← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Hafiz ya aje Mr-Fauzan gida, Sannan shima ya koma gida.
Mr-Fauzan koda ya shiga cikin gida ' a harabar parlor ya tsaya ganinsu Mummy da Daddy zaune suna kallo.
Mr-Fauzan sallama yayi Daddy ya amsa ' sannan ya k'arasa wajensu ya sami waje ya zauna, Tukunna yace.
"Daddy, Na sami wacce zan aura ' kuma mahaifiyar ta tace inturo zuwa gobe."
Daddy maida kallon shi yayi kan Mr-Fauzan yace.
"To Alhamdulillah, A ina suke?."
Nan Mr-Fauzan ya fad'awa Daddy komai da duk abinda abinda ya k'unshi rayuwar da suke ciki, Sannan ya k'ara da cewa.
"Amma Daddy Mahaifiyar ta tana hospital a yanzu haka, Kuma tace babu damuwa zama a iyayin bikin tana kwance."
"Subhanallah! Meke damunta kuma?."
"Eh aiki dai za'ai mata, But nina d'auki nauyin aikin ' bayan biki I mean next week za'ayi mata aikin."
Maganar Mr-Fauzan ne yabawa Daddy dariya, Hakan yasa yace.
"Wato dai Son, Kana nunfin next week za'ayi auren kenan?."
"Eh Daddy, Saboda abunda na riga na tsara kenan."
"Very Good!, To Allah ya kaimu goben sai muje hospital d'in, Allah kuma ya maka albarka."
Ameen Mr-Fauzan yace ' ya tashi zai wuce Mummy tace.
"Fauzan?."
Juyowa yayi ya kalleta with cares.
"Na'am Mum."
"Ina fatan dai ba dangin talaka zaka kawo mana ba!."
Har Mr-Fauzan ya bud'e baki zaiyi magana Daddy yayi saurin cewa.
"Yi tafiyar ka Son."
Mr-Fauzan part d'inshi ya nufa, Sannan Daddy yace.
"Wai kekam meyasa kike haka? Haba! Su talakawan ba mutane bane?."
"Mutane ne amma..."
"Amma what!?."
Mummy tashi tayi ta haura sama cikin k'unk'uni, Tukunna shima yabi bayanta.
B'angaren Mr-Fauzan kuwa, Yana shiga bedroom d'inshi ya cire kayan jikin shi ' ya bari daga shi sai boxer ya fad'a bathroom domin yin wanka.
Mr-Fauzan yana jikin wanka ne ' maganganun daya fad'awa Safna sukaita fad'o mashi a rai, Nan tausayin ta ya kamashi ' sam yasan cewa bai kyauta.
"She's hurt! She is really hurt."
Abunda ya dunga furtawa kenan harya gama wanka, Sannan yayo alwala ya fito.
Mr-Fauzan wardrobe d'inshi ya bud'e ya ciro jallabiya ash color ya sanya, Sannan ya fara sallar isha'i.
Bayan idarwarsa ne ' ya fito daga d'aki ya nufi kitchen ya had'a Coffee ya koma bedroom d'insa.
Mr-Fauzan a bakin gado ya zauna ' ya shanye coffee d'in tass, Sannan ya haye gado tare da kamo pillow ya rungume.
"Is like I miss something!."
Ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya, Nan bacci yayi awon gaba dashi.

_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_

*Follow me on wattpad @Seemaluv1*

*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_UNIQUE WRITERS ASSOCIATION_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*
https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/

*_@I Dedicated This Page To My Love Ones, Thank You For Support And Cares..._*

*38-39*

*_Washe gari_*
*AROUND 8:00AM*
Chapter 19 · 0% Book details