← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Hafiz yazo gidansu Mr-Fauzan tare dayin packing motar shi a packing space, Sannan ya ciro waya yayi dialing number d'inshi.
Mr-Fauzan na zaune a garden d'inshi yaga shigowar kiran Hafiz cikin wayar shi, Nan yayi receiving call gamida karawa a kunne.
"Ya! Kaifa gani na k'araso cikin gidanku yanzu."
"OK, just give me 5minutes ' gani nan fitowa."
Mr-Fauzan cikin gida ya shiga ' direct ya wuce d'akin shi ya bud'e side drower ya d'auko bandir d'in y'an dubu sababbi fil, Ya fito wajen dashi a hannu.
Bayan ya isa wajen Hafiz ne suka gaisa ' tukunna ya mik'a mashi kud'in tare da cewa.
"Behave well!."
"OK."
Abunda Hafiz yace kenan, Ya shige motar shi yaja ' ya wuce, Sannan Mr-Fauzan ya juya ya koma gida.
Koda ya shiga gida kai tsaye ya wuce part d'insu Mummy, Bayan sun gaisa ne Mummy tace.
"Son? Kunfara magana da Nafee kuwa?."
"Oh Mummy come on! Nifa bazan auri wannan ' mara tarbiyar ba."
Cewar Mr-Fauzan.
Mummy zaro ido tayi cike da mamaki and at the same time tare da nuna b'acin ranta.
"What!!! Son? Yarinyar k'awar tawa ce mara tarbiyya?."
Mr-Fauzan sunkuyar dakai yayi ' gami da nuna ko a jikinsa.
"OK! Lallai zan sanar ma Daddynku bari ya tashi bacci, Tunda ni bakajin magana ta yanzu."
Mr-Fauzan tashi yayi yawuce ' Mummy ta bishi da kallo, Kai tsaye ya nufi kitchen ya bud'e fridge ya d'auki yoghurt domin kuwa yunwa yakeji ' kasancewar baiyi breakfast ba.
Mr-Fauzan harya d'auko ya juyo zai bari kitchen d'in suka had'e da Nafee itama zata shigo kitchen d'in.
Wata fitinanniyar rigar bacci ne a jikinta ' wacce take iyakarta gwiwa gata armless, Mr-Fauzan tunda ya kalleta sau d'aya ya d'auke kanshi daga kallonta zai wuce ' ta tsaida da cewa.
"Good morning ' Sweetheart."
"Morning."
Ya fad'a yana tafiya bata tare daya juyo ya kalleta.
Ganin haka yasa Nafee yin smiling gamida girgiza ' tace.
"Zakazo hannu."
Abunda tace kenan ' ta k'arasa cikin kitchen d'in itama ta d'auki yoghurt ta nufi bedroom d'in Mr-Fauzan dashi.
Nafee shiga tayi ba tare da tayi knocking ko sallama ba, A zaune ta iske Mr-Fauzan rik'e da yoghurt hannu d'ayan hannun kuma yana danna laptop dashi.
Mr-Fauzan tsayawa yayi yana kallon ta ' daga bisani kuma ya kauda kanshi, Tare da cewa.
"Get out of my room! Now."
Ya fad'a a uzulce.
"Why?."
Tayi tambayar tana k'arasowa tsakiyar d'akin.
Ganin haka yasa Mr-fauzan mik'ewa tsaye cikin b'acin rai.
"Don't you dare come near me!."
"Meyasa bazaka bi umurnin Mummy ba? Meye aibuna?."
Mr-fauzan ganin zata b'ata mashi lokaci ne yasa shi fizgota suka nufi bakin k'ofar.
"Get out! And be out of my life forever."
Yana gama fad'in haka ya bud'e kofar ya tunkud'a ta waje, Sannan ya rufe k'ofar shi ya koma ya zauna.
Nafee juyawa tayi ta koma d'aki tana dannan hannun ta inda ya rik'eta, Ba k'aramin zafi wajen ke mata ba.
"Dole sai na gasa wajen."
Abunda nafi tace kenan ' ta tashi ta cire rigar baccin jikin ta ta d'aura towel, Sannan ta shige bathroom.

_we don't just entertain and educated, But we also touch the hearts of the readers_

*Follow me on wattpad @Seemaluv1*
[12/1, 7:44 PM] ‪+234 703 270 1670‬: *....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*

*28-29*
Chapter 13 · 0% Book details