← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mr-Fauzan tunda yaja Safna bai tsaya ba saida ya tabbatar sun shiga cikin mutane, Sannan ya tunkud'ata tsakiyar su, Hakan yasa gaba d'ayansu suka juyo suna kallon shi.
Sir-Kamal ya fito kenan rik'e da files a hannunshi zai shiga Office d'in Mr-Fauzan, Yaji surutai ' hakan yasa shi juyawa ya nufi wajen.
Bayan isarshi wajen ne ' ya lura da yanayin da Safna ke ciki, Sir-Kamal harya bud'e baki zaiyi magana yaji Mr-Fauzan yace.
"Attention please!!, Musamman securities ' muddin bazaku rik'a kula da properties na company d'in nan ba to tabbas zan cenja ku in nemi wasu, Look at her."
Ya nuna Safna da yatsa, Hakan yasa dukkansu suka maida kallonsu akan Safna ' wacce hawaye kawai ke zubowa a fuskarta a sunkuye.
"Ta shiga guess-room d'ina da niyyar sata ' domin kuwa aciki na kamata, Shi dama tsiyar talaka kenan! Bai iya samun waje ba, let me warn everyone of you here! Especially securities ' dole ne ku zama masu lura, Idan kuma ba haka ba ' to lallai zan d'auki mummunar mataki.
Muneeba dake tsaye a wajen ne zuciyar ta cike da farin ciki.
"So disgusting!, Nan gaba korar ki za'ayi ma."
Ta furta hakan in murmured.
Mutanen da ke wajen ' daga mai cewa aida ganinta zata iya sai masu suratai kala kala, Safna kuka takeyi sosai ' tana girgiza kai.
Mr-Fauzan nuna Safna da yatsa yayi yace.
"And let me tell you something Ki tsaya ' a matsayin ki kawai zaifi, If not! To kina tattare da wahala arayuwarki ' k'azama kawai."
Yana gama fad'in haka ya juya ya koma office, Safna kam kasa motsawa tayi ko nan da cen saboda kunyar data sha.
Sir-Kamal, Wanda ya dad'e tsaye a wajen ranshi a b'ace cike da tausayawa ne, Ya k'arasa wajenta tare da maida kallon shi akan mutanen da sukayi carko carko awajen.
"Ina son kowa ya koma kan aikin shi ' yanzun nan!!!."
Ya fad'a a tsawace, Hakan yasa kowa ya juya ya koma kan aikin shi.
Sir-Kamal, Files d'in dake hannun shi ya aje gefe ' sannan ya cire Suit d'inshi ta saman ' ya rufema Safna jikinta dashi tare da cewa.
"Kije office d'ina ki jira ni."
Haka Safna ta juya ta nufi office d'inshi a gaban idon shi, Tukunna shi kuma ya wuce office d'in Mr-Fauzan.
Bayan ya kammala duk wani aiki ne ' ya dawo cikin office d'in shi, Ya iske Safna a zaune tana kuka.
Kai kawai ya girgiza ' sannan ya k'arasa ciki ya zauna, Gami da yin gyaran murya.
Safna kai ta d'ago ta kalleshi da rinannun idanun ta.
"Inason ki daina kukan nan haka, Ki fad'amun gaskiyar abunda ya faru."
"Sir, Wallahi babu abunda nayi ' babu abunda na d'auka, Kawai wajen ne..."
Safna k'arashe maganar tayi cikin kuka, Kuka mai tsuma zuciya.
Sir-Kamal runtse ido yayi domin kuwa kukan har cikin ranshi yake jinsa.
