← Book details Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 33

Sashe 12

Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

<<21>>
  Bata kai ga bud'e k'ofar d'akin nasu ba ta ji hon d'in motarsa.
Ai take hanjin cikinta suka kad'a. Da sauri ta fito daga d'akinsu tana lek'ensa ta windon falon Mami. Tana kallo ya kashe motar ya kwashi wayoyinsa, akan idanunta sukayi magana da baba maigadi, batasan abinda suke tattaunawa ba, k'arshe ya yo ciki. Da sauri ta saki labule, kirjinta kamar ana lugude tsabar bugun da yakeyi. Shikenan kashinta ya bushe. Ta fito tana sand'a har ta iso farfajiyar gidan.
  "Ke!"
Ta ji an dakamata tsawa, a firgice ta juyo, yana tsaye jikin windon falonsa yana hangenta.
Ta zaro idanunta taba dubansa kafin kuma tayi narai-narai da fuska kamar mai shirin kuka.
  "Zo nan!"
"Shikenan na gama yawo." Tayi furucin a fili.
Daga haka ya sauke labule. Dole ta taka ta nufi d'akin, a ranta banda addu'o'i babu abinda takeyi.  
  Ta shiga da sallamarta. Ya amsa a ciki, yana tsaye a tsakar falon. Yayi mata kallon tsanake tun daga fuska zuwa yatsun k'afafunta daga inda yake tsaye. Fuskarsa sai ka rantse bai ta6a dariya ba. Batasan ya akayi ba ta ji ta tsugunna.
  "Yaya barka da dare."
Bai amsa ba.
"Ina zaki?"
"Di..di..nar Hafsa."
Ya d'anyi shiru.
"Mami bata ce kiyi jirana bane?"
  Ya fad'a cikin tsananin zafin rai, gaba d'aya yarinyar haushi take ba shi, ya tsani a rainashi. Abin ban haushin ma, wai ita akeson ba shi matsayin mata, wannan abu da me yayi kama?
   "Ta fad'a."
"Ok, itama kin rainata kenan?"
Ta d'an dubeshi, sai kuma ta sauke idanunta, gaba d'aya jikinta ya d'auki rawa. Fatanta Allah Ya mantar da shi abinda tayi mishi jiya kada yayi mata maganar. Ai kuwa dai alokacin baiyi d'in ba. Ya d'auki wayoyinsa ya shige d'aki. Nan ta zauna zaman jira, tun tana duba agogo har ta daina, idanunta tuni suka kawo ruwa ta soma zubar hawaye. Bakinciki da takaici duk suka bi suka addabeta, yana sane ya shanyata. Ta kwashi kusan rabin awa a zaune saman kafet d'in kafin ya fito daga d'akin. K'amshin turarensa ya daki hancinta, ta d'ago ta dubeshi ranta cike da jin tsananin haushinsa. Saidai kuma wani irin sanyin jiki ya ziyarci zuciyarta ganin yanda ya had'e iyakar had'ewa kai ka rantse injin matso kyau ya shiga. Sanye yake da farin boyel mai tsadar gaske, ya d'ora hula bak'a. Yayi kyau har ya gaji. Saidai ta gwammace bata dubeshi ba, don kuwa bai bita da komai ba sai harara. Baice mata uffan ba har saida ya nemi wuri ya zauna, takalminsa ya soma k'ok'arin zurawa.
  "Kina sane da laifinki ko?"
Ya fad'a ba tare da ya dubeta ba. Ta saci kallonsa, ita kam duk ta tsorata.
  "Don girman Allah Yaya kayi hakuri." Ta fad'a cikin muryar kuka, bil hakk'i ta tsorata ganin yanda koda wasa babu annuri a fuskarsa.
   Baice mata uffan ba har ya kammala ya soma kashe futilu, ganin haka ta fito tana sharar kwallah har da sauke ajiyar zuciya duk a hangenta ta tsira.
