← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 29

Sashe 5

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyar Adamcy na tsananin suya da mugun radadin kukan da take yi, ya taka da sauri ya isa gabanta ya zauna a gefenta ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam a kirjinsa yana lallashinta, Ummee na shafa kanta da bayanta itama tana lallabata da bata baki, sai da ƙyar da sudin goshi sannan suka samu tayi shiru bayan taci kukanta sosai ta gode Allah, a hankali ta share hawayenta tana sauke ajiyar zuciya tana jan numfashi ta kara lafewa a jikinsa, dan sosai taji mutuwar Gaishina ta taba zuciyarta ga wani tsantsar tausayin Ma'azzara dake manne a zuciyarta. Ganin tayi shiru yasa ya dan janyeta a jikinsa ta koma jikin Ummee ta kara lafewa ta rumtse idonta tana jin wani iri a jikinta, ya mike a hankali ya fice daga ɗakin ya nufi kofar gida wajen zaman makoki ya zauna gurinsu Harun da Gumar da Hashim suka kara yiwa juna ta'aziyya sannan suka ci gaba da karbar gaisuwa gurin jama'a da suke zuwan musu, daurewa kawai Adamcy yake yi, amma gaba ki daya hankalinsa da tunaninsa duk sun tafi, tunanin yanda zai iya rike amanar da akabar masa kawai yake yi, wanda yake ji a ransa da zuciyarsa kamar an daura masa nauyin duniya ne da abinda ke cikinta duka a kansa.

Haka yana nan zaune a daddafe har aka kira sallar Azuhur a masallaci, suka tashi sukayi, sannan ya shiga cikin gida yayi wanka ya canza kaya ya fesa turarukansa masu tsananin ƙamshi da daɗi, nan Husaina ta kafa masa rigimar ba zai fita ba ta hanasa sakat sai da ya kamota ya lallasheta yayi mata romance ya lallabata har tayi bacci sannan ya kwantar da ita ya sakar mata kiss a kumatu da goshinta ya juya ya fice daga ɗ'akin ya koma kofar gida rumfar zaman makoki.

Sai bayan La'asar sannan ya sake komawa cikin gidan ya yiwa Husaina wanka yasa ta daura alwala suka fito tayi sallah, ya shiryata tsab tayi kyau sosai shima ya sake kayan jikinsa suka nufi asibiti gurin Ma'azzara.

Suna isa direct ɗakin da aka kwantar da ita suka nufa, lokacin da suka shiga ta farka likita na tsaye a kanta tanata fizge-fizge tana zuba ihu tana kiran sunan Uncle da Gaishina, da gudu Husaina ta nufeta ta kamota jikinta tana ƙoƙarin lallashinta ta sake fizgewa taƙi tsayawa ta ci gaba da fizge-fizgen da takeyi tana kiran sunan Gaishina da Uncle tana kuka, cike da damuwa Husaina ta kara kamota jikinta tana lallashinta ta sake zamewa taƙi saurarawa, a marairaice Husaina ta ɗago tana kallon likita cikin tsantsar damuwa tace "Dr dan Allah kayi wani abu akai mana..?" Likita yana kallonta da damuwa a fuskarsa yace "Tun ɗazu faman da muke tayi da ita kenan tun da ta tashi amma taki tsayawa... sai kiran Uncle take." Ya faɗ'a yana juyawa ya kalli Adamcy yace "Kazo dan Allah kayi mata magana zata tsaya.."

