← Book details Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 33

Sashe 6

Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

<<10>>
  Ta muskuta tana duban talabijin. Yau zata rainamishi wayo tunda abin nashi hakane.
   Tayi tsai bayan ta gama fahimtar inda labarun ya dosa. Akan yara masu (kwashiorkor) ne, har gasunan ana nunosu ana jawabinsu. Ta turo d'ankwalinta gaba, kafin ta soma magana.
"Ana magana akan wad'anda k'iba tayi musu yawa ne, da ace duk zasu koma kamar wad'annan da kwarai sun ji dad'in rayuwa kuma..."
  Ba zato ya sakarmata rankwashi a tsakar kanta.
  "Banga amfanin karatunki ba. Tashi ki bani wuri kafin na kwasheki da mari. Dak'ik'iyar kawai."
  Ta mik'e da saurinta ta nufi kicin d'in, tana shiga ta kwashe da dariya, Ma'u da Aisha na tayata kasancewar suna jin abinda ke wakana tsakaninsu.
  "Baki da kirki wallahi. Kin raina mijina Bintun Mami."
  Bintu tana 'yar dariya ta amsa.
"Atoh, ya cigaba da takurawa rayuwata ya gani."
  Sukayi dariya. Sun riga sun kammala, ta ja kujera ta zauna  tana dubansu yayinda suke jerawa saman babban faranti.
Tana ta afkin girgiza k'afa, d'abi'ar da Mami ta hanata. Ma'u kawai take k'arewa kallo ganin yanda fatarta ta murje ta k'ara k'iba sosai.
  "Tab, Anti Ma'u wallahi ki rage k'ibar nan, nan gaba zaki iya illah."
  A mamakince suka dubeta.
  "Illa wace iri kuma?" Cewar Ma'u.
"Yanzu misali, Yaya Ma'aruf ya k'ara aure tsab zaki tomasheta,wannan duka d'aya da wannan mulmulallan hannun naki kin kasheta."
  Aisha ta ji hanjin cikinta sun kad'a. Yau Bintu ta janyomusu, mai fitar da ita sai Allah. Ma'u tayi murmushin yak'e.
  "Hum, ballantana ma bana tunanin Mijina na sha'awar k'ara auren. Sam, ba shi da wannan ra'ayin. "
  Ta d'auki farantin ta fice. Dukan da Aisha ta d'aka mata a cinya ne ya maido da idanunta gareta ga barin kallon Ma'u.
  "Kinsan abinda kike fad'a kuwa? Wallahi naga alama kina neman sanyamu cikin blacklist  d'in anti ma'u. Yau mun shiga uku."
  Bintu ta tsayar da ita ta hanyar yarfamata hannu.
  "Ke dallah can kyaleni, ta sanyamu mana sai me? Nifa ba tsoranta nakeji ba. Ai duk laifinku ne, saida nace bazan zo ba kuka matsamin. Maganin kar ayi kar a soma."
  Aisha dai tayi lamo kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
  "Aisha!" Muryar Ma'u ya katse mata tunani. Ta zaro ido
"Shikenan, ta sanarwa Yaya."
  Bintu ta ta6e baki ta bi bayanta suka fito.
  "Kuzo ku karya mana."
Bintu ta girgiza kai.
  "Nidai na k'oshi, Mami fa cikamin..."
  Kallon da Ma'aruf yayi mata ya sanyata yin shiru.
  "Toh Aisha fa?"
Aisha ta girgiza kai.
"Na k'oshi Anti, mun karya kafin mu fito."
   Zama sukayi suna duban TV. Bintu sai afkin satar kallonsu takeyi. Sai hirarsu sukeyi akan abinda ya shafi ambaliyar ruwan da ake nunowa anyi a wani gari a Aljazeera.
  Can kuma tayi magana.
"Yaya zamu wuce."
Ba tare da ya dubeta ba ya jefo mata tambaya.
  "Daman ba yini kuka zo ba?"
"Eh, gidan Yaya Rufa'i zamuje."
Sai lokacin ya d'ago ya dubeta.
"Ba zaku bar gidannan yanzu ba tunda ba a kurkuku kuke ba, idan na dawo anjima da rana sai na saukeku."
   Ran Bintu ya 6aci, ta daure dai ta had'iye 6acin ran sannan ta koma ta zauna.
  Aisha bataso furucin Yayan ba, don gaba d'aya ta tsorata da Bintu, tana tsoron kato6arar da zata k'ara yi musu.
