← Book details Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 27

Sashe 1

Boyayyen Al'amari Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Compiled by Umar Dalha.

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin K'ai...

*01*

A zaune Safna take saman tabarma rik'e da razor a hannun ta tana cire kumban k'afar ta, Sai Umma wacce take ta kara kaina a tsakar gida ' sai kuwa k'an nanta guda biyu Rumaisa da Anisa wad'an da suke wasan guje guje a tsakar gida.
Safna ita ce babba a cikin su ' don kuwa zata kai kimanin shekara 20 cir, Rumaisa kuwa shekaran ta 17 Anisa 10.
Safna, Rumaisa da Anisa marayu ne ' Mahaifin su ya rasu sakamakon rashin lafiyan da yayi mai tsana ni.
Hakan yasa karatun Safna ya tsaya cak tunda ta gama secondry school ' bata samu damar zuwa gaba ba, Kasan cewar matsalar rashin kudin da suke fama dashi.
Rumaisa da Anisa kuwa ' a makarantar Primary suka tsaya, ba tare da sun cigaba ba ' sai makarantar allon da suke zuwa anan k'ofar gida.
Rumaisa ita ke fita k'ofar gida tana suyan wara, A haka har tayi ciniki susami abinda zasuci.
Ita kuwa Safna aikatau take zuwa mak'otan su, wani lokaci haka zata gama aikin ranar baza'a bata abinci ba.
Umma ce keta d'awainiya dasu da dad'i babu dad'i, Hakan baisa tayi wani auren ba ' wani lokuta ma 'yan uwanta ke d'an harhad'a mata kayan abinci.
"Safna ya kamata ki tashi ' ki tafi wajen aikin ki rana nayi".
Inji Umma.
"Umma ranar ma tayi wallahi ' yanzu ina zuwa fad'a zasu rufeni dashi, Suda basu da uzri".
"Baki da wani uzri ai lafinki ne ' bakison zuwa da wuri, Yanzu dai ki tashi ki d'auki hijabin ki ki wuce".
"To shikenan Umma".
Safna ta fad'i haka tana k'ok'arin tashi.
"Safna zan biki".
Cewar Anisa.
"A'a kiyi zaman ki gida".
Safna na fad'in haka ta mik'e tare da janyo hijab d'inta maroon colour dake saman k'ofa, Ta sanya ta fice.
Haka ta kama hanya ' harta isa kusa da gidan ta had'e da k'awar ta tana fitowa ciki.
"Sumayya ya garin ne".
Cewar Safna.
Harare hararen da Sumayya takeyi ne ya d'aure ma Safna kai.
"Lafiya kuwa".
"Lafiyar ta kawo haka!".
"Tooo! Allah ya baki hak'uri sai anjima".
Safna tana fad'in haka ta k'arasa cikin gidan, Kai tsaye ta wuce d'akin hajiya domin su gaisa.
Bayan ta shiga ne Safna ta iske suna magana da babban d'anta.
Haka ta zuk'unna har k'asa ta gaishe ta, Bayan sun gaisa ne ta tashi zata fita Hajiya ta tsaida ita.
"Safna tsaya tukunna".
"To".
Ta fad'a tare da komawa ta zuk'unna, Hajiya bud'e jakarta tayi ta ciro kudi kimanin dubu 2 ' ta mik'awa Safna, Haka Safna ta mik'a hannu ta amsa ba tare da tasan na menene ba.
"Safna ' wannan kud'in sallama ne, Bakison zuwa da wuri kuma bakison wanke mun kwanoni da kyau ' saboda haka na yanke shawarar cenja ki" .
"Subhanallah! Hajiya don Allah kiyi hak'uri ki dawo dani ' wallahi Allah ina miki aiki dakyau, Yaune kawai na makara".
Tana fad'in haka hawaye na zubo mata a ido.
"Nifa ba kuka nace kimun ba, Saboda haka tashi ki fita".
"Hajiya kiyi mata afuwa mana".
Cewar d'anta.
"Bana son iskanci kaji ko?".
"Allah ya huci zuciyarki".
Safna kuwa ganin bata da niyyar hak'ura ne yasa ta tashi ta fita, Harta kama hanyar fita taji motsi a kitchen alamar ana wanke wanke.
"Bari inga wacce aka cenja".
Ta fad'a a zuciyar ta.
Tana k'arasawa wajen taga mahaifiyar k'awarta wato sumayya, Mamaki ne ya cika Safna ' hakan yasa ta juya da sauri tabar wajen.
Haka Safna ta baro gidan cikin wani hali ' tafiya kawai takeyi tana share k'wallar dake idon ta, Har ta isa gida cike da sallama a bakin ta.
Umma ta iske ita kad'ai a tsakar gida tana surfa dawa.
"Wa'alaiki-salaam Safna, Lafiya kika dawo?".
Matso murmushi tayi ta sakar mata ' amma sam fuskarta babu walwala, Tukunna ta k'arasa kusa da Umma wacce tayi kasak'e tana kallon ta.
"Am... Umma ga wannan inji Hajiya".
Safna mik'awa Umma kud'in tayi, Umma ta lura idanun ta cike suke da hawaye.
"Tooo Kud'in aikin ki aka biyaki da wuri haka?".
"A'a Umma, Kud'in sallama ce".
Nan gaban Umma ya fad'i tayi sauri ta jinginar da tab'arya jikin bango, Gami da dafe k'irji.
"Uban me kikayi? Iyi Safna wane laifin kika aikata? Sata kikayi mata?".
Jin an abaci sata ne ' yasa Rumaisa fitowa daga d'akin su cikin sauri, Ita kuwa Safna hawaye kawai ke mata zarya a fuska.
"Haba Umma! Ya za'ai kici taimata sata? Bayan kinsan halayen Yaya Safna kaf...".
Idanun Umma ne suka ciko da k'walla, Rumaisa tasa hannu ta sharewa Safna hawaye tare da janyo tabarma suka zauna.
"Yaya Safna meya faru?".
Nan Safna ta fad'awa Umma duk abinda ya faru, Umma waje ta samu ta zauna cike da ajiyar zuciya.
"Yanzu abunda Hajiya zatai mun kenan?".
"Umma karki damu ' insha Allah zan fita in nemi aiki, Kuma insha Allah bazamu tagayyara ba".
"Rumaisa ina Anisa?".
Inji Safna.
"Tana Bacci".
Mik'ewa Safna tayi idon ta akan Umma wacce duk damuwa sun bayyana a fuskar ta.
"Umma ki bani koda dubu d'aya ne cikin kud'in, Domin zan hau adaidaita sahu ' inshiga cikin gari".
"Hm... Yanzu idan kinje ina zaki nufa?".
Cewar Umma.
"Umma manyan kanfanoni(Companies) zan fara bin cikawa ' ni koda share share ne su bani".
"Hm... Meyasa baki tunanin k'asa da wannan? Meyasa baza kije gidaje ba? Safna ina ganin kamar neman aiki a kanfanoni zaiyi maki wahalar samu".
Rumaisa ce tayi saurin kutsa baki cikin maganar.
"Haba Umma fatan alkairi kawai zamuyi mata".
"Hakane Rumaisa".
Umma na gama rufe baki ' ta zari dubu ta mik'awa Safna, Ta karb'a sannan tasa kai ta bar gidan cike da rashin sanin inda zata fara nufa.
Bayan Safna ta fito ne ' tayi sa'a tasami adaidaita ta shiga.
"Ina muka nufa?".
"Cikin gari zamu shiga ' kawai kaita kewaye da wajajen manya manyan ma aikatun nan".
Haka mai adaidaita sahu yaja napep d'inshi Safna na ciki, Har suka isa cikin gari.
Mai napep zagaye ya dunga yi da ita ' tana k'arewa kowacce ma'aikata kallo kasancewar Garin babban gari ne ba k'arya. Safna wani k'ayataccen company ta hango cikin garege d'inshi motocin ma'aikata ne birjit iyakar ganin ka.
Hakan yasa Safna yin saurin tsaida mai adaidaita sahun.
"Bawan Allah mu tsaya anan, Nawa ne kud'inka?".
Tayi tambayar tana k'ok'arin saukowa daga napep d'in.
"Gaskiya malama bisa adalci ' dubu d'aya zaki bani".
"Haba kaikuwa? Har dubu d'aya? Ina laifin d'ari ukku? Kaga fa dubu d'ayan nan ita kenan mun, Kuma wajen nan zan iya kaiwa yamma".
"Shikenan kawo d'ari biyar ' gaskiya iyakar abunda zan iya ragewa kenan".
Inji mai Napep.
Safna mik'a mashi dubu d'ayan nan tayi, Shi kuma ya bata cenjin d'ari biyar sannan ta juya ta doshi cikin company d'in.

