← Book details Bintu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 33

Sashe 2

Bintu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Anti Ma'u da Yaya Ma'aruf wai an d'aura musu aure?"
  "Lallai, baki da labari? Ai tun kafin ya tafi bautar k'asa akayi aurensu. Nan gaba zaayi biki. Ai Inna ta sani."
   Bintu dai bata gamsu da wannan kad'ai ba, saidai ta chanja akalar tambayar daga wacce tayi niyyar yi a farko.
  "To gayamin, ai Mami dagaske takeyi idan namiji ya kama hannuna zanyi ciki ko?"
  Aisha ta tuntsire da dariya, bata mantawa, itama Mami ta gayamata haka a baya, don kuwa ta zama budurwa tun tana da shekaru sha uku a duniya, watakila kuma hakan yana da nasaba da cimarsu da yanayin hutun da jikinsu ke samu, idan an ajiye wannan ma, Aisha Allah Yayi mata baiwar hankali, hakanan tana da ilimin addini daidai gwargwado, ana koyardasu duk wadannan hukunce-hukunce da sauran abinda ya dace su sani a addinance.
"Ke Bintu, ana fad'a ne fa kawai don a tsoratar. Ni ki kyaleni da wadannan tambayoyin, Yaya na jiranmu kada yayi fad'a." Ta wuce da sauri don d'aukar mayafi.
"Toh amma.." Ta katse maganar da tayi niyya sakamakon tunawa da gargad'in Yaya Ma'aruf gareta.
"Ki dauko mayafi, zamu biya mu sauke Anti Ma'u a gida sai mu wuce."
Dole ta nufi kayanta itama, bayan sun shirya suka fito, a tsaye suka sami Yaya Rufa'i da Mami, tana ba shi sak'o.
Aisha ta ja hannunta, "Zo muje wajen Anti Ma'u mu jira tana waje."
Suka fito, saidai a 'yar baranda suka iskesu da Yaya Ma'aruf, da sauri Bintu ta tsayar da Aisha suka la6e kad'an. A ranta tana fad'in asirinsu dai zai tonu yau idan itama Aisha ta ga sunyi wani abin.
Yaya Ma'aruf sukaji yana fad'in.
"Banyarda da wannan satar kallon ba na gulma, ke har yau kin kasa sakin jiki ki dunga kallon kwayar idanuna sosai..."

Basu kai ga jin k'arashen ba, Aisha ta figi hannun Bintu suka koma baya.
"Wallahi babu kyau la6e ba ruwana, kenan d'azu ma la6e kikayi ya kamaki ko?"
Ta harareta "Banza, so nakeyi kiga wani abu amma basuyi ba kika wani janyoni, zo mu koma kigani." Ta rik'o hannun Aisha, Aisha ta fisge ta k'ara janta baya.
"Wallahi baruwana, bazamu koma ba."
"Ke bakiji wani iskanci ba ma, wai ta kalli kwayar idanunsa. Nasan harararnan zaiyi mata."
Aisha tayi dariya.
"Ashe na fiki sanin abubuwa Bintu, lallai ke da sauranki. Ai kallon soyayya yake nufi. A shirin RAI DANGIN GORO naji Ahmad Isa yana fad'a, wai da saurayin ya kalleta saida ta ji yarr, wai ta sauke idanunta saboda ba zata jure kallon kwayar idanunsa ba."
Bintu ta tuntsire da dariya. Yi takeyi tana k'arawa.
"Rainin hankali. Kalleni to mugani."
Ta gwalo mata idanuwanta, Aisha ta ja tsaki tana dariya.
"Ke dallah, sai da namiji wanda kakeso."
Bintu banda dariya ba abinda takeyi don abin dariya yake bata, suna tsaye sai ga Yaya Rufa'i.
"Au, maimakon ku shiga mota kuka tsaya anan?"
"Yauwa Yaya Rufa'i. Muga ida..."
Da sauri Aisha ta toshe mata bakin tana dariya.
"Ke wallahi ba'a sirri dake. Sirrine fa."
Yaya Rufa'i yayi dariya.
"Menene abin? Yau kuma ni kuke yiwa 6oye-6oye?"
"Yaya ba haka bane, sirri na bata ai babu kyau fad'awa wani kuma."
"Shikenan ai, ku muje, inaso naje amso d'inkuna na ne."
Suka kama hanya, har lokacin Yaya Ma'aruf na tsaye da Anti Asma'u. Yaya Rufa'i ya tambayeshi "To, ko mu tafi zaka kaita?"
Yaya Ma'aruf ya gyad'a kai, "Yeah kuje kawai."
Bintu ta kalleshi, ya bita da harara ta dauke ido. Wai wannan idan Anti Ma'u ta k'ura mishi ido, ai sai ya sanya ta firgice.
Koda sukaje nan ma Bintu saida ta tsaya ruwan ido, a k'arshe ta za6o mai shegen tsini, duk yanda Yaya Rufa'i da Aisha suka so hanata d'aukarsa ita kuwa ta dage lallai shi takeso. Dole suka kyaleta, ganin haka ya k'aro mata da wani flat mai kyau da rangwamen kud'i.
Murna ya cika Bintu har gwalo take yiwa Aisha.
"Wani abin ma sai gobe."
Aisha tayi dariyar mugunta "Zakiyi bayani ne."
* * *
RANAR SALLAH...!

