← Book details Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 33

Sashe 19

Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sun isa har dab da k'ofar shiga hall d'in sannan Hashim ya faka.
"Ku jira kar ku fito, ina zuwa."
Ya fita daga motar. Ma'aruf ya dubeta, ba laifi kam ta yi kyau kamar ba wacce ya sani ba, duk kuwa da cewar ya ga wadanda suka fita a kyawun. Ya maida kansa ga kallon wajen. Yayi daidai itama ta juyo tana dubansa. Ji fa, namiji har namiji, amma zuciyarsa banda mugunta babu komai ciki.
"Jikina ya bani ana kallona."
Ta kauda kanta, a karo na farko tayi niyyar maida mishi martani.
"Ni me zan kalla a fuskarsa wanda babu shi a wajen..."
Bata kai ga k'arasawa ba sakamakon fisgo kafad'arta da yayi, wannan ya sanya fuskokinsu suka kusanci juna har suna jin hucin numfashinsu. Cikin kakkausar murya kuma mai k'aramin sauti ya soma magana.
"Ki bar gangancin gayamin dukkan wasu kalmomi da suka fito daga bakinki, idan kuwa bazaki kula ba zan ladabtar da bakinki wallahi."
Ya saki kafad'arta, ta matsa da sauri tuni ta soma k'ok'arin zubda hawaye. Ganin haka ya k'ara magana.
"Lallai kukanki na nufin na ci galaba akanki tun kafin a je ko'ina."
Jin abinda yace ya sanyata azamar share fuskarta.
"Ai ba kuka nakeyi ba. Kuma ma.."
Ta had'iye abinda tayi niyyar cewa tunano da abinda ya fad'amata a yanzun. Gane hakan da yayi ne, ya sanyashi murmusawa kawai baice uffan ba. A haka kuma sai ga Aisha tace su fito. Ashe kan 'yan matan da zasu shigar da su aka had'o. Can na hango dangin Rof na whatsapp a sun jeru suma babu wacce batayi anko ba, wannan ne dalilin da yasa dole aka barsu suka shiga jerin masu shigar da amarya.
Bintu ta fito, har aka zagayo da ita angon bai da niyyar fitowa. Shi kam hawayensa ya tsaya d'aukewa. Babu wacce ya tuno sai matarsa Ma'u. Masoyiya agareshi, bayajin har abada zai manceta. Allah Sarki rayuwa.
Hashim na shirin kwankwasa masa sai ya bud'|e ya zuro k'afafunsa ya fito. Bintu takaici ya hanata ma dubansa, idan yana wani yangar sai kace mace. Ita fa ta lura ajinsa har yayi yawa. Tayi kwafa a hankali kawai.
Ba tayi aune ba, sai jin tattausan hannunsa tayi a cikin nata, bai tsaya a rik'on ba har saida ya sark'esu wuri guda. Ta d'aga kai ta dubeshi, sai hasken flasher suka gani, tuni ya soma tafiya ta bishi cikin wani irin yanayi na sanyin jiki da rik'on ya janyomusu duka. A haka suke taku. Da ka gansu sai kayi zaton wasu taurari masu haske fiye da sauran.
Shi Ma'aruf yana takunsa cike da jin isa da k'asaitar shi d'in kyakkyawa ne kuma mai aji kwarai da kowace mace zataso ya kasance abokin rayuwarta. Ga Bintu kuwa, yangar daman ta zamto jiki agareta, haka tafiyarta take saidai ta yau ta bambanta da sauran. Sai wani shan k'amshi takeyi bata ko kallon mutane sosai ballantana ta damu da masu d'aukarsu hotuna. A haka har suka k'arasa mazauninsu.
Sai lokacin ta soma k'ok'arin zame hannunta ganin ba shi da niyyar sakinta. Shaf shima ya mance da wai hannun Bintu ya ke rik'e da, ya saki hannun bayan ya kalleta kad'an kawai.
Nan aka soma gudanar da shagalin biki, can na hango 'yan matan Zauren Karatu da DM har ma da Classic Ladies suna faman cashewa abinsu, kana ganinsu kasan basu da wata matsala asalima murna kwarai sukeyi game da wannan aure na Ma'aruf da Bintu. Bintu ta ja tsaki, wanda ya dira a kunnen Ma'aruf. Ya matso saitin kunnenta yanda zata ji abinda zai ce.
"Kika k'ara tsakin nan tsaka zaki zama."
Ta matsa gami da dubansa, ya d'aga mata gira kad'an da murmushin k'ularwa. Ta kauda kanta kawai tana mai tsuke bakin.
Can kuma aka tsaida kid'an, akayi addu'ar bud'e taro, kafin kuma a soma hada-hadar cin abinci.
Har aka kammala babu abinda Bintu ta sanya a bakinta sai lemo. Shi kuwa gogan babu laifi ya d'an ci abincinsa.
A k'arshe aka umarci Ango da amarya su fito domin yanka (cake), ya soma mik'ewa, abin mamaki ya k'ara mik'o mata hannunsa wanda ba k'aramin burge mutanen wajen sukayi. Ga iyalan Mami kuwa, su Rufa'i da Aisha abin ya basu mamaki matuk'a, haka suma su Atine su d'an dolo da suka san rashin d'asawar Bintu da yayanta.
Ta dubeshi, kallon idanunsa ne bataso, sanyaya jikinta yakeyi.
"Haba Amarya kina yanga, daure ki mik'awa angonki hannu." Cewar mai gabatarwar wanda ya bawa sauran jama'a dariya. Hum! Wai sai ga Bintu ta ji kunya. Ta d'aga hannunta ta d'ora a saman nasa ranta babu dad'i saidai jikin yayi sanyi. Ta mik'e suka soma saukowa. Mami ranta yayi sanyi matuk'a, addu'arta bai wuce yanda ma'auratan nan suka had'u ba, Allah Yasa aurensu yayi albarka.
Adda Ummi ce mai mik'a wuk'ar yanka cake, Ma'aruf ya kar6a. Bayan ya yanko ya sanyamata a baki, aka d'au sowa. Itama dakyar ta iya sanyamishi a baki bayan ta daurewa zuciyarta, abinda ya bak'anta mata bai wuce yanda har ya k'ara wani rik'o hannunnata ba.
Bayan sun kammala aka tsayar dasu, cikin fili, nan aka soma zuba musu ruwan kud'i. Can na hango matasan DM mazansu da matansu suna 6arin ruwan kud'i.
A haka aka tashi amarya ta dage Maminta zata bi. Ba takura kuwa, Mami ta ja ta zuwa motarta suka tafi tare da wasu k'annen Mamin.
Washegari aka gabatat da lakca, inda matan DDM da Khairin Nisa'i suka jagoranta. Da yamma aka shirya amarya za'a kai ta gidan mijinta...!
[7/19, 10:24 PM] ‪+249 99 950 1031‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)
Chapter 19 · 0% Book details