← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari...
*AROUND 6:00AM*
Safna ta tashi ' bayan tayi sallah ta fito ta fara kinkintsa gida, Tana cikin shara ne Umma ta fito daga d'aki nan Safna ta zuk'unna har k'asa ta gaisheta, Sannan ta mik'e tsaye.
"A'a bar sharar nan ' kije kija ruwa a rijiya kiyi wanka don ki tafi da wuri, Sai Rumaisa tayi sharan."
"Uhum."
Aje tsintsiyar tayi, Sannan taje taja ruwa ta nufi bayi dashi.
Koda ta fito daga wanka ta iske Umma tana shirin dama koko ' haka Safna ta wuce d'aki ta hau shafa mai da powder cikin sauri.
Bayan ta gama ne ta d'auko hijab d'inta pink color da atamfa mai ratsin pink, Duk da kayan sun kod'e hakan bai hanata yin shiga ta mutunci ba.
Safna tsakar gida ta fito ' ta nufi wajen Umma ' Umma ta zuba mata koko, Sannan ta karb'a ta shanye ba tareda ansa sugar ba.
"To Umma nizan wuce."
"Allah ya tsare ' Allah kuma yasa asami abunda akaje nema."
Amin Safna tace, Sannan tasa takalminta ta fice.

*DEDICATED TO MY LOVELY FAN'S*
😚😚😚
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

© ```Written```      
By
*_Seemaluv_*👄

*_@Kamar yadda nasami k'orafin readers da dama akan rashin k'arashe B'OYAYYEN AL'AMARI da banyi ba, To Alhamdulillah yanzu dai na aje wancen na kuma cigaba da wannan...._*

