← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safna taji ana buga table d'inda ta d'ora kanta akai, Hakan yasa ta farka daga baccin tare da d'ago kai domin taga waye.
Wani Mutum ta gani sanye da suit a jikin shi ' Chocolate colour, Zubin masu kad'i.
"Who are you?".
Nan nefa Safna ta kauda kanta daga kallon da take mashi ' ta koma kallon sama don duban hadari.
"Ashema angama ruwan!"
Shima juyawa yayi ya dubi sama.
"Oh yes angama, and am advising u, koma wacece ke kibar wajen nan ' kafin nakira securities".
Ai nan Safna ta mik'e tsaye gami da zaro ido.
"Don Allah ka taimaka mun! Wallahi aiki nazo nema ido rufe, Sir koda Shara ne zanyi muku sai ku biyani".
Kujera yaja ya zauna, sannan yace.
"Hope kina da takaddun ki a hannu?".
"Eh dasu nazo".
Miko mata hannu yayi ta bashi takaddun nata ' ya duba tsaf sannan ya mik'a mata.
"Kamata yayi kije ki cigaba da karatun ki ' inyaso saiki dawo mu baki aiki".
"Sir nidai a taimaka mun insamu da secondry school certificate d'in".
"Well... Is ok if that's what you want, Ammm are you good in making Coffee?".
"Coffee?".
"Yes Ruwan bunu".
"Amm.. A'a...".
Bata kaiga k'arasawa ba ya katseta da cewa.
"Then saikije ki koyo ' domin shine zai zama aikin ki dazaki rik'ayi a wannan Company".
"OK! Na gode".
"Am KAMAL ABUBAKAR ni ne mataimakin mai wannan Company ma'ana (P.A), You can call me Sir Kamal Ok?".
Ta d'aga mashi kai alaman To.
"Sir, Yaushe zan fara aikin?".
Murmushi yayi mata ' ganin ta cika sauri.
"Ai zaki fara ' har saikin gaji".
"Hmm".
"Yanzu tashi zakiyi ' ki biyoni mu shiga Office d'ina, Domin insamu wasu informations a tsanake."
"Har ina ne wajen?".
Kamal sauri yayi ya d'ago kai ya kalleta.
"Office d'ina mana!".
"Hmm... Nidai da dai zamu iyayin komai anan".
"What!? You are not serious!, Look inada aiki sosai a gaba na ' so ki tattara inaki inaki kibar wajen nan".
Kamal tashi yayi cikin b'acin rai zai bar wajen tayi saurin rik'o gefen rigar shi, Gami da zubewa k'asa.
"Sir Kamal! Am sorry, ka taimakamun don Allah ' na yarda muje cikin office d'in naka amma kuma inaso ka rik'e Allah ya zuciyar ka".
"It's Ok".
Haka Safna ta bishi suka shige cikin ma'aikatar securities da sauran ma'aikatan kallonta kawai sukeyi, Ita kuwa Safna wurga idanu kawai takeyi tako ina har suka isa cikin Office d'in.
Kamal a kujerar shi yaje ya zauna ' gami da zaro takarda, Sannan ya d'auki pen daga desk d'in shi, Zai fara rubutu kenan ya ankara ashe a tsaye take har yanzu.
"Madam!".
Ta d'ago kai ta kalleshi tare da cewa.
"Sir!".
"Zaki iya zama".
Safna waje ta samu ta zauna ' sannan ta maida kanta k'asa Kamal ya cigaba da rubutu.
Sai da ya kammala ne ya d'ago kai ya kalleta tare da mik'a mata takaddan.
"Am..ansa wannan ' zaki dawo ranar monday! Wannan takaddan itace zaki nunawa securities idan kinzo, Understand?".
"Yes".
"Good! But before then, Ya kamata inji sunan ki ' infact you have to introduce yourself to me now!".
"Ok, Sunana Safna Habib! Ina zaune ne ana k'auyen GATORIYA, Kuma ni marainiya ce mahaifina ya rasu ' sai mahaifiya ta wacce take d'awainiya damu...".
"Ya Salaam! Allah yaji k'anshi".
"Amin".
"Insha Allah zaki sami aiki Safna ' Zanyi magana da Ogana kinji?".
"Nagode".
"Shikenan! Zaki iya tafiya yanzu".
Safna tashi tayi rik'e da takaddan ta ahannu, Tabar Office d'in cikin hanzari tana fita suka ci karo da wani har suna bangazar juna.
Wani Handsome guy ne ' mai kamala shima cikin suit, Fari ne zubin larabawa ' da bloothode d'in shi sanye a kunne, Matashi ne d'an kimanin shekara 30.
"Whattaaa!!!".
Abunda taji ya furta kenan tajuyo cikin tsoro ta kalleshi.
"Kayi hak'uri don Allah".
"What? Are you blind? Wacece ke? Daga ina? And who gave you the permission to...".
Bai k'arasa ba tayi saurin katseshi da cewa.
"Ha'a bana baka hak'uri ba? Hmm".
Tana gama fad'in haka ta juya ta wuce.
Mamaki ne ya cikashi ganin yadda ta juya ta wuce without begging.
"Wace yarinya ce wannan? She don't even have manner, i will surely find out ' mtsww".
Yana fad'in haka ya juya tare da sanya hannun shi cikin aljihu ya wuce.