  Saidai Bintu ta bata mamaki, sakewa tayi kamar batace komai ba, itama Ma'un bata nuna komai a fuska ba. Saidai har zuciyarta ta ji ta tsani yarinyar, ta lura tantiriya ce ta bugawa a jarida. Dole tayi takatsantsan.
   Sai bayan da Ma'aruf ya dawo suka tafi. Bintu zaune a baya. Tana ji yana tambayar  Aisha ko itama tana kula samari. Tayi kamar batasan wainar da suke toyawa ba.
Can ta d'ago kanta, suka had'a ido, ta sauke nata tana murmushi kawai. Ba koyaushe takeson magana ba.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)

<<11>>
Yana saukesu yayi gaba bayan ya basu dubu d'ad'd'aya. Sukaui godiya.
Hajara uwar surutu, nan suka had'u sukayita zuba kamar ruwan famfo. Yaya Rufa'i baya gidan bai dawo daga ofis ba. Nan sukayita kyakyata dariyar abinda Bintu ta yiwa Yaya Ma'aruf da matarsa.
"Ke dai Bintu zanso naga mijin da zai kwashi shiriritarnan ta ki." Cewar Hajara. Bintu tayi dariya irin ta rainin hankali.
"Mijin Bintu? Tab, yana k'asar waje yana karantar masters yanzu."
Suka gwalalo ido.
"Waye?" Suka tambaya har suna had'a baki.
Ta dubesu kafin ta cigaba da rainamusu wayo
"Yana nan, kulkum muna waya. Duk randa ya zo k'asar nan, zaku ganshi."
"Mts, mak'aryaciya kawai."
Aisha ta fad'a bayan ta d'agota.
"Ina batun k'arya anan?"
Aisha tayi murmushi tana duban Hajara.
"Ai nasan halinta ciki da bai. 'Yar iska kawai, wallahi k'arya takeyi.'
Bintu ya kyalkyale da dariya.
"Ho ni, ranar aurena akwai rawa da gira d'aya." Suka dara.
Ranar sun jima cikin nishad'i har dawowar Rufa'i. Shima ya biyemusu sukayi tayi, saida Mami ta kira wayarsu sannan sukayi azamar tafiya, Rufa'i da kansa ya kaisu gidan.
* * *
Bayan watanni Bintu ta soma zuwa jami'a, business take karanta. Aisha lokacin ta shige level2, ita kuwa, Accounting take karanta. Alokacin Hajara ta haifi d'anta namiji, wanda ya ci sunan kakansa Abba, wato Umar suke kiransa Sadauki. Cikin iko da hukuncin Allah itama Ma'u ta samu ciki saidai bisa matsalar da likita yace mahaifarta tana da shi, ya sanya aka k'ulle mata bakin mahaifar da fatan samun cikin ya zauna.
To fa! Bintu kai ya k'ara wayewa, an shiga jami'a. Kwalliya take ci har da na ban mamaki, a lokacin ta k'ara sanin rayuwa, tasan lallai ado shine mace. Hijabi idan ba don sallah ba, ko kad'an baya daga cikin suturunta na sanyawa ta fita, a cewarta yafi dacewa da gidan malamai. Aisha kuwa jefi-jefi takan sanya wataran ta fita makaranta.
Abinda zai burge mutum da Bintu, ko kusa bata da kula kulan samari. Idan kuma ka matsawa rayuwarta, toh fa alokacin zatayi maganinka ta hanyar cin kud'in da k'arya-k'aryacen ankon biki da na katin waya. Ga duk saurayi mai hankalin da ya fahimci ba don Allah take sonshi ba, nan take yake yanke mu'amalarsu. Idan kuma ta gane da iskanci kazo, ta zageka tas ta kuma gargad'eka da babbar murya.
A haka rayuwar ke tafiya.
Watarana tana zaune a baranda, sanye da T-shirt ja da zanin atamfa, kanta babu ko d'ankwali, ta bararraje tana shan rake tana kallon wata wak'a a wayar d'an dolo dake zaune gefen kujera shima yana fisgar rake. Sai dariya suke 6a66akawa da hirar duniya, Mami batanan ta fita, Aisha kuwa tana kwance a falo tana jinsu.
Babu zato Ma'aruf ya iso, sam basuji k'arar motarsa ba kasancewar a waje ya fakata.
"Kai bari na tura wak'ar nan wayata, tayimin kyau."
