← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 29

Sashe 9

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harirah ta shigo ta tsugunna tana gaishe da su Ummee, Ummee ta masa tace"Baiwar Allah abinda mu kaji gaskiya ne ko kuwa gulmar kawai ta kawo ki?" Harirah ta gyara zamanta ko kunya babu ta kwashe duk yanda su Salamatu suka tsara aurar da Ma'azzara tare da 'dan Haliru warsu mai farfadiya kuma gurgu harda uwar garke da aka siyar harda karin karya wai har sun sayi goron d'aurin aure.
Adamcy yanajin bayanin Harirah ya zaro idanu yace" Ashe kuwa gidan yarin Agadez zaiyi bak'i wallahi a daran nan zan makasu koti yanzu zan shigar da karansu police sitetion kafin gobe mu wucce Agadez, wayyo Allah na!! Agaishina kin bani Amana mai wuyar riko meyasa? Kika bani Amana meyasa da zaki mutu kika hada hannuna da nata kikace amana, ni ban saba da matsala ba amma kin hadani da ita kin mutu kin barni wannan 'dan abun za'ama aure ta yaya kuma ma da mahaukaci oh my God Ummeena ni fa bana son hayaniya kin sani....." ummee tace Haba Adamu ka nutsu dan Allah karka ga laifin Agaishina dan ta baka amana dama can haka Allah ya tsaro kaine zaka riketa, ita nata isarawa ce tayi kayi hakuri."
Ma'azzara tana jin abinda Adamcy ya fad'a ta kara fashe da da kuka tana boye kanta jikin Hussaina Hussainar kanta kuka take.

Haushi ya cika Adamcy ya buga masu tsawa su duka biyun sai da suka firgita har Hussaina Harirah kuwa tuni takai bakin kofar parlo a guje.
Adamcy ya isa gaban kawu Hashim ya kama hannunsa yace "Kawu tashi muje mu dawo kuma ku taso muje." Ya kalli su Hussaina Ma'azzara tanajin haka ta saki Hussaina ta mik'e ta kwasa bedroom da gudu tana kuka tana cewa"Wlh uncle naki bana zuwa." Adamcy ya bi bayanta cikin tsawa ya ce"ke ina wasa dake ne?" Ummee ta tafa hannunta tace"oh ni Ummee kai Bature wlh karka saka yar mutane ta suma fa a banza." Amma Adamcy bai saurareta ba yabi bayan Ma'azzara ransa a 'bace yasin nagaji typing wuya😩.............✍🏻

