← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 29

Sashe 12

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace"Waye kika raina tun tafiya batayi nisa ba ni sa'anki ne?" Da sauri ta girgiza kai. Yace "Ok raina nine kikayi?".... Hussaina ce ta fito cikin shiri tasha wani uban less bak'i mai masifar kyau da tsari dinkin riga da siket cif dai-dai ita ta yafa mayafi bak'i takalmi bak'i jaka bak'a.
Ta zaro idanu tace"Wayyo mon coeur me kuma amana tayi dan Allah." Adamcy ya harareta yace"wlh Hussaina zanyi mugun sab'a maki kece zaki saka yarinyar nan ta renani, kuma na hanata kallon film amma kike barinta ko? slm nayi bata jiba tana kallo sai da na kashe kayan kallo, abin ta tambayeni me tayi taban hakuri ta sakamin kuka zata neman ki kizo ki bani kashi." Hussaina ta gintse dariyarta tace"Haba Yayana yi hakuri tuba muke kanmu bisa wuyanmu." Tsaki Adamcy yaja ya kalli hadaddan agogon hannunsa ya zaro idanu yace"Oya maza muje lokaci ya kusa." Ya fadi yana fita ya kirawo megadi ya fitar masu da bayansu, Hussaina ta kama Ma'azzara tana lallashinta suka fito.

Hauwa'u na gaban motar Adamcy ashe gidanta yaje ya daukota su Hussaina suka shiga baya yaja motar suka bar gidan mijin Hauwa'u Faisal na saman mashin yana biye dasu har Airport dan shi zai dawo da motar da matarsa Hauwa'u.

Suna zuwa basu jima ba aka fara sanarwa matafiya daket Jiddah ta rabu da Adamcy sai kuka take saida ya lallasheta tayi shiru ya sakata dariya kafin yake barinta, su shiga jirgi faisal ya kamota suka nufo gida yana lallashinta. Ummee kuwa sai kiran Adamcy take suna hira tana ta masu Addu'ar sauka lafiya.
Wajan hawa jirgi da Ma'azzara daket Hussaina da Adamcy suka rik'eta sai makyarkyata take.
A tsakiyar su suka zaunar da ita saboda a mugun tsorace take sai hawaye take.
Adamcy yaja tsaki yana harara ta yace"Bakauya kawai." Bata dai kula shi ba ta damke hannunsa da na Hussaina.

Karfe shida da minti goma cif jirgin su ya cira zai tashi ai kuwa Ma'azzara ta saki kuka hade da ihu jikinta sai kyarrrrrma yake jama'a sai kallonsu suke yana cirawa sama kuwa da karfin nan ta ida rikicewa hajijiya ta fara daukarta tana kwarara ihu Adamcy ya toshe mata baki da hannunsa ya rungumeta jikinsa yana cewa"ni kam naga ta kaina a rayuwa haba ina dalili ni fa ban saba da fitina ba.........✍🏻

*Na kudi Ne kan farashi Nera 200 kacal +22792589446/ +22796515805*

💃🏻Dag Alkalamin *Real ladingo Sweet Baby* ummu Fareesa😘

*💖BANI DA GATA💖*

*MALLAKIN*

*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻

*DEDICATED TOO*

MY HABIBTY SA'ADATU ISHAQ YAR MUTAN JIGAWA.
*ONE LOVE😘*
*Kiji dadinki ta wajena shafin duka naki ne sai kinso group matasa zusu karanta😉😜*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Chapter 9*

