e bakin shi yace.
"Amma... ina taya ki murna Safna, Wane ne ne Angon?."
"Ogan ka Fauzan."
Cikin mamaki Sir-Kamal ya tsaya yana kallon ta.
"Am... Safna dama kawai nazo duba ki da lafiyar ki ne, Ni yanzu zan koma."
Ya fad'i haka tare da bud'e motar shi zai shiga.
"Am... A babban masallacin juma'a za'a d'aura auren, Ina gayyatar ka."
Safna ta fad'i haka cike da nuna farin ciki.
"To! Na gode."
Ya fad'i gamida shigewa cikin motar shi yaja ya wuce.
Safna komawa gida tayi ta zauna aka idasa lallen, Sannan ta aka kai mata ruwan wankan ta ban d'aki.
B'angaren Mr-Fauzan kuwa, Gidan nasu shima mak'il yake da jama'a.
Cikin garage kuwa cike yake da Abokan Ango, Da kuma Abokan Daddy.
Mr-Fauzan ne ya iso cikin garage d'in cikin manyan kaya ' Hafiz yazo ya tareshi suka k'arasa cikin mutane.
Mr-Fauzan farar shadda ce sanye a jikin shi riga da wando da kuma malin malin, Da hular shi black color ' sai wristwatch golden mai tsada.
Mr-Fauzan komai na jikin shi to-match ne kuma mai tsada.
Haka aka shish-shiga motoci masu tsada na gani na fad'a, Suka nufi Babban masallacin juma'a domin d'aura aure.
B'angaren Safna kuwa, Har tayi wanka ta shirya tayi kwalliya ta k'ure kwalliya iyakar yinta.
Kayan dake jikin ta atampa ce gadagalle sabuwa ' wacce Goggo Mariya ta kawo mata.
Haka Safna ta k'unshe d'aki sabida kunya da 'yan k'annanta.

*1:00pm dot* aka d'aura auren *Mr-Fauzan&Safna*.

Safna na zaune a d'aki ne, d'aya daga cikin wakilen nata ya shigo ya sanar musu cewar Aure ya d'auru.
Gaba d'aya gidan hamdala suka shiga yi, Safna kuwa ji tayi tamkar ta nutse sabida kunya.
"Aunty Safna zan biki cen..."
Inji Anisah.
"Toh Anisah, Karki damu awajen Goggo Mariya zaku zauna ' ni kuma kullun zanzo na rik'a duba ku."
To kawai Anisah tace, Goggo Mariya ta shigo d'akin.
'Yan nasihohi Goggo Mariya taita yiwa Safna, Yi nayi bari na bari da dai sauran su.

*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS."
Chapter 27 · 0% Book details