*Na kudi Ne kan farashi Nera 200 kacal +22792589446/ +22796515805*

Daga alkalamin *💃🏻Sweet Baby💋* ummu Fareesa yar mutan Niger😍

*💖BANI DA GATA💖*

*MALLAKIN*
👇🏻
```Real Ladingo Sweet Baby💋```

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Chapter 7*

Ma'azzara tana shiga zata rufo kofar Adamcy yay zafin nama ya rik'e kofar ya shigo, ransa a 'bace ya damkota ya watsa mata wani mugun kallo, cikin cool voice yace " Ke ina wasa dake ne? Ni sa'anki ne da zan maki magana ki shigo ciki da gudu , wato baki d'aukeni mahaifi ba kamar yadda Agaishina tace ko?" Ya idar da maganar a tsawace.

Ma'azzara taji tsoro sosai yadda Adamcy yay mata tsawa ga damk'ar da yayi ma kafadarta.
Kuka ta saki tun karfi ta fada kirjinsa ta zagaye hannuwanta k'ugunsa, cikin shashekar kuka tace"Dan Allah My uncle kayi hakuri na d'auke ka fiye ma da hakan idan ana d'auka, na tuba bazan karaba gabanan ko wuta kace nazo ka nasani zanzo wlh zanzo uncle kayi hakuri, yanzu duk ka canza min da ba haka kake min ba a mafarki lelena kakeyi har da goyona kake kana min wannan abin da naga kama Aunty a cikin mota, ka dorani saman doki muna yawo cikin franni tsanwaye shar , amma yanzu ka canza uncle." Ta karasa maganar tana sakin kuka mai cin rai tana kara shigewa jikinsa.

Adamcy ya zaro idanu ya dafe kansa da hannu guda, ya zuba mata manyan lumsassun idanunsa cike da mamaki da takai ci, yace" Ke bana son karya yaushe na sanki a ina kika tab'a ganina?" Ya fad'a yana saka tattausan hannunsa ya janyeta daga jikinsa ya kama hannunta suka nufi saman kujera ya zaunar da ita, ya zauna shima ya kuma had'e fuska yace"Ke imun shiru bari kukan bana son hayaniya fa, ko yanzu na kai ki can gidan Salamatu....." Ma'azzara ta katseshi ta hanyar rik'e hannunsa duka biyu tana kallonsa hawaye na zuba idanunta tace"Uncle wlh na daina kayi hakuri kar ka kaini, Agaishana kai taba amanata."

Adamcy ya janye hannunsa ya fesar da isakar bakinsa waje, sai a akan fuskar Ma'azzara ta kalleshi tana goge hawaye ta saki murmushi tace"Uncle wlh isakar bakinka sanyi ga kamshi, wane irin turare kake saka masa nima ka bani wlh shiyasa a mafarki idan kana shan bakina nakejin dadi sosai , uncle har fa mamaki nake nace ko dai kai mayene mutum yasha bakin mutum baiyi amai ba...." Tsawa Adamcy ya buga mata wacce yasa ta dawo nutsuwata, jikinta yana rawa ta matsa gefe tana raraba idanu.
Adamcy ya mik'e tsaye yace"wlh duk ranar da naji kin sake irin wannan tambayar har Hussaina taji , wlh zaki sani ba ruwana zata zane ki tunda ke bakida hankali mahaukaciya ce yaushe kika sanni? Tashi maza muje gidan megari." Ma'azzara da tsoro ya cikata har wani rawa jikinta yake zufa ya wanke mata fuska amma ta dake ta mik'e tayi k'asa da kanta kamar munafuka tana wasa da yatsarta hannunta.

Adamcy yana isowa ya kama hannunta suka fito parlour.

Hussaina ta mik'e ta nufo gunsu Adamcy yace "Kawu Hashim umma Saratu ku tashi muje mu dawo Hussaina zakiji ne?? Hussaina ta d'aga kai tace"Eh mon trésor ina zuwa" Ma'azzara ta janye hannunta daga na Adamcy ta rik'e hannun Hussaina, sai cicira idanu take tana bin kowa da kallo.
Ummee tace"Bature kayi hakuri mana har gobe ka dauki hukunci yanzu dare yayi." Hauwa'u tace"Ai Ummee tsoro ake kar fa su d'aura auran ai kawai suje kawai." Ummee ta ce" To da wata ya wannan kuje kawai" Adamcy ya iso gaban Ummee ya rankwafo ya mata kiss a goshi yace"Sai mun dawo." Murmushi tayi tace" Allah ya kawo ku lfy" Adamcy yace"Ameen ku muje to". Hussaina daman da hijabi a jikinta suka fito baki dayansu tana rik'e da hannun Ma'azzara.

Hussaina da Ma'azzara da Saratu suna bayan mota Adamcy da kawu Hashim suna gaba, direct gidan megari suka nufa.

