← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Safna na kwance a d'aki saman tabarma, Umma da Anisa da Rumaisa kuma suna saman gado suna ' ko wannen su yayi shuru yana tunanin zuci.
"Yaya Safna? Ranar bikin ki ba k'aramin casu za'ayi ba."
Inji Rumaisa.
"Hmm... Lallai Rumaisa zuciyar ki tana fad'a miki k'arya, To Allah dai ya hore mana."
Amin dukkan su sukace ' sannan Umma tayi gyaran murya, Tace.
"Yaro yaro ne ' inbanda abunku, Ai walima tafi rufin asiri ' Allah dai ya baku mazaje na gari."
Amin Safna da Rumaisa suka ce.
"Umma halan Anisa bacci tayi ne, Najita tsit ne."
Cewar Safna.
"Tab wannan ai tunda taji cikin ta ya d'auka shikenan!."
Haka su Safna sukaita fira har bacci yayi awon gaba dasu.

*** *** *** *** *** *** ***

Washe gari da sassafe ' wajen k'arfe *7:00am* Umma ta tada Safna daga bacci.
"Tashi mana! Kinfa makara, Yanzu bakwai tayi fa."
Safna najin haka tayi wuf ta tashi cikin hanzari ' ta fito daga d'akin ta nufi wajen rijiya taja ruwa a buta, Sannan ta shige bayi.
Bayan fitowar tane ' ta iske Rumaisa a bakin rijiyar zataja ruwa itama.
"Yawwa Rumaisa jamun ruwan wanka ' don inayin sallah zan shiga wanka."
"Da ruwan sanyi?."
"Eh mana! To dame kikeso inyi bayan na makara."
Nan wajen Safna ta zuk'unna tayi alwala a gurguje ta shige d'aki tayo sallah, Sannan ta fito ta.
Safna ruwan wankanta ta d'auka ta nufi bayin, Cikin 'yan lokuta k'alilan ta fito.
Tana fitowa ta iske Umma na dama koko, Hakan yasa Safna shigewa d'aki a tsanake ta shirya ' sannan ta kalli agogo taga wajen k'arfe *7:30am*.
"Ya salaam! Lallai na makara da yawa."
Safna waje ta fito ' ta nufi wajen Umma ta zuk'unna, Umma ta zuba mata kokon ta fara sha ko sugar babu don kuwa idan da sabo aita saba.
Tana kammala wa ta mik'e tsaye tare da cewa.
"Umma ni zan wuce wajen aiki."
"To Safna Allah ubangiji ya tsare."
Amin Safna tace, Sannan ta zarce d'aki ta d'auki hijab ta sanya ta fice, Tana fita ne taga mai keke-napep a tsaye jingine a jikin napep d'inshi a k'ofar gida.
"Bawan Allah lafiya?."
Cewar Safna.
"Kece Safna habib ko?."
Ta d'aga mashi kai gami da cewa.
"Eh."
"Yawwa cewa akayi inzo inruk'a d'aukan ki kullun idan zaki tafi wajen aiki."
Abun ne ya ba Safna mamaki tace.
"Bawan Allah injiwa?."
"Yace in fad'a miki Ogan ki Kamal."
Abun d'aure mata kai yayi, Sai dai tayi murmushi tace.
"To shikenan muje."
Safna shiga tayi shima mai keke-napep d'in ya shiga yaja suka tafi.
*AROUND 8:00AM* Safna ta isa cikin company d'in, tana sauka ta ciro d'ari biyu daga cikin 'yar k'aramar jakarta ta mik'a mashi.
"A'a ai shine zai rik'a biyana duk k'arshen wata."
Safna dafe kai tayi alaman mantuwa, Tace.
"Ya salaam! Kayi hak'uri na manta ne."
Nan ta maida kud'inta ta juya ta nufi cikin company d'in, Koda ta shiga a tsaitsaye ta iske mutanen dake ciki ' Mr-Fauzan sai zabga bala'i yakeyi akan ba'ason zuwa akan lokaci.
Jin haka yasa Safna yin ajiyar zuciya ' acikin zuciyar ta tace.
"Uhp ashe ma bani kad'ai bace ta makara d'in."
Safna hango Muneeba tayi ' hakan yasa ta k'arasa kusa da ita.
"Muneeba wai meke faruwa ne?."
Cewar Safna.
"Hmm. Kinsan halinsa ai ' fad'a yake akan wad'anda basa son zuwa in time, Kuma saida ya tambaye ni ina abokiyar aikina."
Nan take gaban Safna ya fad'a, Tace.
"To me kika ce masa?."
"Ha'a me kuwa zance masa? Zanyi masa k'arya ne saboda in faranta miki?, Ce masa nayi baki ruga kin iso ba."
Nan fa Safna tsoro da fargaba suka bayyana a fuskarta, Mr-Fauzan kuwa ashe ya riga yaga shigowar Safna wajen.
"Where is Safna Habib?."
Mr-Fauzan ya tambaya yana kallon side d'inda take.
Safna salati kawai takeyi a cikin ranta.
"She is here Sir."
Cewar Muneeba.
Safna k'arasawa tayi gabansa tare da cewa.
"Gani."
"Baki karanta rules d'in aikin ki bane?."
Mr-Fauzan yayi maganar cikin tak'ama.
"Na karanta."
"Good! So baki shirya ma aikin bane?."
"Ba haka bane, Wallahi nauyin bac..."
"What?? Nauyin bacci? You are not serious Safna."
"Take it easy Sir."
Cewar Sir-Kamal..