Wani irin haushi da tsantsar takaici Adamcy yaji a zuciyarsa, shifa baya son sakakkun yara shagwaɓaɓɓu dan yaga alamar yarinyar kuma ta fiye sangarta da shagwaɓa da yawa ya buɗe baki zai mata tsawa kenan ya tuna da amanar da Gaishina ta kamo hannunsa ta damƙa masa, take sai jikinsa yay sanyi ya matsa a hankali kusa dasu ya zauna a bakin gadon, ya karb'eta a hannun Husaina ya riƙe hannunta a hankali ya ɗan dora kanta a kafad'arsa cikin lallashi da kwantar da murya yana bubbuga bayanta yace "To yi shiru ga Uncle d'in naki yazo... Mene ne.?" Jin muryar Adamcy da tayi yasa ta tsaida kukan nata cak tana sauke ajiyar zuciya ta kara nitsa kanta a ƙirjinsa tana shasshekar kuka haɗe da sauke numfashi, cike da ƙyanƙyani yasa hannu ya tattare mata gashin kanta mai tarin yawa da santsi ga tsayi ya daure mata, sannan ya gyara mata zaman hijabin jikinta, Husaina sai daɗi take ji tana sakin murmushi tace "Mon trèsor ko kai fa. Wallahi naji daɗin hakan da kayi, ka lallabata." Ta faɗa tana jin daɗi sosai a ranta.

Ma'azzara kuwa tunda dai taji muryar Adamcy a kusa da ita hankalinta ya kwanta tai luf ta kara lafewa sosai a jikinsa, shi kuma a hankali cikin ƙyanƙyami yake shafa kanta mai laushi a zuciyarsa yana jin tsananin ƙyamar taɓa jikinta da yake yi sosai yake jin ba daɗi a ransa, amma ya zama dole ne ya kula da ita dan babu yanda zaiyi saboda ta zama amanarsa.

Ganin ta natsu tayi shiru yasa Dr ya sake dubata yaga bata da wata matsala, Adamcy ya ɗago yana kallon Dr yace "Ko zaka iya sallamar mu idan babu wata matsala?" Jinjina kansa Dr yayi yace "Eh dama kaman abin ya firgita ta ne tayi doguwar suma, amma bata da wata matsala zan iya sallamarku." A hankali Adamcy ya janyeta a jikinsa ya matsa gefe Hussaina ta matso ta rungumeta, shiru tayi tana bin Adamcy da wani irin kallo kamar zata lashesa, dan ita babban burinta kawai ta kasance tare dashi, har wani farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta wata natsuwa na saukar mata a gangar jikinta, sai a lokacin ta tuna da mutuwar Gaishina abin ya dawo mata, tana jin mugun ciwo da zafi mai haɗe da raɗaɗin baƙin ciki a zuciyarta ta sake rushewa da kuka ta fizge jikinta daga jikin Hussaina tana kuka haɗe da ihu tana fadin "Gaishinata...Wayyo Allah Gaishinata.... Wayyoooooo Gaishina ta.." ta sakko da mugun gudu ta rirrike Adamcy a kiɗime tana "Uncle ka gaya min da gaske ne ta rasu..?" Wani iri yaji a zuciyarsa a hankali ya kamota ya riketa yana kallon fuskarta cikin sanyin muryarsa da lallashi yace "Kiyi hakuri, dan rasuwa ta rasu, amma insha Allahu zan riƙe ki amana kamar yanda Gaishina ta bamu amanarki nida Hussaina..." Ya fad'a yana kamo Hussaina jikinsa suka haɗu su uku suka rungume juna, Ma'azzara tana kuka Husaina ma na kuka, da ƙyar Adamcy ya samu ya lallaɓasu, likita ya sallamesu, yana riƙe da hannun Husaina, Husaina na riƙe da hannun Ma'azzara suka fita, suka shiga mota suka nufi gida.

Ma'azzara na zaune a baya Adamcy da Hussaina na gaba yana riƙe da hannunta ɗaya yana tuƙi da hannu ɗaya, yayinda itama Husaina har lokacin take riƙe da hannun Ma'azzara dake ta rasgar kuka tana kiran sunan Gaishina, a haka har suka ƙaraso gida, Husaina ta kaita part d'insu ta had'a mata ruwan wanka ta kaita toilet tayi wanka ta wanke mata gashinta ta gyara mata jiki, ta dauko mata kaya a cikin nata ta bata ta saka, suka ki shigarta sai da ƙyar saboda sun mata kaɗan sosai, domin ita Husaina bata da jiki Ma'azzara ta fita ƙiba, duk surarta ta fito 'yan ƙananun matasan nonuwanta duk suka fito, ta gyarata sosai ta shiryata tsaf ta bata abinci taci sosai ta ƙoshi sannan ta kama hannunta suka nufi part d'in Ummee.

