Sashe 23
Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mr-Fauzan juyowa yayi ya kalli Safna tare da cewa.
"Muje."
"Ni babu inda zanje, Don Allah ka maida ni inda ka d'auko ni."
"I don't want to argue with you Safna, Don't forget akwai yarjejeniya tsakanin mu, Kar kuma ki manta da Mahaifiyar ki dake hospital ba lafiya."
Safna sunkuyar da kanta tayi tana nazari, Sannan Mr-Fauzan ya cigaba da cewa.
"Sabida haka ya zama dole kibi abinda nace, Because I can change my mind at any time."
"Saboda kana azzalumi? Meyasa ku masu kud'i bakwayin abu tsakani da Allah?."
Safna maganar cikin rawar murya.
"Daki aure ni Mahaifiyar ki ta warke, Da kik'i amincewa kuma ta mutu wane kika zab'a?."
Mr-Fauzan ya fad'i haka ba tare da ya kalle ta ba.
"Wai kai wane irin azzalumi ne? Wane irin mugu ne kai? Meyasa bakwa taimako tsakani da Allah?."
"Why? I thought ke kina da tarbiyyar da zaki iya sadaukawar Mahaifiyar ki farin cikin ki."
Mr-Fauzan ya fad'i haka tare da jan tsuki, Sannan ya k'ara da cewa.
"Let me just call the doctor ' na fad'a mashi cewa nina cire hannuna game da mahaifiyar ki."
Ya fad'a tare da d'aga wayar shi zaiyi dialing number d'in Doctor, Safna saurin dakatar dashi tayi da cewa.
"A'a Don Allah... Kar kayi haka...Kayi hak'uri naji na amince zanbi duk abinda tace."
Ta fad'i haka hawaye na gangaro mata saman fuskar.
Mr-Fauzan handkerchief ya mik'a ma Safna domin ta share hawayen dake fuskar ta, Haka ta karb'a ta share cike da takaici.
"Kuma as from today ' inaso ki adana hawayen ki, Because am not bullying you."
Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan ya bud'e mota ya fita.
Safna itama budewa tayi ta fito, Wani babban shop suka shiga wanda ya k'unshi komai da komai.
Bayan shigar sune Mr-Fauzan ya nufi b'angaren Abayas Safna na biye dashi a baya.
Safna tsayawa tayi wajen wata Abaya mai kyau, Ganin haka yasa Mr-Fauzan tsayawa ya duba kud'in Abayan da Safna ke kallo.
"So cheap."
Ya fad'a gami da kamo hannun ta yaja ta suka k'arasa ciki.
Mr-Fauzan bai tsaya ko ina ba sai a wajen wasu Abayas masu kyau wanda daka gansu kaga kud'i.
Safna k'ok'arin raba hannun ta take da nashi amma ta kasa.
Mr-Fauzan kuwa Abayas kawai yake jida, Yana sakawa cikin basket.
Suna cikin hakanne Suhailah ta shigo cikin shop d'in, Itama wajen Abayas d'in taje tana zab'ar wanda yai mata.
Suhaila hango Mr-Fauzan tayi rik'e da hannun Safna yasa ta aje basket d'in nan wajen ta nufi inda yake.
Mr-Fauzan kuwa tunda suka had'a ido da Suhailah yasa ke rik'e hannun Safna sosai.
"Fauzan?."
Suhailah ta ambaci sunan shi cikin mamaki.
Mr-Fauzan juyowa yayi ya kalle ta, Safna kuwa k'ok'arin ta shine taga ta raba hannun ta da nashi.
"Who is she?."
Tayi tambayar tana yi mashi nuni da Safna.
"She's my wife to be."
Ya furta with proud.
Suhailah zaro ido tayi gami da k'arewa Safna kallo, Ganin haka yasa Safna sunkuyar da kai.
Nan Suhailah ta matsa kusa da Safna tare da fincikar hijab d'in gami da cewa.
"Wannan abun ce kakeso ka aura Fauzan? Dame ta fini?."
Mr-Fauzan kab'ewa Suhailah hannu yayi tare da yi mata kasheda yace.
"Don't try something stupid here Suhailah, And i advise you to leave us alone...!!' kafin ki raina kanki a wajen nan!."
"Fauzan abinda zakace kenan? Ni kake fad'awa haka akan wannan k'azamar?."
Suhailah ta fad'i haka cike da tsirawa Safna hannu.
Mr-Fauzan tsuki yaja suka bar wajen.
"What! Ni Fauzan zaima haka? Ni zai yaudara? Ni zai ciwa fuska sabida wannan abin? Lallai zan nuna mishi kad'an daga cikin aikin Suhailah."
Abinda Suhailah ta fad'a kenan tare da karkad'a kanta ta koma wajen inda take zab'an Abayas.
A wajen mai karb'ar kud'i Mr-Fauzan ya tsaya, Ciro wallet d'in shi yayi ya zari ATM card d'in shi ya mika musu domin su cire kud'in su.
Tunda suka tsaya wajen Safna ke kallon Mr-Fauzan jikin ta a sanyaye.
"Sona kake da gaske ko kuwa?."
