← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ankaita andawo ne, Mutane suka fara watsewa ya rage daga su Safna sai Goggo Mariya.
“To Safna ki daiyi hak'uri kuma ki cigaba dayi mata addu'a kawai, Kuma kinga irin rayuwar da muke ciki ' yanzu tashi zakiyi da sana'a saboda ki samu ku kare mutuncin kanku.”
Cewar Goggo Mariya.
“Yanzu Goggo Mariya, Bazamu sami tallafi daga wajen ku ba kenan?.”
Safna ta fad'i haka.
Goggo Mariya ajiyar zuciya tayi tare da girgiza kai cike da nuna tausayawa tace.
“Safna kenan! Yanzu wa kike ganin zai baku wani tallafi? Toh ni d'innan kinga nima ba wani hali gareni ba ' sai mijina ya nemo ya kawo, Gani kuma da 'ya'ya ' kuma yanzu masu kud'in nan ba taimako sukeyi ba.”
Safna wasu zafafan hawaye suke kwaranyo mata, Kallon Rumaisa tayi taga babu abinda takeyi sai kuka.
Nan ta maida kallon ta kan Anisah ta ganta rakub'e jikin bango tayi shuru.
“Bakomai Goggo Mariya, Nagode sosai da shawarar ki kuma insha Allah zan nemi aikin yi.”
Nan Goggo Mariya ta tashi sukayi sallama sannan ta wuce.
Bayan anya sallar isha'i ne, Safna da su Rumaisa suna zaune a tsakar gida wani yaro ya shigo tare da yin sallama.
Bayan an amsa masa ne yace.
“Wai ance ana sallama da Safna.”
“Kace gata nan zuwa.”
Cewar Safna.
Yaron juya wa yayi ya fita, Sannan Safna ta tashi ta fita domin duba wanda ke kiran ta.
Safna koda ta fita Ganin Sir-Kamal tayi tsaye, Hakan yasa ta k'arasa inda yake jingine jikin motarshi.
Bayan sun gaisa ne Sir-Kamal yace.
“Safna naje hospital d'in akace min an sallame ku, To yaya jikin Mahaifiyar taki? Anyi mata aikin ne?.”
Safna d'ago kai tayi ta kalli Sir-Kamal tare da cewa.
“Umma Allah yai mata rasuwa d'azu.”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...”
Cewar Sir-Kamal.
Shuru sukayi na d'an lokacin, Sannan Sir-Kamal ya lura da kukan da Safna keyi.
“Kiyi hak'uri Safna, Allah ya gafarta mata Allah kuma yasa hutun kenan.”
“Amin na gode.”
Ta fad'a da disash-shiyar murya.
“To yanzu waye ke zaune daku?.”
“Ba kowa.”
“Toh... Insha Allah idan akayi sadakan uku, Zan dawo domin akwai maganar da nakeso muyi.”
To Safna tace, Sannan Sir-Kamal ya bud'e mota ya ciro abincin da Mr-Fauzan ya umurce shi daya siya masu as usual.
Sir-Kamal mik'awa Safna yayi ta amsa, Sannan yace.
“Inji Mr-Fauzan, Oga na kenan ' yace inkawo muku wannan, Baima san da rasuwar ba shiyasa but zan fad'a mashi idan na koma.”
Nan Safna ta mayar mashi ledar gami da cewa.
“Ka mayar mashi da abincin shi, Domin bama buk'ata.”
“Ha'a Safna meye dalilin yin hakan?.”
“Kamal... Abubuwa da dama sun faru ba tare da saninka ba, Saboda haka kawai abarni inji da mutuwar rasuwar Umma na kad'ai ta ishe ni.”
Ta fad'i haka gami da share hawayen ta.
“Insha Allah Safna komai zaizo maki da sauk'i, Kuma as far as am alive ni zanyi maki komai, Yanzu kuna da abinda zaku ci ne?.”
Kai Safna ta girgiza mashi alaman a'a, Tukunna yace.
“To, Kiyi hak'uri ki ansa wannan kuci, Saboda kada ku kwanta da yunwa.”
“Kada ka damu Kamal, Zan nema mana abinda zamu ci don akwai sauran kud'i a waje na.”
OK kawai Sir-Kamal yace sannan ya maida ledar takeaways d'in cikin mota.
Sir-Kamal dawo wa yayi ya tsaya tare da sanya hannun shi cikin aljihu ya ciro 10k ya mik'awa Safna gami da cewa.
“Kiyi amfani da wannan, Kafin na sake dawo wa.”
Nan Safna ta fashe da kuka, Cike da cewa.
“ hak'uri, Amma ni kunyar ansan kud'in ka nakeyi yanzu, Sabida na kasa karb'ar soyayyar ka.”
Murmushin takaici Sir-Kamal yayi tare da cewa.
“Karki damu Safna, A yau koda ace ban furta miki kalmar so ba ' to zan cigaba da kasancewa inuwa a gareki.”
Safna d'ago kai tayi ta kalle shi cikin shauk'in kuka da sautin shagwab'a tace.
“Da gaske kakeyi?.”
“Uhm.. Da gaske nake mana! Idan har kika bani dama.”
“Na gode.”
Ta fad'a tare da sunkuyar da kanta, Nan sukayi sallama Sir-Kamal ya shige motar shi yaja ya wuce sannan Safna ta shige gida.