Suna zuwa Ummee ta riƙota ta rungumeta a jikinta tana jin tsananin tausayin Ma'azzara a zuciyarta, ta fara lallashinta cike da nuna tsantsar kulawa tana fada mata daɗaɗan kalamai, kan tayi haƙuri ta yiwa Gaishina addu'a itace kaɗai abinda take bukata daga gareta, tana gyaɗa kanta wasu hawaye na sake zirarowa kan fuskarta.

Da misalin karfe tara na dare su Hussaina na zaune a parlo da yan tsirarun mutane Adamcy ne ya shigo waya manne a kunnansa yana sakin murmushi, ya magana cikin siririyar murya sa tamkar baya son maganar ya zauna kusan Ummee, ya dora kansa a kafadarta cikin harshen fransanci ya ce "ma tant ga Ummee kuyi magana". Murmushi ummee tayi ta gano Rukaiyya ce mahaifiyar Hussaina.

Amsa tayi ta kara a kunnanta tana sakin murmushi. Ma'azzara kuwa tana jikin Hussaina tana bata labari mai dadi, amma Ma'azzara tayi nisa aduniya kallon Adamcy ko kiftawa bata yi Adamcy ya kai kallonsa gefen su Hussaini karaf suka hada idanu da Ma'azzara ta kafesa da idanu.
Kansa ya dauke gefe k'asan makoshi ya furta "Wannan inaga mayya ce tirr ina dalili". Ya fad'a yana kai kallonsa kan Hussaina wace ta dukufa tana ma Ma'azzara hira.

Haushi ya ciki Adamcy kenan bata ta tashi ma mik'ewa yayi tsaye, ya zura hannunsa aljihu ya ce"mon Bebe zo na ganki". Hussiana sai lokacin ta d'ago ta kalli Adamcy taga fuskarsa murtik ba walwala da sauri ta janye Ma'azzara ta mik'e tsaye ta nufi gunsa tana langwab'ar da kanta. Adamcy ya nufi kofar fita tabi bayansa da gudu Adamcy yana dab da fita Salamatu ta shigo da sallama, Adamcy ya amsa yana kallonta ganin suna yar kama da Ma'azzara tsaye tayi daga inda take, ta kalli Adamcy tace"Nazo na tafi da Ma'azzara ne ni kanwar Babanta ce uban mu daya dashi bazamu barta cikin daula ba taje ta manta da butar ubangaji, dan haka ke taso mu tafi ta nufi gurin Ma'azzara tana zaro mata idanu.

Ma'azzara a mugun tsorace ta mik'e jikinta na b'ari da gudu tayi kan Adamcy tana kiransa "Uncle ka ceceni karka bari su tafi dani" Adamcy ya warema Ma'azzara hannunsa ta kara so ta fada jikinsa tana kuka, jikinta sai kyarrrrma yake dan tana mugun tsoron Salamatu.

Adamcy ya maida hannunsa ya zagaye bayanta ya watsama Salamatu mugun kallo wanda yan hanjinta saida suka kada, amma saboda tsabar dauriya da mugunta da take cinta, dan yau ta tsara naunin azabar da zata mata ta ce" Haliru ku shigo a yita ta kare wlh sai sun bamu yarmu haka kawai salon a sata ta manta da Ubangijinta wlh sai kun bamu yarmu saboda.... tsawar da Adamcy ya mata ne, yasa sauran maganar ta mak'ale mata..................✍🏻
Real Ladingo ce😅

*Na kudi ne Kan fara shi Nera 200 kacal +22792589446/ +22796515805.*

Daga...✍🏻ummu Fareesa💋💋💋

*💖BANI DA GATA💖*

*MALLAKAR*
👇🏻
```Real Ladingo Sweet Baby```

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Chapter 5*
Chapter 5 · 0% Book details