Cewar Bintu wacce hankalinta kacokam ya tafi akan wayar, gaba d'aya batasan da tafiyar d'an dolo ba. Hakanan batasan da zaman Ma'aruf ba a wajen.
Kallonta yakeyi a matuk'ar fusace, yana takaicin wannan taurin kai irin na Bintu da bata da aiki sai hira da d'an dolo.
Ya warce wayar kafin ya kai mata hauri da k'afarsa ya had'a da kai mata mari, da sauri ta kauce.
"Don ubanki bana hanaki mu'amala da mutumin nan ba? Ina rantsuwa da Allah sauran k'iris ya bar gidannan!"
Tuni ta soma hawaye, ranta ya 6aci, kamar ita k'atuwar budurwa wai Ma'aruf ke duka?
"Ai ba hira mukeyi ba, wata wak'a yake gwadamin."
"Wak'ar banza da wofi kai! Shashasha kin zauna kanki babu ko d'ankwali kina wagewa gardi baki. Zan sa6amaki wallahi!"
Ta mik'e ta tattara wayoyin ta nufi ciki tana kuka, bata tsaya a falon ba ta zarce zuwa d'akinsu. Yaya Ma'aruf ya tsani ganin walwalarta, tun tana k'arama ya takurawa rayuwarta. Lallai zata bar gidan nan idan har ba zai kyaleta ba. Ta yi kwafa kawai.
Mami koda ta dawo, bata goyamata baya ba, haka tayi mata fad'a ita dai a ganinta kowa ya tsaneta ne kawai.
Hakan yasa ta dauki fushi da mutanen gidan. Daga gaisuwa bata k'ara cewa uffan ga kowa. To gidan ya koma babu dad'i garesu, daidai da ma'aikatan Mami suna jin dad'in zama da Bintu, da wuya kuyi hirar mintuna uku bata sanyaka dariya ba. Abba da kansa ya rarrasheta don kuwa samunsa tayi tace zata tafi Rano. Mami jikinta yayi sanyi, tana son Bintu, wannan ne dalili babba da ya sanya ta d'aukota daga wajen k'anwarta Dije.
Nan ta shiga nan nan da ita har ta ware. Washegari ran Mami yayi fari k'al ganin Bintu ta shirya ta nufi makaranta, don har makarantar ma yaji tayi masa.
* * *
Bayan watanni tara, Aisha ta koma gidan Yayanta Ma'aruf domin taimakawa Anti Ma'u. Gaba d'aya daman an hanata aiki mai wahalarwa, cikinta ya girma cikin hukuncin Allah saidai a yanda likitan ya fad'a, cs zasuyi mata, har an sanya (Date).
Suna samun hutu Aisha ta koma gidansa. Bintu ko daman Rano takeson zuwa, rabonta da Rano tun kafin ta soma zuwa jami'a. Saidai zuwa yanzun tana matuk'ar tausayawa Ma'u musamman yanda ciki ya sanyata ramewar dole. Har mamaki Aisha da Mami kai harma da Hajara sukeyi idan sun ga yanda Ma'u da Bintu ke d'asawa. Kodayake, Bintu bata da raini a zahiri, barta dai idan ta so zata kwa6a maka magana a wasa. Tana da fushi amma bata da rik'o. Sannan a gaban Ma'u ta sha fad'amata. Ta k'i jinin mijinta, tafi k'aunar zuwa gidan Yayanta Rufa'i akan Ma'aruf. Da Ma'u ta fahimci halin na Bintu haka yake, sam bata da 6oye abinda ke ranta, yasa ta bar damuwa.
Kwananta uku a Rano, aka yiwa Ma'u aiki.
Suna zaune tsakar gida suna hira da yayanta Saifullahi, sai kannenta, Habib da Habiba, da Innarsu sai 'ya'yan abokiyar zaman innar, wacce suke kira Umma .
Wayarta tayi k'ara ta duba. Ganin sunan A'i yasa ta d'agawa da sauri.
"Me muka samu?"
"Baby Boy." Cewar Aisha cikin tsananin murna.
Ihu Bintu ta saki tana mai tsananin farin ciki.
"Ta haihu! Ta haihu!!"
Haka ta hau fad'i. Nan su Inna suka shiga murna da hamdala.
Washegari kuwa wajejan tara na safe, Inna da Bintu sai Saifullah suka nufi Kano.
Tunda Bintu ta shaidawa Mami sun taho ta kashe wayarta. Basu jima sosai ba a hanya (inji ni..lol) suka iso Birnin Kano.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)
Chapter 6 · 0% Book details