Bayan shigar ta gida ne ta iske har Anisah tayi bacci.
“A'a Rumaisa tada Anisah, Babu wanda zaiyi bacci baici abinci ba.”
Safna ta fad'i haka gami da cire hijab d'in jikin ta.
Bayan Rumaisa ta tada Anisah ne Safna tace.
“Indomie zaki je ki siyo mana dafaffa wajen mai shayin cen.”
To Rumaisa tace sannan Safna ta cire d'ari biyar ta mik'a mata tace.
“Kice uku zai dafa maki.”
Kai Rumaisa ta d'aga alaman to, Sannan ta sanya hijab d'inta ta fita.
B'angaren Sir-Kamal, Bayan ya koma gida ne yayi shirin bacci ya kwanta ya d'auki wayar shi yayi dialing number d'in Mr-Fauzan.
Ringing tai tayi bai d'aga ba har sai da Sir-Kamal yayi four missed calls sannan Mr-Fauzan yayi receiving call d'in.
“Good evening Sir.”
“Evening, Any problem?.”
“Well, Yes Sir, Mahaifiyar Safna ce Allah yayi mata rasuwa d'azu.”
Mr-Fauzan a kwance yake amma jin haka yasa shi yin saurin tashi zaune.
“What!! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Why didn't you tell me earlier??.. Meyasa sai yanzu kake fad'amin?.”
“Am sorry Sir, Nima bansani ba sai da naje kai musu abinda zasuci ne ake fad'amun an sallame su shine nabi ta gidan nasu.”
“Ya salaam!...”
Mr-Fauzan ya furta tare da dafe goshin shi.
Mr-Fauzan ending call d'in yayi ya jefar da phone d'in saman gado, Ya fito yana kwala wa Mummy kira.
“Mom! Dad!.”
Mummy da Daddy kwance suke suna bacci, Jin yadda kiran yayi yawa ne yasa Mummy tayi firgigit ta farka.
Parlor ta sauko cikin sauri tana cewa.
“Son what's wrong? Meyafaru?.”
Mr-Fauzan dafe kanshi yayi, Gami da cewa.
“Mom, Yanzu ake fad'amin Mahaifiyar Safna ta rasu.”
“Wacece Safna?.”
“Ita ce wacce zan kawo miki ita gobe, Surukan ki Mom.”
Mummy rufe baki tayi tare da girgiza kai alaman tausayawa.
“Ya salaam!... Allah ya jik'anta.”
Amin Mr-Fauzan yace gamida dafa saman kujera.
“Shit!!.”
Ya furta tare da bugun kujerar.
“Calm down Son, Yanzu kaje ka kwanta gobe sai ayi mata ta'aziyya.”
“I can't sleep at this time Mom... I can't, I know that Safna will never forgive me...”
Mummy tsayawa tayi tana kallon shi cikin mamaki.
“Meyasa? Me kai mata?.”
Mr-Fauzan shuru yayi na d'an lokaci Sannan Mummy tace.
“Kaje dai ka kwanta, Saboda abinda safiya batayi ba dare bazai yi shiba.”
Mr-Fauzan juyawa yayi ya wuce part d'in shi, Mummy girgiza kai kawai tayi itama ta koma b'angaren su ta kwanta.
Mr-Fauzan koda ya kwanta, D'aga kanshi yayi ya duba clock yaga *10:00pm*.
“Huh! Lemme call Hafiz.”
Abinda Mr-Fauzan ya fad'a kenan, Yayi dialing number en Hafiz.
B'angaren Hafiz kuwa kwance yake a d'akin shi ya kwanta harya fara bacci wayar shi ta fara ringing.
Jikin shi a mace ya tashi gami da d'aukar wayar ya duba yaga Mr-Fauzan me ke kiran shi.
“At this time!!??.”
Ya fad'i haka tare da picking call d'in.
“Babban Mutum! Ya akayi ne?.”
Cewar Hafiz.
“Hafiz, Ba lafia ba fa!.”
“What is the problem?.”
“Wallahi Hafiz an yanka ta tashi.”
Hafiz wata doguwar hamma ya saki gami da cewa.
“What does that means?.”
“Please idan ma zaka aje bacci agefe ka aje, Mahaifiyar Safna ce ta rasu yau.”
Jin hakan yasa Hafiz ya saki salati, Sannan Mr-Fauzan yace.
“Hafiz I don't think zan iya bacci seriously, Yarinyar nan tana iya cewa bazata yarda na aure ta ba ' nasan ta taurin kaine da ita, And she can even blame me for her mother's death!.”
“Ai kaga abinda nake guje maka, Shiyasa tuntuni nakeso abi komai a hankali.”
“Oh come on! Yanzu meye nayi wanda ba daidai ba a ciki? Kawai son nake na taimaka mata na aure ta that is it.”
Mr-Fauzan ya fad'i haka a gadarance.
“You fall for her didn't you?.”
Hafiz yayi tambayar cike da zolaya.
“Haba dai!...”
“Oh har yanzu bazaka bada kaiba ko? Aboki kabi a hankali fa.”
“Yanzu dai what's the solution?.”
Cewar Mr-Fauzan.
“Kawai ka bari sai gobe, We will find a way out.”
OK Mr-Fauzan yace sannan suka yi sallama ya kashe wayar shi, Ya kwanta.
Mr-Fauzan koda ya kwanta tunani iri iri kawai suke zuwa mashi a rai har bacci yayi awon gaba dashi.

