← Book details Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 33

Sashe 15

Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

<<26>>
Rufa'i ya dubi Maminsu.
"Nadai lura 'yarki batason muna kiranta da wannan sunan ko Aisha? Kuma ai girman kujerarta ne."
Ya k'arashe yana maida dubansa ga Ma'aruf wanda yaji maganar k'aninnasa tamkar an soka mishi allura a k'ahon zuci. Ya maze kawai, babu damar ya bar musu falon saboda Mami ta nuna tanason magana da shi. 
  Maganar Mami ta katse tunaninsa.
"Nikam zan hanaka zuwa gidannan Rufa'i, ka girma amma bakasan ka girma ba baka da aiki sai tsokanarmin 'ya?"
  Suna dariya hakan ya yi daidai da fitowar Bintu daga kicin. Mami  kirata.  Ji tayi kamar ta d'ora hannu a ka ta fasa, meyasa Mami zatayi kiranta a gaban wannan mutumin? Kodayake gaba d'ayansu ma haushinsu takeji ganin yanda suke faman dariya wato su kenan duniyar dad'i take musu. Tana mai tur6une fuska ita wai shagwa6a ta k'araso ciki, kai tsaye jikin Mami ta kwanta. Ma'aruf bai ko k'ara kallonta ba tun daga kallon da yayi mata fitowarta daga kicin d'in. A ransa har tsaki yayi, yarinyar kowane shiga ma idan ta so yin abinta takeyi babu wata damuwa kan hakan. Haka kawai baisan dalilin jin sosuwar rai ba.
   "Zaki fara ko? Aure fa muke shirin yi miki." Cewar Rufa'i. Ina, tuni Bintu ta kai wuya, ai kuwa ta fashe da kuka. Mami ta rungume kafad'arta, nan ta shiga yiwa Rufa'i fad'a, tace ya bar mata gidanta bazai zo ya hana 'yarta sakewa ba. Rufa'i jiki yayi sanyi ganin Bintu na kuka, shi kam gogan, ba zaka gane komai ba a fuskarsa. K'arshe ma ya mik'e ya ja gefe yana amsa waya.
  Nan Rufa'i ya hau bata hakuri.
"Haba tawan, kinsan bama haka dake. Ai ke tawa ce."
Da ire-iren haka ya samo kanta. 
  Ma'aruf na waya saidai jefi-jefi idanunsa kan sauka akan Bintu, har haushin kansa ya soma ji don bai ma san lokacin da yake kai duban gareta ba. 
   Ganin zaman falon bazai mishi bane, yasa ya d'auki wayoyinsa.
"Mami zan d'anyi wani aiki kafin wadannan su barmu muyi maganar."
  Anan ne Bintu ta saci kallonsa. Yayi kyau kam don kyau, saidai mamakinta bai wuce yanda batajin soyayyarsa ba kamar yanda Aisha ke son Ashir d'in. To kodai wannan 6ace 6acen ran da takeyi shine so d'in? 
"Oho." Ta bawa kanta amsa. Ashe batasani ba har ya fice. Dariyarsu Aisha ta maidota cikin hankalinta. Ta mik'e zaune sosai cike da masifa tace.
"Wai ke Aisha banason rashin mutunci fa, ai Yaya Rufa'in zai tafi ya barmu a gidan wallahi sai na rama."
Aisha ta had'iye dariyarta sanin halin Bintun da son ramuwar gayya wanda babu kyau. Gashi kuma tayi rantsuwa, tasan Bintu bata wasa da rantsuwa.
  "Allah Ya huci zuciyar..."
Kafin Aisha ta k'arashe, Rufa'i ya amshe.
"Matar Yayanmu."
  Aisha ta dubeshi ita kam ba abinda ta so fad'a kenan ba. Dariya suka sanya, a fusace Bintu ta fice daga falon zuwa can baranda wajensu Sadauki. Mami ta nunawa Rufa'i k'ofa.
"Tashi ka barmin gida." Ya mik'e yana dariya, daman ficewar zaiyi don a wannan karon ya daure ya bar Sadauki ya kwana."
  "Ayi hakuri Maminmu."
Da haka ya fice bayan ya d'auki ragowar ruwan robar da ya sha.
                     * * *
   Da daddare misalin tara. Bintu na kwance a d'akin Hanif, tana yi musu wasa tare da Sadauki, a rayuwa tanason yara. Idan Hanif ya kyalkyale da dariya itama ta dauki dariyar marar sauti saboda Mami ta haneta dariya mai k'ara ko yawan nan.
   Can kuma ta tsinci Sadauki a gefenta ya watso mata tambaya.
  "Anti, ai dai zaki tafi da mu gidan Uncle idan kunyi aure ko?"
  Ta dubi yaron da baifi shekaru biyu zuwa uku ba da mamaki.
  "Waya gayamaku zan je gidan Uncle?" 
    "Daddy."
Ta numfasa yayinda haushin Rufa'i ya k'ara kamata. Batace komai ba ta bagarar da zancen. 
   Ga Ma'aruf kuwa, al'ardarsa ce baya kwanciya batare da ya zo ya ga d'ansa yayi mishi addu'a ba. Wannan na d'aya cikin burikan da Ma'unsa ta ci idan har ta haifi bebinta. Burinta duk dare ta tofe yaranta da addu'a kafin bacci. Har kishi ya kamashi alokacin da tayi wannan furucin shi a dole yafiso ta so shi sama da komai don ya lura tun samuwar cikinta magana d'aya biyu, to fa zata sanyo abinda zata haifa 
   Hakan yasa shi k'ok'artawa wajen cikamata burinta, duk kuwa da cewar wani abin sai mace. 