"Calm down Safna! Is ok, Na fahimci cewa ya yanke hukunci ne abisa rashin sanin gaskiyar lamarin, But it's ok."
"Sir, Nidai kawai ina ganin ban shigo company d'in nan da sa'a ba, Ina ganin zan aje aikin kawai..."
"What!!! Don't you ever say that again!."
Sir-Kamal ya fad'a cikin fad'a.
"Yau yau da baki aiki ' sannan kice zaki aje? For what reason? Kinsan yadda aiki yake da wuyar samu kuwa? Ko don kinga kin samu cikin sauk'i?."
Safna lura tayi ranshi ya b'aci, Hakan yasa ta sunkuyar dakai ' tare da cewa.
" Sir!, idan abunda na fad'a ya b'ata maka rai kayi hak'uri..."
Ajiyar zuciya kawai yayi ' sannan yace.
"Idan lokacin tashi yayi ' karki tafi ki tsaya ki jirani, Ina hijab d'inki?."
"Yana a d'akin nashi."
"D'aki kuma? Uhm! Guess-room ake cewa."
Sir-Kamal wayar shi ya d'aga wacce ake amfani da ita cikin company d'in, Ya umarci security da su binciko hijab d'in Safna cikin guess-room d'in Mr-Fauzan.
Haka ko akayi ' cikin lokuta k'alilan security man d'in nan ya shigo da hijab d'in Safna cikwikwiye a hannun shi, Tare da cewa.
"Sir, here it is."
"What!!! Haka kaga ya dace ka kawomin shi? Because bakasan darajar hijabi ba ko?."
"Am sorry Sir."
Security man d'in ya fad'i haka, Sannan ya ninke hijabin ya mik'a mashi.
"Ita zaka bawa, Ba niba."
Sir-Kamal ya furta hakan cikin isa.
Safna hannu ta mik'a ta karb'a hijab d'in nata ta sanya a jikin ta, Sannan security man d'in ya juya ya fice.
"Yanzu ki tashi ' ki kawomin coffee."
Safna tashi tayi cikin hanzari ta nufi store ta had'a mashi coffee d'in cikin d'an k'an k'anin lokaci, Sannan ta dawo office d'in ba tare da tayi knocking k'ofar ba ta fad'a.
Safna sallama tayi Sir-Kamal ya amsa, Tukunna ta k'arasa ciki ta aje mashi coffe d'in gami da cewa.
"Sir, Gashi."
Sir-Kamal d'ago kai yayi ya kalleta, yace.
"Sami waje ki zauna!."
Babu musu ta sami waje ta zauna.
Nan yayi gyarar murya yace.
"Safna Habib!."
Ta d'ago kai ta kalleshi.
"Ki kasance mace mai nutsuwa, And in tambayeki?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh.
"Kinaso ki shirya da Ogana?."
"Eh Sir, Inhar hakan mai yuwuwa ce."
"Good!."
Ya furta ' sannan ya d'auki coffee yakurb'a, Tukunna ya cigaba da cewa.
"This your dressing! Dole saikin cenja shi."
Cikin mamaki ta kalleshi.
"Yes! Zaki daina sanya wannan kayan na jikin ki, da wannan hijab d'in."
"Sir! Bangane abinda kake nufi ba."
"Very soon! Zaki gane, Yanzu ki koma kan aikin ki ' After closing karki tafi ki tsaya ki jirani, Ok?."
"Ok."
Tana fad'in haka ta tashi ta bar office d'in ta wuce cikin ma'aikata, Safna koda taje wajen mutane kallonta kawai sukeyi suna zund'en ta. Ganin haka ne yasa ta juyo ta dawo bakin store taja kujera ta zauna.

