← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Hafiz ya koma gida ' yayi wanka yaci abinci, Tukunna ya kira Mr-Fauzan awaya ' bayan ya sanar dashi komai da duk damuwar da Safna ke ciki a yanzu, Mr-Fauzan yace.
"Zanyi amfani da wannan damar ' in tursasa mata dole sai ta aure ko tana so ko bata so."
"Hmm... Aboki kenan bakada dama ' kamar kana son yarinyar nan fa!."
"Oh Come on! Sam babu sonta a raina ' me zanyi da wannan k'azamar? Kawai zan aureta ne don banason Mummy na ta auramun wanda banaso, You know me very well Hafiz."
Murmushi kawai Hafiz yayi ' yana jinjina maganar Mr-Fauzan.
"Yanzu a wane hospital suke?."
Cewar Mr-Fauzan.
"Suna private hospital girmi, And please ka aika akai musu abinda zasuci ' because basuci komai ba."
"Alright, Zan tura P.A Kamal, Hafiz inason Monday ka kawo ta Office d'ina."
Ya fad'i haka agadarance.
"OK I will do that."
Nan sukayi sallama da junan su ' Mr-Fauzan ya kashe wayar, Sannan yace.
"Duk abunda ' na buk'ata saina sameshi!!!, Zaki aureni ko kinaso ko bakyaso ' That's Fauzan."
Yana gama fad'in haka ya fito daga d'akin shi zuwa garden.

_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_

*Follow me on wattpad @Seemaluv1*
[12/1, 7:53 PM] ‪+234 703 270 1670‬: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*

*_@My Bestie~Jameesha..., Wannan page d'in naki ne ' kuma zanyi amfani dashi domin Nuna how much I care about you! You're just different Besty, You're different indeed... Bari dai inyi shuru saboda sa'idawa!, In short! I love you... _*