*DEDICATED TO MY FAN'S*
😘😘😘
[12/1, 7:39 PM] ‪+234 703 270 1670‬: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*

*_Seemaluv is back again!!!..._*

*26-27*

Bayan komawar Sir-Kamal gida ne yaga shigowar kiran Mr-Fauzan, Cikin sauri yayi receiving.
"Hello Sir!."
"Kamal, Inason ka turomin da address d'in wannan yarinyar."
Mr-Fauzan ya fad'a a tak'aice.
"Wace Yarinya kenan?."
"Ha'a karka cemun baka gane abunda nake magana ba! That k'azama wacce tabar company na."
"Oh! Safna?."
"Whatever her name is! Nidai ka turomun address d'in gidan right away."
"OK."
Abunda Sir-Kamal yace kenan, Mr-Fauzan ya kashe wayar.
Sir-Kamal, Mamaki ne yacika shi ' ganin yadda Mr-Fauzan ke neman address d'in gidan su Safna.
"Ha'a to meyafaru haka? Me kuma ya k'ara had'ata dashi?."
Sir-Kamal bai wani b'ata lokaci ba, Yayima Mr-Fauzan sending address d'in gidan ' sannan ya fice zuwa masallaci, Kasancewar lokacin sallar magrib yayi.
*AROUND 8...PM*
Bayan Mr-Fauzan ya dawo daga mosque ne ' ya sami waje ya zauna a parlor ya fara duba wayar shi ' ya ga text d'in Sir-Kamal, Hakan yasa shi dubawa ' ganin abunda ya buk'atane yasa shi dialing number d'in Hafiz, Ringing d'aya zuwa biyu ya d'aga.
"Babban mutum, Ya akayi ne?."
Cewar Hafiz.
"Lafiya k'alau, Nasami address d'in gidan su fa... Soboda haka Hafiz ' kai zakaje ka fara yi mata magana."
"Oh come on! Kai d'in fa? Tare ya dace muje ai."
"Hafiz, kaje kawai! Please inda hali ma ni kawai akawomin ita gidana as my wife ' ba tareda nayi wasting time d'ina ba."
Cewar Mr-Fauzan.
"Ha'a haba Aboki? Wace irin magana ce haka?."
"To shikenan, Yanzu dai ka fara zuwa tukunna ' and you know what?.
"Sai ka fad'a."
Cewar Hafiz.
"We have to meet ' kafin kaje wajen ta, Zan baka kud'inda zakayi spending mata ' because kasan irin su saida haka."
"Alright, Shikenan ' Gobe Around *12:00pm* zanzo in ansa sai inwuce gidan nasu."
"To shikenan."
Sallama sukayi ' sannan Mr-Fauzan ya kashe wayar shi, Ya Cigaba da kallo.
Mr-Fauzan na cikin kallo ne ' Daddy ya dawo daga wajen aiki d'auke da sallama ya shigo cikin parlor, Mr-Fauzan amsa sallamar yayi gamida yi mashi sannu da dawowa.
Bayan Daddy ya wuce ne ' Mr-Fauzan yace.
"I don't think ' Daddy yasan abunda Mummy ke shirin yi."
A zuciyar shi ya furta hakan.
Tashi yayi ' ya koma d'akin shi ya zauna a kujerar sofa tare da janyo laptop d'inshi zai hau aiki.
Mr-Fauzan yana cikin hakan yaji wayarshi ta fara k'ara alaman kira, D'auka yayi ya duba ' ganin Number ce yasa shi tab'e baki gami da cewa.
"What a trashy!"
Ya fad'a gami da maida kallon shi zuwa kan laptop ba tare da yayi receiving call d'in ba.
B'angaren Aleeza kuwa zaune take a d'akinta rik'e da wayarta a hannu tana kiran number d'in Mr-Fauzan, amma baya d'agawa.
"Meyasa bazakayi picking ba? Please pick up my call Fauzan..."
Abunda Aleeza taita nanatawa kenan a zuciyar ta, Gami da sake dialing number d'in ' ganin baiyi receiving bane yasa tayin wurgi da wayan saman gado cikin zafin rai.
Aleeza kwalla ne suka ciko Idonta ' tayi saurin mayar da hawayen.
"Wallahi inason shi..."
Abunda ta furta kenan, ta bud'e wadrope ta ciro night gown ta sanya ' sannan ta haye gado taja blanket.