*10-11*

Safna na fita bata wani wasting time ba ' ta tari mai keke-napep ta shiga, Tukunna taimashin kwatancen inda zai kaita.
Bata isa company d'in ba sai wajen k'arfe *8:00am*, Haka ta mik'awa mai keke-napep kud'insa ya wuce ' ita kuma ta shige cikin company d'in da takaddar ta Kamal yace ta dawo da ita a hannu.
Dai dai bakin k'ofar shiga security ya tsare ta.
"Kina da buk'atar taimako ne?."
Ya fad'a cikin harshen turanci.
"Yes."
Nan Safna ta mik'a masa Application letter d'in ya karance ta tsaf.
"Sir Kamal ya baki ko?."
"Eh."
"Ok barima inkaiki har Office d'in nasa."
Haka Safna tabi bayan security man d'in, Har saida ya shigar da ita office d'in tukunna ya juya yayi tafiyarsa.
A zaune Safna ta iske Kamal ' tare da laptop a gaban shi.
Jayo attention d'inshi tayi da cewa.
"Good morning, Sir!."
A hankali Kamal ya d'ago kai ya kalleta da manyan idanun shi, Ganin itace yasa shi rufe laptop d'in gami da calming hands d'in shi.
"Have a seat!."
Abunda yacewa Safna kenan ' ta sami waje ta zauna, Tukunna ya kafeta da ido.
"I have been expecting you!."
Nan tad'an sunkuyar da kai alaman ladabi.
Nan ya d'aga waya ya kira messenger d'inshi.
Cikin hanzari messenger ya shigo cikin office ' cike da ladabi.
"Sir! Gani."
"Yes, Inaso ka kaita inda ake screening coffee makers."
"Ok."
Haka Safna ta tashi jiki a sanyaye tabi bayan messenger d'in, Har sunkai bakin k'ofa ya tsaidai ita da cewa.
"Be praying."
Uhum, Kawai Safna tace suka fice daga wajen ' wani waje suka shiga an k'ayatashi da kujeru yadda kasan parlor komai pink colour yayi kyau sosai, Ita dai kalle kallenta kawai takeyi bata ankara ba taji ance.
"Madam, Ki sami waje ki zauna."
Inji Messenger.
Saida ya tabbatar ta zauna ' sannan ya juya yabar wajen.
Bayan ta zauna ne ta ankara da mutanen da ke zazzaune a wajen, Mata ne dukkansu ' sunci kwalliya sunci gyale wasuma babu ko gyalen a jikinsu, Daka gansu kaga 'ya'yan manya.
Cikin 'yan lokuta k'alilan aka kawowa kowanen su cup&spoon da ingredients d'in da zasuyi amfani dashi wajen making coffe d'in.
Nan Safna taji wata murya tace "start!".
Kasancewar bata tab'a had'awa ba hakan yasa ta fara kallon yadda ta kusa da ita keyi, Cikin hikima Safna ta fara making coffee har ta gama ' sannan taji ansake cewa.
"Your time is off! Young ladies."
Mr-Fauzan yayi maganar in slangs.
Nan ne Safna ta d'ago kanta domin taga inda maganar ke fitowa, Hakan yayi daidai da juyowar Mr-Fauzan wanda yake zaune a saman kujerar shi ' nan sukayi ido hudu da Safna.
"Subhanallahi! Wannan bashine wanda nabige shi ' a bisa rashin sani ba?."
Tayi tamabayar a cikin zuciyar ta.
Nan take zufa ta fara karyo mata.
Shi kuwa Mr-Fauzan tunda ya fahimci Safna cike take da tsoro yasaki wani irin murmushin da baikai zuci ba.
Nan ya umarce su ' da kowaccen su ta kawo mashi coffee d'inda ta had'a yayi tasting, Haka sukaita tashi suna kaiwa yana tasting kuma yana rubuta masu score.
Safna ganin an kusa kaiwa kanta ne yasa ' ta fara addu'o'i, Tana gama rufe baki line d'in ya kawo kanta ' nan ta tashi cikin sauri rik'e da cup d'inta ta nufi wajen shi.
Mr-Fauzan ko kallon ta beyiba ya karb'a yayi tasting ya rubuta mata score d'inta, Sannan ta juya ta koma ta zauna.
*After some minutes* ya tashi ya koma office d'inshi, messenger na biye dashi, Bayan Mr-Fauzan ya zauna ne messenger yace.
"Sir, akwai wani aike ne?."
"A'a babu, Zaka iya fita."
Bayan fitar shine ' Mr-Fauzan ya d'aga waya ya kira P.A Kamal, Ringing d'aya zuwa biyu tayi ya d'auka.
"Sir?."
"Kamal, Kazo yanzu."
"Ok."
Abunda Kamal ya fad'a kenan Mr-Fauzan ya kashe wayar.
Cikin 'yan lokuta k'alilan Kamal ya shigo cikin Office d'in Mr-Fauzan, Bayan ya zauna ne Mr-Fauzan ya mik'o mashi paper tare da cewa.
"Kamal, inaso kaje kasa a nuna ma Safna Habib and Muneeba Imran yanayin aikinsu ' sauran kuma a sallamesu because they are not qualified."
"Ok."
Abunda Kamal yace kenan ' sannan ya juya yabar wajen, Jin sunan Safna a ciki abun yasa shi farinciki matuk'a.
Kamal hole d'in ya shiga da kansa, Nan yayi calling attention d'in ko wacce a wajen.
Kamal ' hak'uri ya fara bama wad'anda basu sami aikin ba, Ita kuwa Safna babu abinda gabanta keyi inba fad'uwa ba.
Bayan ya gama dogon bayanin shine ' ya kira sunan Safna da Muneeba tare da cewa.
"Safna Habib da Muneeba Imran, Su kad'ai ne aka d'auka amatsayin Coffee makers."
Safna mik'ewa tayi cikin jin dad'i tana murmushi, Don kuwa samun aikinta shine burinta na farko daya fara cika.
Kamal ganin yadda hole d'in ya hargitse ne ' yasa shi komawa Office tare da kiran messenger d'inshi a waya cewa.
"Kaje cikin hole d'in nan, Ka zomun da Safna Habib da kuma Muneeba Imran."
To kawai d'an aiken(messenger) yace, Sannan Kamal ya kashe wayar shi.
B'angaren Safna kuwa! Ai baki har kunne, Nan take ta fara neman Muneeba gami da kwala mata kira.
"Muneeba Habib!."
Muneeba kuwa jin yadda aketa kiran sunan tane yasata juyowa a tsorace' cikin sa'a kuwa sukayi ido biyu.
"Lafiya kiketa kiran sunana?."
"Lafiya kalau ' Muneeba nice Safna Habib, Ina fata zamu had'a kanmu domin muyi aiki tare."
Muneeba tab'e baki tayi cike da downgrading ta juya tacigaba da harkar gabanta, Ba tare da tacewa Safna komai ba.
Safna ganin haka ne yasa ta koma ta zauna ' jiki a sanyaye taci gaba da k'arewa mutanen da ke wajen kallo.

©Seemaluv_Novels 📚📚
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```      
By
*_Seemaluv_*👄

*_Ina dai sake bama Fan's d'ina hak'uri , Masu bin Novel d'ina ' Ayyuka ne sukai yawa..._*

*12-13*
Chapter 4 · 0% Book details