← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 27

Sashe 7

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

B'angaren Mr-Fauzan, Zaune yake a d'akin shi rik'e da pen a hannun shi, Yana duba documents.
Bayan ya kammala ne ya tashi ya wuce garden ' inda yake hutawa ya same waje ya zauna, Yana nazarin ayyukan dake k'unshe cikin company d'inshi.
Yana cikin haka ne Safna ta fad'o mashi a rai, Yana tuna da irin wulak'ancin da yayi mata.
"But i see passion in her eyes!, Tana k'unshe da wasu abubuwa ' dana kasa gane meye su!."
Abunda Mr-Fauzan ya furta kenan a fili, Sam baisan Mummy na tsaye a bayan shiba ' sai ji yayi tace.
"Son?."
A razane ya juyo ya kalleta, sannan ta sami waje ta zauna d'auke da murmushi a fuskarta.
"Son! Wacece wannan wacce naji kana maganar ta?."
"Mummy wa kikaji ina maganar ta?."
"Yakamata ka kawo man ita ' ta gaisheni."
"Mummy ' nifa bakiji da kyau bane."
Mummy b'ata rai tayi tare da nuna fushin ta fili.
"Fauzan! Karka sake ka k'ure ni, Don kuwa inhar ka bari raina ya b'aci game da maganar nan to tabbas zan aura maka wacce baka so!!!."
Mummy na gama fad'in haka ta tashi ta koma cikin gida, Shi kuwa Mr-Fauzan in ranshi yayi dubu ya b'aci, Don kuwa babu abinda ya tsana irin auren had'i.
"I really have to do something!, Dole in nemi mafita."
Abunda yace kenan ' ya tashi ya wuce part d'in shi shima.

*SEEMALUV NOVELS GROUP*📚
*FACEBOOK @SEEMALUV HAUSA NOVELS*

*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```      
By
*_Seemaluv_*👄

Follow me on wattpad @Seemaluv1

*18-19*

Safna kuwa tunda ta dawo ta shige d'aki, Sam babu walwala a tattare da ita ' Umma ta lura da haka, Hakan yasa ta tashi tabi Safna d'aki ta iske ta a kwance saman gado tayi ruf da ciki.
"Safna?."
Jin ankira sunanta ne yasa ta tashi ta zauna ' tare da cewa.
"Na'am Umma!."
Umma bakin gado ta zauna ' daidai saitin Safna.
"Na lura dake tunda kika dawo ' sam babu walwala a fuskar ki, Kuma baki fad'amun komai game da aikin kiba ' ince dai babu wata matsala ko?."
"Eh babu komai Umma, Aiki kuma Alhamdulillah nasamu."
Safna na gama fad'in haka ta koma ta kwanta.
"Ha'a ya ina magana kin koma kin kwanta, Safna akwai abunda ke damunki fa."
Safna sake tashi tayi ta zauna cike da damuwa, Tace.
"Umma karki damu ' kawai wasu 'yan matsala dana fuskanta yau, Amma babu komai."
"To Allah ya k'ara tsarewa."
"Amin."
Har Umma ta tashi zata fita Safna ta tsaida ita ' da cewa.
"Umma abinci na fa? Yunwa nakeji wallahi."
"Abincin ki ' gayacen a kwano ki d'auka."
Umma taiwa Safna nuni da wani kwano ' dake a k'asa a gefen gado tukunna ta fice, Cikin sanyi jiki Safna ta sauko daga saman gadon ta d'auki abincin ta fara ci da sauri.
Bayan ta gama ne ta fito daga d'akin ta iske Rumaisa da Anisa zaune saman ta barma Umma kuma na zaune a saman turmi tana gyara shinkafa.
Safna bakin rijiya ta nufa ta wanke hannunta ' Sannan ta dawo ta zauna cikin su Rumaisa.
"Umma, Me za'a dafa ne da yamman nan?."
"Gashi kuwa ina gyarawa shinkafa!."
"Yauma shinkafa da mai da yaji?."
"Eh."
Ajiyar zuciya kawai Safna tayi, Sannan ta tashi ta nufi bakin murhu ta hau had'a wuta domin d'aura ruwan zafi.