Sai a wannan lokacin ne Safna ta lura da Sir-Kamal a wajen, Ganin sa yasa tayi ajiyar zuciya ' tasan koba komai bazata wulak'anta ba.
"Zaki bama duk wani ma'aikaci dake cikin wannan company d'in Coffee for good 2weeks ba tare da taimakon abokiyar aikin ki ba, Wannan shine punishment d'inki."
Mr-Fauzan ya fad'i haka d'auke da murmushin mugunta, Sannan ya k'ara da cewa.
"Idan kinso zaki iya cigaba dayin nauyin bacci, Zaku iya komawa kan aikin ku."
Ya umarce su, Nan Safna ta juya kowa ya watse ya cigaba da harkar gabansa.
Safna direct store ta nufa ' ta fara had'a coffee tana zubawa a cups tanayi tana kaiwa ma'aikatan dake wajen, Saida ta kammala tukunna ta fara kaiwa office.
Safna office d'in Sir-Kamal nufa, Knocking tayi ya bata iznin shiga ' sannan ta bud'e k'ofar ta shige d'auke da sallama.
Bayan ta aje mashi coffee d'in saman table d'inshi ne suka gaisa, Sannan tace.
"Sir?."
Ya d'ago kai ya kalleta.
"Naga Abun arzik'i naji dad'i kuma nagode, Allah ya saka da alkairi."
"Ki sami waje ki zauna ' first."
Safna zama tayi suna facing juna, Sannan Sir-Kamal yace.
"No need of thanking me Safna, Saboda wannan ai yiwa kaine."
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta.
"Yanzu kije ki cigaba da aikin ki, Idan kin gama saikizo i have a surprise for you."
Ok Safna tace ' ta mik'e d'auke da murmushi a fuskarta, Sannan ta d'auki ragowar Coffee d'in ta nufi Office d'in Mr-Fauzan dashi.
Nan suka had'e da Hafiz abokin Mr-Fauzan yana k'okari shiga cikin Office d'in, Safna tsayawa tayi cak tare da cewa.
"You are welcome."
Hafiz kallonta yayi daga sama har k'asa, Sannan yace.
"Thank you!."
Hafiz bud'e office d'in yayi ya shige tukunna Safna ta biyo shi a baya.
Haka ta shiga da sallama a bakin ta jikin ta na d'ar d'ar.
Bayan Mr-Fauzan da Hafiz sun gaisa ne Safna ta aje musu Coffee two cups a wajen, Ganin yayi bak'o ne yasa ta juyawa zata wuce ba tare data gaishe shi ba ' saboda kar tayi interrupting d'in shi.
Harta kai bakin k'ofa ya daka mata tsawa da cewa.
"Where did you think you're going to?."
Cikin fargaba ta juyo ta kalleshi a sanyaye.
"Sorry Sir."
"Wane irin Sorry Sir, Come on zo nan."
Safna dawowa tayi ' tayi tsaye wajen desk d'inshi, Shi kuwa Hafiz kallon su kawai yakeyi yana murmushi.
"First, Kin kawomin Coffee without sayin anything, Second ' kin juya zaki tafi without greetings, Tarbiyyar da aka koya miki kenan daga gidan ku?."
Nan take hawaye suka zubo daga fuskarta.
"Am sorry Sir!..."
Ta furta cikin rawar murya.
"Calm down mana!, Hak'uri akeyi and she even apologized."
Tsaki Mr-Fauzan yaja cikin b'acin rai yace.
"Leave my office."
A tsawace yayi magana, Hakan yasa Safna juyawa cikin hanzari ta bar Office d'in tana hawaye.
"Haba aboki! Kacika zafin rai da fad'in hash-words."
Cewar Hafiz.
"Yarinyar sam batada alk'ibula ne, P.A nane ya matsa saina d'auke ta aiki ' ita gata k'azama."
Mr-Fauzan ya fad'i haka cikin izza, Hafiz murmushi kawai yayi yad'an tsaya k'are mashi kallo nad'an lokaci.
"Meye haka, Kana kallo na kana smilling."
"Kuma yarinyar nan daga ganinta talakace ko."
"Ehen now!."
Nan Hafiz ya gyara zama ' gamida duba wristwatch d'in hannun shi.
"Ina ganin ' yanzu komai zaizo mana da sauki."
"What do you mean?."
Mr-Fauzan yayi tambayar.
"Ina nufin ita tafi dacewa da kai Abo....."
Hafiz bai kaiga k'arasa maganar sa ba, Mr-Fauzan ya dakatar dashi.
"No please ' karma ka k'arasa please, Hafiz wace irin magana kake fad'amin? Yau kuma da wannan k'azamar zaka had'ani?."
"Ka daiyi tunani akai Fauzan! Ni abokin kane, Kuma bazan tab'a baka gurguwar shawara ba, Batun rashin tsafta kuma ai kaine zaka gyara ta."
"No no no... Mubar maganar nan don bazata sami shiga ba."
"Ok! Then, Ni bara in tafi, Idan kayi tunani akai ' saika nemeni."
Nan Mr-Fauzan da Hafiz sukayi sallama da junan su, Bayan fitar Hafiz ne Mr-Fauzan ya bud'e laptop d'inshi ya fara aiki.

*©SEEMALUV NOVELS GROUP📚*
*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

® ```Written```      
By
*_Seemaluv👄_*

*_Dedicated to Momyn-Sultan and Sadnaf 💁💁,..._*

*22-23*
Chapter 8 · 0% Book details