   Bayan sun isa wajen motarsa ta kama gidan gaba zata bud'e ya harareta.
  "Koma baya."
Ta koma babu shiri, ai ita ko boot ne zata shiga matuk'ar ba zaiyi mata wani hukunci ba.
  Ya saki kid'a lokacin da motarsu ta cilla titi. Tana kalle-kallenta a hanya, tun tana saka ran ganin sun iso Afficent har dai ta nutsu ta gane ba ma hanyar suka d'auka ba.
  Fargabarta ta k'aru, gaba d'aya hankalinta ya tashi.
  "Yaya ba hanyar muka yi ba kamar."
  Baice mata uffan ba sai ma ya k'ara volume na rediyo. Ai kuwa ta soma kuka. Ya dubeta ta madubi ya dauke kansa yana mai sakin murmushin mugunta.
  Bai tsaya ko'ina ba sai a wani k'aton gida wanda ko ba'a fad'a ba, kallo d'aya idan ka yiwa gidan zaka san akwai wani abu wai shi kud'i.
  Bayan ya shiga yayi fakin ya rage muryar kid'an dake tashi. Wayarsa ya fiddo ya danna kira bayan ya bud'e speaker.
  "Prince." Wata murya ta fad'a daga can 6arin, yayi wani murmushi na mugunta yana mai duban fuskar Bintu wacce take k'arewa gidan kallo ta madubi amma furucin da ta ji wata tayi ya sanyata maido hankalinta ga saurarensa.
  "Gani nan a waje."
Daga can ta saki ihun murna.
"Wow!! Yau lallai ina da mugun sa'a. Ma'aruf da kansa a gidannan?"
Ya d'anyi dariya kafin ya amsa.
"Kika wuce 5minutes zan juya na koma inda na fito."
Ai sai ta d'an d'aga murya.
"A'a, na tuba don Allah. Ganinan fitowa."
Ya katse wayar. Bintu ta rushe da kukan bak'in ciki, tsabar ma rainin wayo yau itace ta zama 'yar rakiyar zance?
"Rufemin bakinnan."
Ya fad'a a hankali, dolenta tayi shiru. Ya d'an karkato yana dubanta.
"Ko tari ban yarda kiyi ba har mu bar gidannan wallahi, idan kikayi wani kwakkwarar motsin da ta fahimci kina motarnan sai kin raina kanki. Bani wayarki."
Da sauri ta mik'a mishi tana kokarin danne kukan da ya taho mata, wata irin tsana da haushin Ma'aruf kawai take ji.
Ya kashe wayoyinsu ya ajiye.
Mintuna uku kawai, sai ga wata budurwa kyakkyawar gaske. Fara tas da ita, ta ci ado har ta gaji cikin wani rantsesan yadi. Tana taku cike da yanga. Bintu sai kuka ya tsaya cak, shakka babu ta had'u iyakar had'uwa. Ita kuwa budurwar ko kusa bata ganinsu kasancewar gilas din tint. Ta k'araso, Ma'aruf ya bud'emata gefensa ta shigo ta zauna.
Nan ta bishi da wani sassanyar kallo.
"Prince ka shayar da ni mamaki, na kasa gask'atawa. Don Allah mu shiga daga ciki mana."
Ya d'an ja fasali kafin ya amsa yana wani yamutse fuska.
"No, kiyi hakuri, ina da uzuri ne banason na jima. Don kin damu da ganina ne na daure na zo yau."
Bintu fa ta ga abinda ya fi k'arfinta. Ashe daman haka mata ke yiwa Yaya Ma'aruf? Mamakin da takeyi bai wuce yanda wannan mace mai shegen yauk'i da ji da kanta ba ta marairaicewa Ma'aruf har tana rok'onsa ya dunga kulata ko yayane tunda mai sonka yafi mak'iyinka.
Ta saki ido da baki tana duban yanda shi kuwa yake faman shan k'amshi. Gaba d'aya ta samu abin kallo ta mance da batun dinner. Wannan shine karon farko da ta ji Ma'aruf ya burgeta...!!
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)