*30-31*

Bayan ya zauna ne ' Mr-Fauzan ya d'aga wayar shi ya kira Sir-Kamal, Ringing d'aya tayi ya d'aga.
"Hello Sir."
"Amm... Kamal ' what are you doing now?."
"Nothing Sir."
"Good!, Inason kaje private Hospital Girmi ' yanzun nan, Wannan yarinyar na nan Mummyn ta batada lafiya, So I want you to go there! Ka siya musu abunda zasuci ' Ok?."
"Ok Sir!."
Cewar Sir-Kamal.
"And if you guys need something ' you let me know."
"Ok Sir."
Abunda Sir-Kamal yace kenan, Mr-Fauzan ya kashe wayar shi.
Sir-Kamal mamaki ne ya cika shi ' zuciyar shi na rayamai wani abun daban.
Tashi yayi ' ya fito daga gida ya shige motar shi gate man ya bud'e gate, Sannan ya fice a guje.
B'angaren Mr-Fauzan zaune yake a garden tunda suka gama waya da Sir-Kamal, Tsuntsaye da furanni kawai yake kallo.
Yana cikin hakan yaga Nafee tazo wajen taja kujera ta zauna ' tunda ya kalleta sau d'aya bai sake kallon taba, Nafee gyarar murya tayi zatayi magana ya d'aga mata hannu alaman dakatarwa.
"Meyasa kika zamo tamkar karya ' wacce batada zuciya?."
Kalmar daya fad'i ne ta bugi zuciyar Nafee, Don kuwa abunda tayi hating arayuwarta shine akira ta da karya.
"Ko ce miki akayi ana so dole? Mum tana deceiving d'inki ne kawai ' amma babu yadda za'ayi na aura wacce bana so."
Cewar Mr-Fauzan.
Nan Nafee ta sunkuyar da kai ' hawaye na shirin zubo mata, Tace.
"Fauzan! Inason ka! Kuma nid'in mai k'aunar kace, Ka zageni ka kuma muzantani iya muzantawa ' amma inason ka sani cewa a yau d'in nan zan bar gidan nan naku... Kuma tabbas zan dawo domin saina rama abunda kaimun."
Hawayen idonta ne suka zubo ' tayi sauri ta share, Sannan ta tashi tabar wajen.
Mr-Fauzan karan kanshi yasan she is hurt, Amma sam baiyi nadamar abunda ya fad'a ba.
Haka ya tashi yabi bayanta domin ya tabbar ko dagaske takeyi, Mr-fauzan koda ya shiga parlor a zaune ya iske Mummy da Daddy suna fira, Nan ya sami waje ya zauna shima.
*After 5minutes...* Nafee ta fito along with her trolley ' Khairat nabiye da ita abaya sai faman bata hakuri takeyi, Ganin haka yasa Mr-fauzan yatsine baki tare da nuna halin ko inkula.
Mummy ne da Daddy suka mik'e tsaye cike da mamaki.
"Nafee lafiya?."
Cewar Mummy.
"Mum! Ina d'aki fa naga tashigo tana kuka, Sannan tace mun ita gida zata wuce yau she will no longer stay with us again."
Khairat ta fad'i haka cikin damuwa.
"Nafee? Lafiya? Ko mun maki wani abun ne?."
Inji Mummy.
"No ni bakuyi mun komai ba, Nidai kawai inason in tafi gida yau am tired."
Nan Daddy ya shiga cikin maganar.
"Nafeesat, Zo zo ki zauna nan muyi magana."
Nafee sakin trolley d'in nata tayi ta sami waje ta zauna, Sannan suma suka zauna.
"Inason ki fad'amun dalilinki nacewa zaki wuce gida yau!."
"No reason! Ni dai kawai I just want to go home, And please don't stop me."
Daddy ajiyar zuciya yayi ' tare da girgiza kai.
"Shikenan Nafee bari insa driver ya kaiki."
Mummy ta fad'i haka tana k'ok'arin mik'ewa tsaye, Nafee ta tsaida ita da cewa.
"Na riga na kira driver d'in gidanmu and am sure that he's on his way now, Nagode da hallaccin da kika nunamin."
Nafee na gama fad'in haka ta mik'e tsaye tare da jan trolley d'inta ta fice, Nafee cen wajen gate ta nufa ta bud'e, Sannan ta fice ' nan ta tsaya tana jiran driver d'in gidansu.
B'angaren Mummy kuwa tunda Nafee ta fice ' take kallon Mr-fauzan, Tasan cewa duk yadda akayi he is responsible.
"Son?."
Mr-fauzan kai ya d'ago ya kalleta ' idon shi kawai ta kalla taga rashin gaskiya k'arara.
"Me kaiwa Nafee?."
"Mum! Ta fad'a miki naimata wani abune?."
"Son! Nasan abunda zaka iya da abunda bazaka iya ba, Haka nan kawai Nafee bazata ce zata wuce ba."
"Mum, Kawai fa na fad'a mata gaskiya ne ' cewa bana sonta, Nothing else."
Mr-fauzan ya fad'i haka tare da maida kallon shi akan TV.
"What!!!?."
Daddy ya furta haka cikin mamaki.
"Haba Yaya Fauzan ' wallahi tana sonka sosai."
Cewar Khairat.