*** *** *** *** *** *** *** ***

*Washe gari...*
Da assussuba Safna ta tashi ' ta tada su Rumaisa da Umma, Sukayi Sallah ' sannan Umma ta koma bacci kasancewar ta tashi da zazzab'i.
Safna Umarni ta bawa Rumaisa dataje ta fara wanke wanke, Ita kuma sai tayi shara daga nan ta d'aura ruwan zafi a murhu domin dama koko.
Misalin k'arfe *6:00am*, Su Safna suka kammala aikin gidan ' Safna d'aki ta nufa ta tada Anisa daga bacci.
"Jeki wajen Rumaisa ta zuba maki koko kisha, Ki kuma wanke baki tukunna."
To kawai Anisa tace ' ta wuce, Sannan Safna ta fara yiwa Umma magana cikin siga ta tausayawa.
"Umma?."
Umma d'an motsawa tayi tare da sakin ajiyar zuciya.
"Umma, Ki tashi kisha koko ' daga nan sai inje chemist in anso maki magani."
Umma tashi zaune tayi ' tana shivering, Safna ta fita cikin hanzari ta d'iboma Umma kokon a cup ta kawo mata.
"Gashi Umma! Ki daure ki shanye ' kinga ko suga bansa ba, Ni bari inje chemist d'in insiyo maka magani."
"Toh."
Abunda Umma ta iya furtawa kenan ' Safna ta d'auki hijabin ta ta sanya ta bar d'akin, Harta kama hanyar fita sai kuma ta dawo.
"Rumaisa! Ku tashi ku koma d'aki wajen Umma, Don batajin dad'i."
Rumaisa da Anisa, Tashi sukayi suka koma d'aki wajen Umma ' Sannan Safna ta fice.
Kai tsaye Safna ta nufi chemist aka harhad'o mata magun guna kala kala sannan ta juyo ta kama hanyar dawowa gida.
Cikin sauri take tafiya ' daka ganta kasan a uzurce take.
Bayan ta dawo gida ne ' ta kaima Umma magun gunan had'e da ruwa tasha.
Haka Umma ta ansa tasha maganin ' tukunna ta koma ta kwanta, Safna dasu Rumaisa sannu kawai suke mata tana ansawa agajiye.
Safna kwantawa tayi k'asa saman tabarma ' tare da cewa.
"Rumaisa bari ind'an runtsa, Nad'an lokaci."
To kawai Rumaisa tace, Sannan Safna ta fara bccinta cikin kwanciyar hankali.

*AROUND 11:30AM*
Chapter 12 · 0% Book details