*AROUND 6:00PM*

Mr-Fauzan na zaune a babban parlor Khairat ta sauko daga saman steps ' tazo ta zauna a parlon rik'e da popcorn a hannunta tana ci.
"Ehen! Bani pop-corn d'in nan inci."
"Haba Yaya don Allah! Bafa shida yawa."
Ta fad'a tana turo baki, Ganin haka yasa shi fizge ledar popcorn d'in gaba d'aya tare da cewa.
"Ni kike turowa baki ko? To aisai kici ingani."
"To nida abuna?."
"Yes!!! Ke da abun naki ' na hanaki."
Khairat ganin baida niyyar bata ne ' yasa ta barin parlon cikin gunguni.
Mr-Fauzan kuwa cin pop-corn yakeyi yana kallon news, Yana cikin haka ne maganar Mummy ta fad'o mashi a rai ' hakan yasa shiyin zambur ya mik'e tsaye tare da dailing number d'in babban abokin shi mai suna Hafiz.
Ringing d'aya zuwa biyu wayar tayi Hafiz ya d'auka.
"Hello Hafiz?."
"Babban mutum! Ya akayi ne?."
"Where are you?."
"Am at home now."
"Good! Hafiz i really need your help, Ya za'ayi inganka?."
Cewar Mr-Fauzan.
"Kazo gida kawai ' sai muyi magana."
OK kawai Mr-Fauzan yace, Sannan ya kashe wayar ya fita zuwa garege ' ya shiga motar shi, Ganin haka yasa mai gadi yin saurin bud'e gate tukunna Mr-Fauzan yaja motar shi ya fice.
Hafiz kuwa tunda suka gama waya da Mr-Fauzan ' yaje part d'in hajiya wato mahaifiyar sa ya sanar mata da cewa babban abokin shi zaizo, Hakan yasa Aleeza wato k'anwarsa yin saurin shiga kitchen ita da 'yar aiki suka fara preparing abinci.
"Wayyo Allah! Dama yace yana sona."
Cewar Aleeza.
"Amma wai daman bak'on kine ko kuwa bak'on Yayan ki?."
Inji 'yar aiki.
"Nidai banason surutu! Kiyi abunda na saki."
Aleeza barin kitchen d'in tayi ta wuce parlor inda Hafiz ke zaune, Ta zauna.
"Yaya Hafiz, Haryanzu abokin naka bai iso bane?."
Hafiz d'aure fuska yayi, Tare da cewa.
"Kinada sak'on da zaki bashi ne?."
"A'a kawai dai na matsune ingansa, Saboda inajin labarin sa ' Allah Yaya guy d'in..."
Bata kaiga k'arasawa ba Hafiz ya daka mata tsawa da cewa.
"Ke! Don Allah kin isheni da surutu, Inma sonsa kikeyi gwara kin cireshi a ranki ' don ba ajinki bane."
Aleeza tashi tayi ta wuce part d'in hajiya tana gunguni.
Aleeza kyakkyawar yarinyace 'yar shekara 19 tana, Cikin wannan year d'in zata gama school d'inta na fannin jami'a.
Hafiz na cikin danna wayar shine yaji tsayawar mota ' a cikin garege, Hakan ya tabbatar mashi da cewa Mr-Fauzan ne.
Hafiz tashi yayi taje ya shigo dashi cikin gidan ' tare da yimashi maraba, Sannan Mr-Fauzan ya nemi waje ya zauna.
"First bari in kira hajiyata ku gaisa, Tunda ka dad'e rabonka da gidan nan."
Cewar Hafiz.
Hafiz wuce part d'in hajiya yayi ya sanar da ita cewa abokin nasa ya iso, Saboda haka ta fito su gaisa.
Hafiza da hajiya tare suka fito zuwa parlor sai kuma Aleeza dake binsu a baya, Koda suka isa parlor Aleeza bata k'arasa wajen ba ' saidai ta rakub'e jikin bango tana lek'en Mr-Fauzan har suka gama gaisawa da Hajiya ta koma part d'inta.
"Wayyo... Allah na! Jibeshi cikin fararen kaya, Wallahi guy d'in nan ya riga ya lashe zuciyata inason shi."
Abunda Aleeza ta fad'a kenan tare da dafe k'irjinta tana sauke ajiyar zuciya, Tukunna ta juya ta nufi kitchen ta iske 'yar aikin sai kai da komowa takeyi.
"Oh my God! Yanzu baki gama abincin ba?."
"Eh, Kiyi hak'uri kinsan halin shinkafa."
Girgiza kai kawai tayi gamida jan tsaki, Sannan ta d'auri trey ta bud'e fridge ta had'a drinks kala kala, Sannan ta d'auka ta nufo parlor d'in dashi a hannu.
Koda Aleeza ta doso parlon idonta na kanshi, Haka ta k'arasa ciki da sallama a bakinta ' dukkansu suka amsa, Sannan Aleeza ta ajiye trey d'in a k'asa daidai saitin Mr-Fauzan.
"Sannu da isowa!."
"Yawwa."
Abunda ya fad'a kenan ba tare da ya d'ago kai ya kalleta, Hakan yasa ran Aleeza ya b'aci ta juya ta wuce tamkar zatayi kuka.
Bayan wucewar tane Mr-Fauzan yace.
"Ehem! Hafiz nazo wajenka akan wata magana ne."
"Fad'amun inajinka."
Nan Mr-Fauzan ya gyara zama, Tare da yin gyaran murya.
"Wato Mummy ce ' take nema ta huramun wuta! Akan lallai saina kawo mata wacce zan aure."
"Fauzan, To meye aciki? Ai kawai malam kayi aure musha biki."
"No please! Ka daina zaulaya! This is a serious issue, Babu matar ne ai."
"Kamarya? Kana nufin duk 'yan matan dake sonka babu wacce taimaka?."
Mr-Fauzan d'an k'aramin tsaki yaja.
"Is ok! I understand your pain, Ya kamata mu sami lokaci mu fitane ' domin kaga wacce taimaka."
Nan Mr-Fauzan yayi saurin taron numfashin Hafiz, Da cewa.
"Ehen! And ita Mummy ta nace dole sai 'yar gidan masu kud'i, And to tell you the truth? Ni gaskiya bazan auri yarinya tazo tana raina ni ba, Su suna da raini ne."
"Eh kwarai haka ne ' suna da wannan, Yanzu dai you know what?."
Mr-Fauzan ya girgiza kai alaman a'a.
"Insha Allah zan zauna ' inyi tunani domin muyi finding solution, Gobe kuma zanzo company d'inka sai a tsayar da magana."
Mr-Fauzan dad'i yaji sosai, Sannan ya mik'awa Hafiz hannu alaman gaisuwa.
"Gaskiya na gode sosai Abokina da time d'inka."
Cewar Mr-Fauzan.
Haka suka tashi ' Mr-Fauzan yayiwa Hafiza sallama, Sannan ya fita ya shige motar shi yaja ya wuce.