"Ke ni abokin wasan kine ko? Sai na kakkaryaki awajen nan ' muddin kika sake sako bakin ki cikin maganar nan."
Zumb'uro baki Khairat tayi ' taje kusa da Mummy ta zauna.
"Wane irin rashin hankali ne wannan? Yarinya tabaro gidansu duk saboda kai!, Sannan kayi wasa da feelings d'inta haka?."
Nan Mr-fauzan ya d'an nutsu, Don ko kad'an bayason yaga ya b'atawa Daddy rai.
"To bari kaji in fad'a maka, Tunda har ka wulak'anta yarinyar nan haka! Na baka nan da 2weeks ka kawomin wacce zaka aura, Idan kuma ba haka ba! To kasa aranka tamkar Nafeesat taga gama matar kace."
Nan hankalin Mr-fauzan ya tashi, Sunkuyar da kai kawai yayi ' sannan yace.
"Daddy ' karka biyema Mum mana, Kuma... "
Bai k'arasa abunda yake shirin fad'a ba Daddy ya dakatar dashi ' ta hanyar yimasa tsawa.
"Fauzan!!, Zaka b'acemun da gani ko saina sab'a maka?."
Mr-fauzan tashi yayi ya wuce d'akin shi sumumu tamkar wanda yai k'arya.
Bayan wucewar Mr-fauzan ne Daddy yace.
"Kinji mun ja'iri? Please ki tabbatar kin kira mahaifiyar yarinyar nan."
"Insha Allah."
Daddy tashi yayi ya wuce part d'inshi, Mummy da Khairat kuma suka cigaba da kallo.
B'angaren Mr-fauzan, Yana shiga d'akin shi ya zauna a kujerar sofa tare da jinginar da kanshi yana sauke ajiyar zuciya, Wayarshi ya d'auka datake gefensa ya kira number d'in Sir-Kamal.
Sir-Kamal yana restaurant tare da Safna da k'annan ta, Yaga shigowar kiran Mr-fauzan ' d'agawa yayi cikin sauri.
"Hello Sir?."
"Kamal! Ina fatan kayi abunda nasaka."
"Eh nayi ' gamu nan ma tare dasu a restaurant, Yanzu zan maidasu Hospital d'in."
"Ok ' ka tabbatar kayi abunda ya dace."
"Ok Sir."
Abunda Mr-fauzan ya furta haka ya kashe wayar shi, Nan Sir-Kamal dasu Safna suka fito daga restaurant d'in gami da rik'oma Umma nata abincin ' domin ta samu taci bayan ta dawo conscious.
Bayan sun shiga cikin mota ne ' Sir-Kamal yace.
"Kinga wannan Restaurant d'in?."
Safna ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan yace.
"To anan na sama miki aiki ' kuma anriga anyi settling komai, Sunci inhar kin shirya zaki iya zuwa Ranar monday!."
Safna wani dad'i taji har cikin ranta, Batama son lokacin data bud'e motar ta fito ta tsaya tana kallon restaurant d'inba don kuwa babban restaurant ne.
Safna saida ta kai 5minutes a tsaye a wajen ' tukunna ta koma cikin mota.
"Na gode!, Na gode sosai ' Insha bazan yi maka butulci ba, To amma ya maganar school d'in da kace zaka sani?."
"Wannan duk ba matsala bace ' sunce zaki iya zuwa haka nan."
Safna juyawa tayi ta kalli su Rumaisa ' da farinciki ya bayyana a fuskarsu, Tace.
"Rumaisa kuyi masa godiya."
Rumaisa da Anisa godiya sukayi mashi tare da nuna farin cikin su a fili, Sannan Sir-Kamal ya tada motar shi yaja suka d'auki hanyar komawa Hospital.
Bayan sun isa cikin hospital d'in ne ' yayi packing a gefe, Sannan yace .
"Amm... Safna akwai maganar da nakeso muyi dake, Amma ba yanzu ba tukunna ' sai Umma ta sami lafiya ."
"To."
Tace cikin nutsuwa, Sannan sukayi sallama ' ta fito daga motar, Suma su rumaisa suka fito.
Sir-Kamal saida yaga shigewar su ciki tukunna yaja motarshi ya wuce.

*_Fan's d'ina kuyi hak'uri da wannan!, kuma kuyi hkr da rashin yin posting in time ' duk da dai dama banyi muku alk'awarin zaku ruk'a samu kullun ba kasancewar nima inada abunyi!!! And then Aisha Inaso ki gane cewa bazan mayar miki da martani ba har saikin je kin koyi yadda ake magana tukunna..._*

_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_

*Follow me on wattpad @Seemaluv1*

[12/2, 6:26 AM] 0mmer Farouk: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*

*_@Been in love ' is something special, Ever since I meet you Samra ' my heart keeps telling me that you are the right person to be with 💋,You are my Sweetheart♥ ' my lollipopty. This page is yours kawai..._*

_And for you my Besty(Jameesha), Am very sorry, you know I heart you ♥, so inasonku both._

*32-33*
Chapter 15 · 0% Book details