← Book details Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 33

Sashe 14

Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

<<24>>
 Bayan sun shiga d'aki ta kora yaran zuwa tsakar gida. Bintu tuni ta soma hawaye.
  "Ke, sanardani meke faruwa? Ina Yaya Fatima, ya na ganki ke d'aya?"
  Inna ke jero dukkan tambayoyin nan cike da tsananin rud'ani. Bintu ta tsaida kukanta.
"Wai Mami ce, wai.." Kuka ya hanata k'arasawa. Inna ta soma fusata.
  "Ki gayamin mana, me yafaru?"
"Cewa sukayi zasu auramin Yaya Ma'aruf."
  Mamaki ya rufe inna, ta tsaya kyam tana dubanta.
  "Shi ne kikace musu me?"
Ta turo baki.
"Gudowa nayi don ni..."
Marin da Inna ta shek'a mata ya haneta k'arasawa. Cikin tsananin tashin hankali take dubanta, kamar ba wannan Innar mai sanyin hali kuma mai tsananin nuna k'auna gareta ba. Kallo d'aya ta hangi tsananin 6acin ran dake kwance saman fuskarta.
   "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Inna ta maimaita har sau biyu. Kawai sai kuma ta kece da kuka.
  "Kaico wannan rayuwa, ni Dije wane zamani muke ciki da d'an Adam ke saurin manta halacci? Da ace kinsan menene kawaici da girmamawa da lallai baki baro gidan 'yar uwata ba bisa wannan k'aramar maganar. Idan ban ta6a gayamiki ba yau ki sani, Yaya Fatima ko dukkan yarana ta nema na bata ta rik'esu zan iya, babu irin sadaukarwar da bazan iya yi dominta ba matuk'ar bai sa6awa addini ba. Ban taso naga mahaifiyata ba, Yaya Fatima nasani, bayan mahaifina, bani da wata gata sai ita. Idan nace zan tsaya gayamiki ire-iren abubuwa na kyautatawar da Yaya Fatima tayimin a rayuwa zamu iya cinye lokaci wanda bazan so hakan ba. Bazan so Yaya ta ankara da cewar nan kikazo ba, ban haifi d'iyar da zata k'i biyayya ga 'yar uwata ba, yanda banyi ba, to muddin ina raye ba zan aminta da d'ayanku ya aikata hakan ba. Kin bani kunya! Kin kuma shayar da ni mamaki kwarai, ko a mafarki banyi zaton 'yar uwata zata bijiro miki da wata buk'atar ba ki k'i amincewa. Bakisan fa dad'ina ba Bintu, Yaya Fatima ita ta yayeki, itace komai na gatanki. Tana sonki fiye da son da na nunamiki, a tunaninki, Yaya Fatima zatayi abinda zai cutar da ke da rayuwarki?"
Inna ta k'arashe cikin sanyin murya. Ta ja majina
"Tun kafin na 6ata miki rai nayi abinda ban ta6a yi gareki ba, ki tashi ki koma inda kika fito, idan kuma na isa da ke, ki amince da auren dan uwanki."
   Bintu ta mik'e jikinta a sanyaye, da alamu dai maganganun na Innarta sun shigeta. Har ta sanya kai zata fice, Inna ta kirawota ta mik'a mata dubu biyu akan ta k'ara kud'in mota. Ta k'ara da fad'in.
"Ma'aruf yaro ne da yasan abinda yakeyi, yasan daraja da girman d'an adam. Miji ne wanda zakiyi alfahari da shi. In sha Allah ba zaki koka ba da kasancewarsa miji gareki. Ki koma ki yi biyayya ga uwarki mai k'aunarki. Kada ki sake ki sanarmata kinzo garinnan. Kije, Allah Yayi albarka ga rayuwarku, Ya shiga lamuranku. Ina miki murnar samun miji abin alfahari ga dukkan wacce ta sameshi."
Bintu ta dubi innarta cikin zubar hawaye. Sai kuma ta juya a sanyaye ta gyara zaman jakar hannunta wacce ta fito da zummar zuwa makaranta ta yo Rano. Ta fice daga d'akin bata bi ko ta kan k'annenta ba dake yi mata magana ba ta bar gidan da sauri-saurinta.
Don tayi sauri yasa ta hawan k'aramar mota peagout. A motar ma hawaye kawai takeyi. Gaba d'aya ta tsinci kanta cikin jin kunyar abinda ta so aikatawa Maminta mai k'aunarta da zuciya d'aya. Lallai ta kusa tafka kuskure babba, dad'in magabata kenan. Duk wanda a duniya ya rasa mai fad'a masa gaskiya shakka babu yana cikin garari na rayuwa. Tayi alk'awarin yin biyayya ga Abba da Mami, zata auri d'ansu ba wai don halinsa ba, saidai domin Allah.
"To so fa? Kina sonsa?"
Wata zuciyar ta jefomata tambayar da ta hautsina cikinta. Ai ita batasan ma soyayyar ba ballantana ta fahimci komai. Kodayake, a zamanin k'uruciyarta, Aisha ta ta6a shaida mata kad'an daga yanda kake gane ka fad'a son mutum. Fad'uwar gaba, da wani kallon kwayar idanu.
Ta ja k'aramin tsaki. Shirme kenan. Tsoro ke kawo fad'uwar gaba kawai, shi kuma kallo, kawai idan mutum yana da kwarjini zaisa ka ji bazaka iya duban kwayar idanunsa sosai ba. Banda wannan, sauran kawai tunani ne na marasa aikin yi da suka yarda suka amince da soyayya har ma suke wahalar da rayuwarsu.
A haka tayita tunane-tunanenta har dai suka shigo Kano, kai tsaye tashar unguwa uku suka isa. Mintuna arba'in ne suka kawosu. Ta duba agogon dake d'aure a fatar hannunta. K'arfe uku na rana har da mintuna.
Ta fito ta nemi abin hawa tayi mishi kwatance.
Adaidai junction na titin Zoo road, wajejan Oasis Bakery motarsu ta tsaya cikin go-slow.
Ma'aruf yana daga gefensu batare da zato ko tsammani ba, a gefensa abokinsa ne Hashim suna ta6a hira. Juyowar da zaiyi ya hangeta cikin adaidaita, fuskarta babu walwala, hankalinta gaba d'aya yana ga kallon gabanta, yayi daidai da basu hannu da akayi wanda ya janyo rabuwarsu. Mamaki kwarai ya kamashi. Daga ina take? Wajen wa ta zo a wannan unguwar? Abin mamakin kenan, sam bata da k'awaye ballantana yayi zargin ko wajensu ta zo. Haka ya 6oye mamakinsa ya maida hankali ga abokinsa da ya dage ba shi shawarar yanda zai tafiyar da zaman aurensa da Bintu har ma ya ladabtar da ita.
Shi dai Ma'aruf baice uffan ba. Tunaninsa gaba d'aya ya tafi ne ga ganin da ya yiwa Bintun yanzu daga hanyar da zata sadata da unguwa uku. To ko dai Rano ta je? Yayi kwafa a ransa kawai.

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)
Chapter 14 · 0% Book details