Suna zuwa Adamcy yama megari bayanin komai ai kuwa megari ya tusasu a gaba har gidansu Salamatu.

Lokacin da suka je har ta kwanta Haliru yana kofar gida a kwance a tabarma megari ya dirka masa duka a baya, ya zabura yana ihu megari yace"Wato zaku aura da yarinya ga mahaukaci ko?" Haliru yace"inji wane munahikin karya ce muda bata hannunmu ina ruwanmu da ita." Megari yace"Ka tabbatar karya ce har uwar garke da kuka siyar ta hidimar biki?" Haliru ya zaro idanu ya shiga tafa hannuwa ya mik'e tsaye yace "Allah ya tsinewa yan zaune gari banza wanda basu da aiki sai gulma da tsegumi, ta yayama akayi maganar taje kunna yan tsirku bari na kirawo Salmai tamin maganin ku, ai in har shugaba ya zama lalatacce a gari To fa an kar." Ya idasa maganar yana shigewa cikin gidan ya nufi kewayan Salamatu.

Ita ko Salamatu ta baje saman tabarma sai bacci take ta saki baki da hanci sai tusa take saki buuurrr buuuttt.😂 Haliru yana jin karan tusa biyu kafin yaja burki yace"Hegiyar tayi toshe-tushe ba aiki sai tusa kai Salamatu malam musa na hakuri dake wlh, kai Subahanallahi tirrr. " ya fadi yana shirin d'aga dan zanan da suka saka tsakanin kewaye su, lokacin malam musa ya fito daga bayi dan tusar Salamatu ta ishesa yaga Haliru zai d'age labule yace"Haliru lfy dai ko a daran nan?" Haliru ya yamutsa fuska yace "Yauwa taso bodara kace anzo har gida aci mana mutunci, tazo ta wanke min su tass." Malam musa yace"Asha to bazata ba tunda ku bakuda aiki sai masifa da jaraba, ni nake da iko da ita bazata ba wuce ka bani guri." Haliru yace" Nima walkine dai dai k'ugunsu bari na koma, kai kuma kaji da tusarka ma ta isheka." Yana gama fad'ar haka ya juya ya fice.

Malam musa ya girgiza kai ya shihe kewayansu.

Suna tsaye suna jiran Haliru da Salamatu, sai gashi ya fito yana cewa"Kuyi duk abinda zakuyi ba'a fasa auran ba" Megari ya bude baki zaiyi Magana... Adamcy ya katseshi ta hanyar cewa" Ok kuna nufin gaskiya ne zaku aurar da ita yarinya karama da ko ciwon kanta bata saniba, to bari kuga yadda zamu kwashe daku, yanzu abinda nake so da kai zaku janye auran ko sai na kaiku gaban yan sanda tukun?" Haliru yayi dariya yace"yaro yarone watakan mune za'ayiwa barazana ko to baza mu janye ba, kai Salamatu tafi ku iya shege fa." Megari ya zaburo zaiyi Magana a karo na biyu Adamcy ya katseshi yace "No barsu bari mu fara wasan a daranan." Ya fada yana ciro waya daga aljihun wandon sa ya shiga ma'adanar numbers ya nemo wata number yay dailing ya koma gefe Hussaina ta bishi a baya.
Tana ringing aka d'auka Adamcy yace"Asp yay slm Adamcy ya amsa yace"Asp inaso a kayi kira nan Audaras kasa a turo mota guda cike da yan sanda zamuyi maganin wasu mutane, nan bayan gidan megari ne kwana ta farko akwai katon dakali akofar gidan, ni ban san Asp da yake nan garin ba." Asp Aseem yay murmushi yace"Ok na zata daga nan Agadez ok bani 10 minutes zasu iso." Yana gama fadin haka ya tsinke kiran ya kira ya bada umarni.

Ma'azzara tana sharb'al hawaye tabi su Hussaina da kallo tana jikin Adamcy ta kwantar da kanta akafadarsa tana magana amma ba'a juyowa, tsoron Haliru ya cikata tayi saurin matsawa kusan Saratu ta lab'e a bayanta. Hashim yace"a jiye hankalinki babu abinda zasu miki" Haliru ya zabga masu harara yace"Wlh sai kinci gidanku hegiya munahika mai ruwa da bak'ake'n mayu, idanu zuru-zuru zo nan dan babanki."
Megari yace"Watakon Haliru ka girma babu hankali ko yanzu kafison ya kirawo motar iko tazo ta kwasheku har gida?" Dariya Haliru yayi yana tafa hannu yace "Mu mune Audaras megari kaja girman ka fa tau". Megari ya jinjina kai yace" Zaku sani hummm."
Chapter 9 · 0% Book details