  Yayi sallama batare da ko a ka ya kawo zai isketa a d'akin ba. 
  Ai kuwa sukayi ido hud'u tana kwance ta d'ora Hanif saman k'afafunta tana mishi wasa. Doguwar riga ce mai kauri ta bacci a jikinta. Kan babu kallabi. Kusan lokaci guda suka kauda kansu. Ta ajiye Hanif saman gado, da gudu ya rarrafa ganin zai fad'o yasa Ma'aruf d'aukarsa. 
  Bintu ta mik'e zata fita, ya dakatar da ita ta hanyar jifanta da tambaya.
  "Ina Atine ne?"
Ciki-ciki ta amsa.
"Ta je kicin dafa fidar Hanif."
Tana k'ok'arin sa kai ta fice ya k'ara tsaidata.
  "Ke zo nan."
Ranta yayi wani bak'i, ita fa ko ganinsa ma batason yi, mugu da shi.
   Saidai dolenta ta dawo baya batare da ta zauna ba. Haushin kansa ya ji a fusace ya soma magana.
"Wato tun yanzu raini ya gilma tsakaninmu, banda kin raina mutane ya zanyi kiranki ki tsayamin a ka?"
  Ta had'iyi miyau na takaici kafin ta zauna. Yayi shiru yana duban Hanif kafin yayi kwafa a fili ya dubeta.
  "Shine kika cewa su Abba ni kikeso ko?"
  Ta zaro ido ta dubeshi, idanunta ya kawo ruwa.
"Lallai ma, wallahi ni ban ta6a ma sonka ba, ni kawai..."
  Ta soma hawaye. Ya harareta, yarinya sai tsabar iyayi da yarinta.
  "Idan ba ke kika nunamusu kin amince da aurena ba, ta yaya zasuyi tunanin had'amu? Wai ke bakiga irin 'yan matana  ba ne? Kin ta6a cin karo da mai shekarunki?"
Ya d'an fasali kafin ya cigaba da magana bayan ya lalla6a Sadauki ya bar d'akin gudun kada ya kwashi rahoto don lura da yayi yaron akwai wayo. 
  "Me kika sani a aure ne? Bana tunanin ko girki da gyaran gida kin iya don ban ta6a ganin kina yin d'ayansu ba."
Sai kuma ya d'an ja tsaki.
"Kin d'ebo ruwan dafa kanki Bintu, ina tausayinki a gidana. Sai na kunce miki wad'annan notinan na kanki na saita miki su. Sannan daga yau na k'ara ganinki cikin shiga irin na d'azu sai na 6allaki, hakanan na kafa miki dokar d'ankwali, koda wasa na k'ara cin karo dake babu d'ankwali zaki d'and'ana kalar azabata."
   Ta mik'e ta goge fuskarta, gaba d'aya ta gama k'uluwa. Har zata fice sai kuma tayi tunani, ai idan ta barshi batare da ta ya6a mishi ba to fa bazata ji sanyi ba, gwara ta dunga ramawa kafin azo lokacin da ya riga ya zama miji gareta. Hakan yasa ta dawo da baya. Ya dubeta, ta kauda kanta gefe, ita ko kusa batason yawaita kallon kwayar idanunsa. Ta tsuke baki wanda ta saba yi idan zatayi rashin ta idon.
  "Dad'in abin dai nima k'ak'abamin kai akayi ba sonka nakeyi ba. Ni da ace zaka taimaka ka samu su Abba kace bana sonka da nafi kowa jin dad'i. Kaima kasan nafi k'arfinka. Maza nawa ne suke sona don ma soyayyar ba damuna tayi ba? Yanda kake shiryamin uk'ubobi nima haka nake shiryamaka don wallahi bana sonka, mugunta kawai kasani ba komai..."
  Mik'ewar da ta ga yayi ya sanyata fita a guje. Ran Ma'aruf ya 6aci ainun, tunda yake bayajin akwai macen da ta ta6a gasa mishi maganganu irin haka. Shakka babu Bintu ta k'ara rura wutar k'iyayyarta a zuciyarsa. Sai kuma alokacin ya k'ara jin wani kwarin gwuiwar aurenta, acewarsa, wannan kad'ai ne hanyar k'untatawa rayuwarta. Ya d'auki d'ansa ya fice zuwa sashensa.
  Da gudu ita kuma ta k'arasa d'akinsu. Anan ta tarar da Aisha dake faman laluben wayarta. A firgice Aishar ta dubeta.
  "Lafiya?" Bintu ta zauna bakin gado.
"Oho. Kekuma lafiya kika wani rikita mana d'akin?"
Aisha ta ja tsaki.
"Yauwa, bakiga wayata ba don Allah? Nasan Ashir yanata kirana bai samu ba."
  Bintu ranta yayi fari k'al. A fili kuwa ta ta6e baki.
"D'aukar miki waya nakeyi? Bangani ba."
  "Bani aron naki nayi kiransa."
Ta harareta "Kud'ina bana banza bane."
  Aisha ta ji haushi. Haka ta gama lalubenta, Bintu ta zura wayarta a cikin filo bayan ta kasheta ta kwanta ta rufe idanu. A ranta tana fad'in. "Yi iyakar bincikenki. Gobe kya k'ara kirana Matar Yaya."
   Tun tana sauraron shige da ficenta, har baccin gaske yayi awon gaba da ita.
  Sai a washegari ta damk'a mata da zasu fice zuwa makaranta.
  Bintu bata k'ara yarda sunyi arba da Ma'aruf ba, saidai fa acewarta ba tsoro bane!
                         * * *
             Bayan Wata d'aya da sati biyu....!!

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)
Chapter 15 · 0% Book details