← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 27

Sashe 21

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*_FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS_*

*_SeemaluvNovels📚_*

*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_UNIQUE WRITERS ASSOCIATION_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*
https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/

*_@It's so sweet to say that... This page is yours alone! My new bestie Ayeesha👌👌, Ba sai nace komai ba ma!💕💕 Cox you know everything..._*

*40-41*

*AROUND 2:00PM*
Bayan Mr-Fauzan ya ajiye Daddy wajen business d'in shine ya kama hanyar komawa gida.
Mr-Fauzan a bakin gate ya tsaya gate man ya bud'e mashi sannan ya shigo.
Bayan yayi parking ne ya bud'e motar ya fito ya k'arasa ciki, Mr-Fauzan koda ya shiga parlor a zaune ya iske Mummy rik'e da remote a hannunta sanye da medicated glass a idonta.
Mr-Fauzan sallama yayi tukunna ya k'arasa cikin harabar parlor.
Bayan ya zauna ne Mummy ta kalle shi tace.
"Son?."
"Mom."
Ya furta a gajiye.
"Inaso gobe ka kawo min ita domin mu gaisa, Inason naga surukata."
"To Allah ya kaimu."
Ameen Mummy tace, Sannan Mr-Fauzan ya tashi ya wuce part d'in shi.
Bayan ya shiga bedroom d'in shi ne ya cire suit d'in jikin shi tare da takalmin shi built, Sannan ya haye gado ya kwanta.
Mr-Fauzan janyo wayar shi yayi ' yayi dialing number d'in Sir-Kamal, Ringing d'aya zuwa biyu yayi receiving.
"Kaje GIRMI hospital kuwa yau?."
Cewar Mr-Fauzan.
"No Sir."
"OK then, Kaje yanzu! ka siya musu abinda zasuci, I will transfer 10k into your account now!."
Dogon numfashi Sir-Kamal yaja, Sannan yace.
"OK."
Nan Mr-Fauzan yayi ending call d'in.
Mr-Fauzan transfer yayiwa Sir-Kamal through mobile bank.
Nan ya ajiye wayar saman side drower ya koma ya kwanta tare da rungume pillow.
B'angaren Sir-Kamal, Fitowa yayi daga company ya nufi inda yayi parking motar shi cikin hanzari.
Shiga yayi gami da yiwa motar key ' yaja ya nufi restaurant.
Sir-Kamal abinci ya siyowa su Safna, Sannan ya shiga motar shi ya nufi Girmi-Hospital.
Bayan isarsa cikin hospital d'in ne ya fito daga motar cikin sauri rik'e da ledar takeaways a hannun shi.
Cikin hospital d'in ya shiga ya nufi ward d'in da Umma take.
Sir-Kamal shiga yayi cike da sallama a bakin shi.
Safna ce tayi saurin mik'ewa tsaye tare da amsa sallamar, Nan su Rumaisa suka gaishe shi ya amsa, Sannan ya mik'awa Safna sak'on da aka bashi.
Sir-Kamal maida kallon shi yayi akan Umma yaga bacci takeyi.
"Yaya jikin Umma?."
"Da sauk'i."
Cewar Safna.
"Am.. Abinci ne a ciki inji Oga."
Sir-Kamal ya fad'i haka fuskar shi babu annuri atattare da ita.
Safna karb'a tayi tare da cewa.
"Gashima har na siyo mana abinci munci ' wannan sai dai anjima da yamma."
Sir-Kamal juyawa yayi zai wuce, Safna tayi saurin tsaida shi da cewa.
"Kamal?."
Sir-Kamal tsayawa yayi cak ba tare daya juyo ya kalleta ba yace.
"Safna."
"Kamal, Zan iya magana da kai don Allah?."
"Eh."
Ya fad'a a tak'aice, Hakan yasa Safna ta mik'awa Rumaisa ledar takeaways d'in, Sannan tabi bayan Sir-Kamal suka fito bakin hospital d'in.
"Am...Kamal..., Nasan zaka d'auke ni a matsayin butulu wacce tak'i karb'ar soyayyar ka ko?."
Safna ta fad'i haka tana kallon gefen fuskar shi kamar zatayi kuka.
Sir-kamal smiling d'in k'arfin hali yayiwa Safna gami da cewa.
"Ko kad'an, Ai nasan kina da dalilin yin hakan."
"Kamal, Yin hakan shine alkairi a gareni, Banaso na amshi soyayyar ka daga k'arshe kaga kamar na yaudare ka.
"Na fahimce ki Safna, Amma inaso ki sani bazan daina sonki a cikin zuciya ta ba."
Safna girgiza kai tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa idanuwan tane suka cicciko da kwalla.
"Kamal, Ka cewa Ogan ka nagode ' kuma don Allah inaso ka cire zancen sona a ranka, Mu zama abokai."
Safna na gama fad'in haka ta juya ta koma ciki, Sir-kamal right hand d'in shi ya dunk'ule zuciyar shi na mashi k'una.
Sir-Kamal wajen motar ya nufa cikin hanzari ya tada motar ya bar hospital d'in.
Sir-Kamal gida ya wuce direct, Bayan yayi parking motar shi a compound ne ya fito ya shige cikin gida.
Kasancewar bai sami kowa a parlor bane yasa shi shigewa bedroom d'in shi kai tsaye.
Sir-Kamal kayan jikin shi ya cire ya ya shige bathroom, Koda ya shiga shower ya kunna ya tsaya tsakiya ruwa na ratsa jikin shi.
Takaicin maganganun Safna kawai ke fad'o mashi a rai.
"Meyasa baza kice kina sona ba? Why? Didn't I deserve to be loved?."
Abinda Sir-Kamal ya rik'a fad'a a cikin zuciyar shi kenan, Nan ya rufe shower d'in gami da d'aura towel a k'ugunshi tukunna ya fito.
Sir-Kamal koda ya fito k'ana nan kaya ya ciro ya sanya sannan ya fito daga d'akin.
Ta parlor ya biyo zai fita suka had'e da Ammi tana shigowa cikin parlon.
"Kamal?."
"Na'am Ammi."
"Ina zuwa kuma ' ka dawo ko hutawa baka yi ba?."
Ammi ta fad'i haka tare da zaunawa saman kujera.
"So nake inje ziyarar wani friend d'ina."
"Kamal dawo ka zauna na tambaye ka."
Jin hakan yasa Sir-Kamal dawowa harabar parlor ya zauna a k'asan kujerar da Ammi ke zaune.
"Ammi gani."
"Kamal, Kana cikin damuwa ko?."
Cewar Ammi.
Sir-Kamal 'yar dariyar k'arfin hali yayi yace.
"Ammi kenan, Ni banda wata damuwa please karki d'aga hankalin ki."
"Ka tabbata?."
"Eh Ammi."
Sir-Kamal ya fad'i haka tare da duba wristwatch d'in hannun shi yace.
"Ammi, Bara inje."
To Ammi tace sannan Sir-Kamal ya tashi ya fice.

*** *** *** *** *** *** *** *** ***

*AROUND 4:00PM*
Chapter 21 · 0% Book details