<<23>>

Yana zaune gaban Abba domin amsa kiransa. Abba ya dubeshi.
  "Ina sauraron ra'ayinka game da maganarmu ta kwanaki."
Ma'aruf ya k'ara yin k'asa da kanshi.
  "Na amince." Ya fad'a da kyar, Abba ya ji wani farinciki ya lullu6eshi. Ya yi hamdala a fili kafin ya bi Ma'aruf da kyawawan addu'o'i. A k'arshe ya sallameshi.
Ma'aruf ya mik'e jiki babu kwari ya bar falon.
  Kai tsaye falon Mami ya nufa. Tun kafin ya k'arasa ya jiyo dariyar Bintu da Aisha saidai na Bintun yafi na kowa d'aguwa. Takaici ya sanyashi fasa shiga ya juya ya koma sashensa. Wai meya kaishi amincewa auren wannan yarinyar ne? Wane su6utar baki ne haka?
  Kai gaba d'aya ji yayi ya tsani kansa, ya tsinci kansa cikin yanayin 6acin rai da damuwa matsananciya. Ganin ba wani sauk'i ya sanyashi barin gidan batare da ya d'auki motarsa ba.
                     * * *
   Bintu tayi shiru tana duban Mami wacce ke k'ok'arin zama gefenta a saman gado. Mamakinta bai wuce na kiran da Mamin tayi mata ba har da rufe d'aki da korar Aisha.
   Mami ta soma da kiran sunanta.
"Fatima Bintu, takwara kuma d'iya awajena."
  Bintu tana murmushi ta amsa.
"Na'am."
Shiru ya d'an biyo baya, ita kam tana jin nauyin ma gayamata maganar, saidai ba yanda ta iya tunda Abba ne ya sanyata jin ta bakinta.
  Cikin hikima irin ta manya Mami ta soma da kwantar mata da hankali da nunamata lallai ita mai k'aunarta ce, ba zata bari a cutar da ita ta kowane hanya ba. Tana k'aunarta tamkar yanda take k'aunar yaranta. A k'arshe ta sanarmata da buk'atar Abba ta son had'ata aure da Ma'aruf har ta k'ara da sanarmata cewa Ma'aruf ya amince da aurenta.
   Bintu ta ji gabanta ya mugun fad'uwa, Ma'aruf kuma?! Innalillahi!! Meyasa tunanin Abba zai kawomishi hakan? Ya zatayi da rayuwa idan har Ma'aruf ya kasance mijin aurenta? Idanunta suka ciko da kwallah. Mami ta kauda duba daga gareta cikin sanyin jiki tace.
  "Bazan bari a kwareki ba Bintu, zan jiraki daga nan zuwa kwanaki uku, matuk'ar baki k'aunarsa, kada ki kwari kanki, ki fito fili ki sanarmin, bazan ta6a bari a aura miki shi ba. Ki tsayar da tunaninki wuri guda, ki kuma dunga addu'a."
  Daga haka Mami ta fita daga d'akin batare da ta k'ara dubanta ba ballantana ta fahimci komai a fuskarta.
  Bintu ta zame ta zauna dirshan a saman carpet. Yaya Ma'aruf fa?!! Me ya burgesu har sukayi tunanin wannan had'in? A rasa ma wanda za'ayi tunanin had'asu aure da shi sai mutumin da ya k'i jinin walwalarta? Koyaushe burinsa ya k'untata rayuwarta?
  Abar batun haka ma, ta nunamusu wata alama na cewar aure take buk'ata ne? Eh lallai, sun bi son zuciyarsu kawai zasu yiwa d'ansu gata. To ai itama tana da nata gatan, don haka ba zata k'ara kwanan gidansu ba daga wannan rana, gobe Rano zata nufa.
  Gaba d'aya tunanin Bintu ya birkice, kukanma babu sai ruwan hawaye kawai. Ranta banda k'una babu abinda yakeyi. Ba Ma'aruf d'in kad'ai ba, gaba d'aya gidan saida ta ji ta tsanesu.
   A ranar haka ta wuni babu walwala, Mami na lura da ita saidai batace uffan gareta ba. Gaba d'aya itama ta ji ta damu, tayi da na sanin yi mata maganar nan, daman ita tasan da wuya abin ya yiwu. Da dai ace Rufa'i ne, wannan kam tana da tabbacin ba lallai ne Bintu ta k'i ba.
  Gidan bai musu dad'i ba ko kad'an,  daman Bintu ce mai rayamusu shi, yau ita kuwa babu kanta. Fuskarta tamkar an aikomata sak'on mutuwa.
  Washegari da wuri ta fito, ta lissafa kud'inta zasu isheta hawa motar zuwa Rano. Kai tsaye kuwa inda zata sami motar ta nufa maimakon makaranta.
  Inna suna zaune sai ganinta sukayi. Nan k'annenta suka hau murna. Umma kishiyar Inna batanan, hakanan Saifu da babansa suna kasuwa. Kallo d'aya Inna tayi mata ta fahimci babu lafiya. Abin akwai mamaki matuk'a.

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)
Chapter 12 · 0% Book details