*SEEMALUV NOVEL'S GROUP*
📚📚📚
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```      
By
*_Seemaluv_*👄

Follow me on wattpad @Seemaluv1

*16-17*

Bayan ta zauna ne da 'yan lokuta k'alilan, Muneeba ta iso wajen cike da shan k'anshi taja kujera ta zauna tare da cewa.
"Safna?."
Safna d'ago kai tayi ta kalleta ' ba tare da tace komai ba, Sannan Muneeba tace.
"Ko zaki fad'amun gaskiyar abunda ya faru?."
Cikin mamaki Safna tace.
"Bangane ba!."
"Ina nufin kinyi satar ko bakiyi ba? Kamar yadda Oga ya kamaki, Kuma da yadda naji mutane na fad'a don kuwa kaf workers d'in da ke cikin company d'in nan sun yarda cewa kinyi sata.
Safna nan take idonta ya cika da k'walla tace.
"Muneeba, ni nasan cewa ba sata nayi ba ' kawai dai k'addara ce."
"Well. Ban yadda dake ba Safna, Because dama irin ku sai a hankali."
"Me kike nufi?."
Ya tsine baki Muneeba tayi ' ta tashi tabar wajen, Ba tare da tace komai ba.
Safna girgiza kai kawai tayi cike da damuwa, Tana cikin haka ne lokacin tashi yayi *2:00pm* hakan yasa ta tashi gamida kakkab'e jikinta zata wuce suka had'e da Muneeba ta dawo d'aukar hand-bag d'inta domin wuce gida.
Safna fita daga company d'in tayi taje ta tsaya bakin gata, Harta tsaida mai keke-napep kenan ta tuna da abunda Sir-Kamal yace mata.
"Ohh Sam! Na manta zan tsaya injira wani, Bawan Allah kayi hak'uri ka tafi kawai."
Abunda ta cewa mai keke-napep kenan ta koma k'ark'ashin bishiya ta tsaya jiran Sir-Kamal.
Safna bata dad'e a tsaye ba Sir-Kamal ya fito cikin company rik'e da wasu documents tare da Ogan shi Mr-Fauzan, Sir-Kamal sai da ya tabbatar Mr-Fauzan ya shige cikin motar shi ' sannan ya mik'a mashi documents d'in gami da rufe mashi mota.
Ganin haka yasa Safna k'arasawa inda yake tare da cewa.
"Sir?."
Sir-Kamal jin ankira shine yasashi juyowa a uzurce, Ganin Safna ce yasa shi sakin smiling.
"Yes! I keep you waiting koh?."
Safna girgiza mashi kai tayi ' tukunna yace.
"Alright, Muje toh."
Sir-Kamal k'arasawa wajen motar shi yayi, Sannan ya umarci Safna ta bud'e motar ta shiga.
Babu musu Safna ta bud'e ta shiga ' tukunna shima ya shige, Bayan shigar shine yace.
"Safna, Nasan hankalin ki yana gida ko?."
"Eh."
"Inason in kaiki gida ' da kaina."
"No Sir, da kabarshi ma wallahi."
"Meyasa?."
Yayi tambayar yana kallon fuskarta.
"Gani nayi bazaka rasa aiki ba sosai, Kuma...".
"No ni nasa kaina ai, So just let me."
Zatayi magana kenan yayiwa motar key ' yaja suka wuce, Safna kwatancen k'auyen nasu taimashi, Sir-Kamal mamaki ne ya cika shi jin inda Safna ke zaune.
"Kai!!! Tun daga cen kike zuwa?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh.
"Okay! Insha Allah za'a nemi mafita."
Jin haka yasa Safna ta d'ago kai ta kalleshi, Shi kuwa tuk'in shi kawai yakeyi.
A haka har suka isa cikin k'auyen ' tukunna suka shiga cikin unguwar har k'ofar gidan su Safna.
"Na gode."
Abunda ta furta kenan ' ta juya zata bud'e motar, Sir-Kamal ya tsaida ita.
"Saurin me kikeyi?."
"Am... Babu komai."
"Good! Well, Yanzu kije kawai we will talk tomorrow Ok?."
Kai ta d'aga mashi tare da cewa.
"Na gode sosai."
Safna bud'e motar tayi ta fita ' ta shige gida, Sannan shi kuma yaja motar shi ya wuce.
*WANENE Sir-Kamal?*, A tak'aice Sir-Kamal mutum ne mai kyautatawa iyayen sa ' shi kad'ai ne wajen mahaifiyarsa, Mahaifinsa kuwa Allah yai masa rayuwa...
Sir-Kamal bayan ya koma gida ne, Yayi packing motar shi a packing space ' tukunna ya shige ciki ya iske mahaifiyarsa a zaune tana kallo, Hakan yasa yashiga ciki d'auke da sallama a bakinshi.
Bayan ta amsa sallamar ne Sir-Kamal ya nemi waje ya zauna, Sannan yace.
"Ammi, Yana sameki?."
"Lafiya kalau Kamal, Ya aikin naku?."
"Lafiya Ammi..."
Ya fad'a tare da sauke ajiyar zuciya.
"Kamal ' yau da farin ciki ka shigo, Meke faruwa?."
"Uhm! Ammi kenan, Ai dama kullun haka nake shigowa."
"A'a, ba kamar na yau ba dai."
Murmushi mai k'arfi Sir-Kamal yayi, Sannan ya mik'e tsaye tare da cewa.
"Uhm! Ammi kenan idan tayi wari zakiji ' yanzu dai kice ma mai aiki ta kawomin abinci na."
Yana fad'in haka ya juya ya haye sama ya wuce d'akin shi.

*AROUND 3:00PM*
Chapter 6 · 0% Book details