[7/20, 9:56 PM] Aysha Abe:  ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)

<<04>>

Tun bayan sallar asuba, Bintu bata koma bacci ba.  Zama tayi tare da su Mami dake aikin girke-girken sallah tana tayasu da hira. Ko a k'auyensu babu abinda take tsinanawa innarta duk kuwa da faman da Innar zatayi, saidai tayi ta gaji. To zuwanta ne ma wajen Mami abin ya d'anyi sauk'i.
   "Mami, wai bazamu idin ba?"
Mami wacce ta riga ta gama gundura da wannan maimaicin tambayar da Bintu ke yi mata, ta bata amsa a fusace.
  "Bansani ba, ke wai bakisan abinda ya kamata ba? Tashi ki bar nan tun kafin na 6ata ranki."
  Ta mik'e tana zum6ure baki, Atine da Magajiya masu taya Mami hidima suna dariya.
  Tana shiga d'aki ta nufi wajen kayanta dake a goge a ninke.
   Bayan ta gama shafasu ta janyo takalminta ta gwadashi a karo na shida tun bayan da aka siyo.  Kwas kwas d'in da takalmin keyi ne ya tayar da Aisha daga bacci. Ta dubeta tana mutsistsika idanu kafin ta ja tsaki tayi mik'e.
  "Kedai wallahi kamar na kwasheki da mari nakeji, duk kin wani ishi mutane tun siyo takalmin nan."
  "Sai ki mareni idan kin isan."
Cewar Bintu tana k'ok'arin dafe bango ganin tana neman kaiwa k'asa.
   "Ki tashi ki shirya, Mami tace Abba ya shirya."
  Ai da jin haka Aisha ta mik'e zaune.
  "Dagaske? Ke meya hanaki wankan?"
  "Kaya kawai zan saka."
Hakan da ta fad'a yasa Aisha mik'ewa ta fad'a band'aki.
  Bayan fitowarta, itama ta soma k'ok'arin shiga. Daman batayi, wankan dai tafiso Aisha ta soma."
       K'arfe bakwai, sun gama shiri tsaf. Bintu dole ta bari Aisha tayi mata kwalliya da d'aurin d'ankwali, saidai duk da haka, saida tayi d'igo a goshinta hakan bai hanata fitowa tsaf tayi kyau ba. Shadda ce a jikinsu fara tas, ta sha aiki mai duwatsu. Aisha sai kallon Bintu take.
  "Ke sai naga kamar fa kin fini yin kyau."
  "To uwar ba'a, yanzun ma shi kikeyimin? Ke da kike fara tas, menene abin gani a yaba wajen bak'ak'e. Ai dole ma nan gaba na soma kwailin."
  "A wane gidan?" Suka tsinci muryar Mami wacce sam basu kula da shigowarta d'akin ba kasancewar k'ofar tasu a bud'e take. Ta k'araso ciki, itama shaddar ce a jikinta saidai kala da ta bambanta don ita ruwan k'asa ta sanya, iri d'aya da mijinta, bawani ado sosai ta yiwa fuskarta ba. Sunyi zaton fad'a zatayi, sai kuma ta saki fuska tana dubansu.
  "Inye, kaga 'yanmatan Abba, to ko ku fa? Bintu har kinso ki fini kyau ni d'inma. Kalarki mai kyau ce kada na k'ara jin kinyi zancen wani shafe-shafe."
  Bintu ta amsa da toh tana mai washe baki na jin dad'in yabon da Mami tayi gareta.
   "Toh sai ku fito ga 'yan uwanku da Abbanku duk sun kammala shiri."
  Kowaccensu ta dauki mayafinta wadatacce ta yafa. Aisha ta dubi Bintu baki bud'e ganin tana k'ok'arin zura takalmi.
  "Wai dagaske takalmkn nan zaki sanya?"
  "Me zai hana kuwa? Lallai ke d'innan kina wasa da Bintu."
  Tuni ta zura tana k'ok'arin daidaita tsayuwarta. Aisha ta girgiza kai. "Wallahi ki chanja ki sanya d'ayan nan, ina jiye miki ki fad'i."
  "Jikinki ko jikina? Kudai 'yan birni kun maida mutanen k'auye wasu da basu da wayewa. Tunda ke bazaki iya tafiya da shi ba sai ki bar wad'anda zasu iya suyi ai."
Daga haka ta nufi k'ofa tana taku gaba d'aya a takure.
"Ke muje."
Suka fito.
A nan farfajiyar gidan suka tarar da su Mami na k'ok'arin shiga mota. Abba yayi murmushi ganinsu. Suka gaisheshi.
"Lallai, yaran Abba sun fito. Kamar ba ku ba." Sukayi dariya kawai.
Ita dai Bintu da sauri ta fad'a mota sakamakon takalmin dake neman kayar da ita. Mami ta girgiza kai.
"Bakya ji Bintu, kinason wahalar da kanki."
Yaya Rufa'i yana dariya yace "Barta Mami, jiki magayi."
Bintu ta d'ago ido da zummar kallon Yaya Rufa'i, saidai cikin rashin sa'a suka had'a da Yaya Ma'aruf, abin mamaki yau kam babu hararar, kallon sak, kallo d'aya ya maida kansa ga tuk'i. Motar tayi shiru sai kabbara da kowanne keyi a hankali, wato(Allahu Akbar Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamd) kamar yanda sunnah ta koyar.
Bintu wacce bata iya sosai ba, sai mus-mus da baki. A karshe sai ma ta matsa daidai kunnen Aisha.
"Ke, wallahi Yaya Ma'aruf yayi min kallon arziki yau. Yayi kyau sosai."
Aisha ta harareta kawai, hakan yasa ta dauke kai tana kalle-kallen gari. Takalmi kuwa tuni ta tu6eshi tana hutawa.

[7/20, 9:56 PM] Aysha Abe:  ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar 
         (July...2016)
Chapter 2 · 0% Book details