*FACEBOOK@SEEMALUV HAUSA NOVELS.*

*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_UNIQUE WRITERS ASSOCIATION_*

® ```Written```
By
*_Seemaluv👄_*
https://www.facebook.com/groups/1649808818646464/

*46-47*

Washe gari misalin k'arfe *7:00am* Mr-Fauzan ya tashi, Bathroom ya shiga yayi wanka tare da d'auro alwala sannan yayi sallah.
Mr-Fauzan shiryawa yayi kamar yadda ya saba cikin suit sky blue colour, Komai nashi matching color ne.
Mr-Fauzan perfume ya fesa Sannan ya fito zuwa parlor, Ko da ya isa parlor iskewa yayi har house girl ta gama shirya breakfast su Mummy sun zauna suna karyawa.
Mr-Fauzan k'arasawa wajen dinning table d'in yayi ' yayi joining d'insu ya zauna.
Mr-Fauzan Daddy da Mummy ya gaisar sannan Khairat da ke gefe tace.
"Yaya Good morning."
"Ehem, Morning Khairat.
Cewar Mr-Fauzan.
Mr-Fauzan tsiyaya tea yayi cikin cup at fara sha.
"Fauzan, Yau da safe Hajia ke fad'amin cewar Safna tayi rashin mahaifiyar ta, Allah ubangiji ya gafar ta mata."
Mr-Fauzan cikin nutsuwa ya aje cup d'in hannun sa tare da cewa.
"Amin Dad."
"Idan ka tashi zuwa wajen ta'aziyyar, Zaka tafi da Khairat ' ita ce zata wakilce mu nida Alhaji."
Mummy ta fad'i haka.
"OK, Aima yanzu zan tafi ' because inaso in lek'a office yau."
Abinda Mr-Fauzan yace kenan ya cigaba da sipping tea d'in shi.

*Some minutes later...*
Chapter 24 · 0% Book details