*DEDICATION...:*
_My Family!♥♥_

*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI*

*_Pure Moment Of Life writers_*

© ```Written```
By
*_Seemaluv_*👄

*2-3*

Safna tafiya takeyi tana kallon yanayin Company d'in, Har ta isa bakin k'ofar shiga ciki ' jitayi ana.
"Hey! Hey!!!".
Hakan yasa ta tsaya cak ' cike da fargaba, Wasu securities guda biyu sukayo kanta.
"Madam! How can we help you?".
Nan bakin Safna ya hau rawa ' kasan cewar turancin kad'an kad'an take iya maidawa.
"Am... Sunana Safna ' nazo neman aiki ne a job".
Nan securities d'in suka fara dariya tare da k'are mata kallo.
"Madam, ba'a d'aukan aiki anan, saboda haka ki tafi ki nemi wani wajen".
Cewar d'aya daga cikin su.
"Don Allah koda shara ne zanyi muku ' sai ku rik'a biya don Allah".
Tana gama fad'in haka suka rufe security door d'in, Hakan yasa Safna juyawa ta matsa daga wajen ' ta nemi waje ta zauna tana k'arewa motocin da ke wajen kallo.
Bata ankara ba taji iskar hadari ta taso ' hakan yasa tabarin wajen cikin hanzari, Ta shige cikin wani garden wanda aka k'ayatar dashi matuk'a.
Safna kujera ta samu ta zauna ' tare da d'aura kanta saman table, Haka akaita tsugaga ruwan sama ita kuwa tuni bacci ya kwashe ta a wajen.

*35 MINUTES LATER*
Chapter 1 · 0% Book details