Ta fad'i haka cikin ranta.
Tana cikin wannan tunanin ne taji ya jata sun nufi wajen k'ofar fita.
Fita sukayi daga cikin shop d'in, Mr-Fauzan saida suka isa wajen mota tukunna ya sakar mata hannu.
Key ya sanya ya bud'e motar, Sannan ya saka kayan cikin bode ya koma cikin mota ya zauna, Tukunna itama ta bud'e front seat ta shiga ta zauna.
Mr-Fauzan tada motar yayi suka nufi hospital domin maida ta.
Mr-Fauzan driving d'in shi kawai yakeyi Safna na satar kallon shi.
Tabbas Mr-Fauzan kyakkyawa ne kuma ya cancanci duk wata mace ta kalle shi ta yaba.
Cikin 'yan mintoci suka isa cikin hospital d'in, Bayan yayi parking ne ya danna wani waje cikin motar hakan yasa bode ya bud'e.
"Kije ki cire kayan ki."
Ya fad'a cike da tak'ama ba tare da ya kalle ta ba.
"Na gode."
Safna ta fad'a, Sannan ta bud'e motar ta fito.
Safna wajen bode ta zagaya ta d'aga ' ta d'auki ledar kayan, Sannan ta rufe bode d'in.
Nan Mr-Fauzan yaja motarshi ya wuce.
Safna koda ta shiga cikin hospital d'in cikin ward ta wuce kai tsaye.
'Yan uwan su Umma ta iske a ciki hakan yasa gaban ta ya fad'i.
Da sauri Safna ta k'arasa ciki, Ganin yadda su Rumaisa ke kuka ne yasa nan take k'afafun Safna suka fara rawa.
Anisah ce ta taso ta rungume Safna cikin kuka tace.
"Aunty Safna, Likita yace wai Umma ta rasu..."
Raras gaban Safna ya sake fad'uwa, Nan take idanuwanta suka ciko da hawaye.
Safna maida kallon ta tayi ga mutanen da ke tsaye a wajen, Ganin yadda suke girgiza kai alaman tausayawa ne yasa Safna ta matsa wajen gadon Umma.
Safna ganin an rufe Umma da farin k'yalle ne yasa ta zubewa k'asa, Cikin kuka take cewa.
"Umma don Allah ki tashi...karki mana haka... Umma ki tashi don Allah."
Safna ta k'arashe maganar cikin kuka.
Rumaisa tasowa tayi tazo kusa da Safna ta tsaya gami da dafa kafad'an ta.
Hakan yasa Safna d'ago kai ta kalle ta.
"Rumaisa meyafaru da Umma haka?.".
Tayi maganar cikin disashewar murya.
Rumaisa share hawayen da ke mata zarya tayi tace.
"Lokacin da kika fitane ciwon ta ya tashi harta kaiga yin kashin jini, Shine na fita na kira likita, Koda yazo ya duba ta sai kawai naga ya rufe mata fuska yace in kira 'yan uwanmu, Shine na d'auki kud'i naje na kira su Goggo mariya."
Da sauri Safna ta rungume Rumaisa cikin matsanancin kuka.
Goggo Mariya ce ta taso tazo inda Safna take.
"Kiyi hak'uri Safna ki kuma d'auki k'addara."
Cewar Goggo Mariya.
Goggo Mariya k'anwa ce ga Umma.
Wani ne ya shigo ya cikin ward d'in tare a cewa.
"Ga motar cen an kawo."
Abinda ya fad'a kenan ya shigo ciki tare da Nurses guda biyu suka d'auki gawar Umma suka d'aura ta a trolley chair, Suka nufi wajen mota da ita.
Safna dasu Rumaisa kuka kawai sukeyi har suka shiga cikin mota, Aka sanya gawar Umma a baya.
'Yan uwan Umma suma shiga suka yi cikin motar, Kasancewar boss ce motar shiyasa ta d'auke su gaba d'aya..
*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS.*
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*
*_UNIQUE WRITERS ASSOCIATION_*
® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*
https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/
*_@Dedicated to SEEMALUV NOVELS GROUP & B'OYAYYEN AL'AMARI FANS GROUP,,,,,,,,,Masoya na ina ganin sak'on nin ku ' Seemaluv really appreciate it._*
*44-45*
Koda su Safna suka isa gida kafin kace kwabo gidan ya cika da mutane, K'ofar gidan kuwa cike yake da maza.
Bayan anyiwa gawar wanka ne, Safna tana ji tana gani aka d'auki gawar aka fita a ita domin yi mata sallah, Daga nan akaita masaukin ta.
“Wayyo Allah na shiga uku... Ni yanzu yazan kasance da k'annai na?.”
Safna dake zaune cikin hijab ta fad'i haka cikin matsanancin kuka.
Goggo Mariya ce, Ta taso tazo inda Safna take tace.
“Haba Safna meyasa bazakiyi tawakkali ba? Meyasa? Karfa ki manta duk mai rai mamaci ne, Kuma ai Allah yana tare daku.”
Haka duk mutanen dake wajen suka dunga lallashin Safna.
*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***
*AROUND 5:00PM*