*SEEMALUV NOVELS GROUPS*📚
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv_*👄

Follow me on wattpad @Seemaluv1

*_Kuyi hak'uri jina da kukayi shuru! Na d'anyi fama da ciwon kai ne shiyasa INASON KU MASOYA NA, i love you too JAMEESHA Wannan page d'in naki ne ke kad'ai..._*

*20-21*

Bayan Mr-Fauzan ya dawo gida ne, Yayi packing motar shi tukunna ya shige cikin gida ' kasancewar bai sami kowa a parlor bane yasa shi wucewa kitchen kai tsaye domin ya zuba abinci.
Koda Mr-Fauzan ya shiga kitchen d'in 'yar aiki ya iske tana ta k'okarin kammala abincin.
"Haba! Me akeyi since ' ba'a gama ba?."
Cewar Mr-Fauzan.
"Kayi hak'uri an kusa gama wa."
'Yar aikin ta fad'a tana k'okarin duk'awa k'asa.
Mr-Fauzan juyawa yayi ya wuce part d'in, Yayi wanka tukunna yayo alwala kasancewar baiyi sallar isha'i ba.
Bayan ya fito daga bathroom ne ya bud'e wardrop d'in kayan shi, Ya ciro jallabiya ya sanya ' sannan ya shinfid'a dadduma yayi sallar sa.

*AROUND 9:00PM*
Chapter 7 · 0% Book details