.....Lallashinta Adamcy yaci gaba da yi yayin da taci gaba da kuka cike da rashin sabo, shi kam kansa yakan dauki zafi in har tana masa irin wannan shirman, to yaga idan yaci gaba da nuna fushin sa a kan shirmanta ba wani dainawa zatayi ba, dole yaci gaba da lallaɓata cikin dabara ya zame hannunsa a nata ya ɗora saman tsakiyar bayanta yana shafawa.
Ai kuwa a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya, can kuma yaji tana sauke numfashi alamar tayi barci, tafiya ake cikin kwanciyar hankali aroud 9:00 pm suka sauka a garin babban birnin niger, wato Naimey mai cike da ɗinbin jama'a da albarka, dai-dai lokacin kuma Ma'azzara ta kusan kaiwa ƙarshe a mafarkin da take inda tayi mafarki Uncle Adamcy ya sayo masu chocolate.
juyi tayi cikin baccin inda takamo lallausan hannunsa ta sanya yatsarsa a bakinta ta fara tsotsar cikin nutsuwa.
Hakan yayi dai-dai da dawowa da Adamcy yayi daga duniyar tunanin da ya lula, da mamaki yake ƙoƙarin zare hannunsa daga bakinta dan sosai take tsotsar yatsarsa kamar ta sami Sweet, yana matuƙar jinjina wa da rigima irin ta 'yar amana, sanda ya zare hannunsa daga bakinta hakan yayi dai-dai da farkawarta daga baccin da ta ɗauki lokaci tana yi.
Manyan idanunta ta bude tar ta sauke su a kan Adamcy wanda yay kicin-kicin da fuska, tai saurin kallon Hussaina taga bacci take jikin Adamcy, sadda kanta k'asa tai tana wasa da yatsotin hannunta, amma bata yi k'ok'arin janyewa daga jikinsa ba.
Adamcy ya rabata da jikinsa yana jan tsaki, kallon Hussaina yay wacce ta kwantar da kanta a kafadarsa tana bacci cikin nutsuwa take fitar da numfashi, Adamcy ya kara shigar da ita jikinsa yana shafa kyakyawar fuskarta yana sakin murmushi.

Ma'azzara ta saci kallonsa taga yanda ya rungume Hussaina yana murmushi, kanta ta sadda taji kwalla ta cika mata idanu ta goge ta jingina kanta jikin Hussaina ta lumshe idanunta, bata sake koda motsi ba har jirginsu ya tsaya aka gama duk abinda za'ayi matafiya suka fara sauka.

Sai da taji Adamcy yana ma Hussaina magana cikin zazzak'ar muryasa yana tashinta, shine ta d'ago ta kalleshi ta sake maida kanta k'asa.

Hussaina ta farka Adu'a d'auke a bakinta, ta kalli Adamcy ta dan turo baki ta damk'e hannunsa tana murza tace"mon trésor nayi bacci sosai, nabar my baby." Ta fadi tana juyowa b'angaran Ma'azzara wacce idanunta suke a kumshe kanta sadda taki ta kallesu tana matsar kwalla .

Hussaina ta rungumeta tana murmushi tace"my Baby amana mun iso fa sai gida." Ma'azzara sai lokacin ta bude idanunta ta kalli Hussaina. Hussaina ta zaro idanu tace"Subahanallah kukan me kike baby? Wayyo mon coeur amanatu na kuka." Adamcy ya kalli Ma'azzara ya kauda kansa yana mai cike da jin haushin kauyencin ta, a ransa yace yanzu haka kukan rashin bata tab'a hawa jirgin bane yaki karewa, koko yawan jama'ane ba taso. Ya fadi a ransa, a zahiri kuma yace"Oh my God amanatu kukan kauyen cin ne? Sorry munzo Oya ku tashi muje." Nan suka mik'e bayan Hussaina ta lallashi Ma'azzara tako saki ranta tana mak'ale da hannun Hussaina, taki ko kallon Adamcy sai ma fushi da take masa, dan da zai rik'e hannunta kiyawa tayi ta rik'e hannun Hussaina gam.

A hankali suka fara saukowa daga matattataƙalar jirgin inda Hussaina take tafiya a hankali tana damk'e da hannun Ma'azzara, sakamakon zama da suka dan jima cikin jirgin ta gaji sosai dama gashi duk kasala takeji .

wajan sauka daga jirgin ma kaɗan ya rage Ma'azzara ta tara masu jama'a sai da Adamcy ya mata tsawa, dan gaskiya hankalinsa yana ga Hussaina saboda yana jin tausayinta tare da yaba mata a ko yaushe. Direban sa ne yazo daukarsu cikin wata jibgegiyar mota *Ferrari* kirar 2020 Bak'a sudik mai numfashi.
shi kansa direban idan ka kalleshi zakasan maigidan sa na kula dashi babu karya, bayan sun gama fitowa sun gaisa da direban cikin mutunci da karamci.

Direct katafaran gidan shi dake plateau suka nufa wadda itama wata ƙayattaciyar unguwa ce a cikin birnin Naimey ɗin.

Suna shiga gidan na saki baki da hanci kallon gidan tamkar a k'asar turai dan komai ya hadu na gidan, ba karya.
Suna fitowa Ma'azzara ta saki baki da hanci tana kallon tafkeken gidan, wanda bata tunanin ko a mafarki zata shigesa ba, duk ma a tsorace take, ta mak'ale Hussaina.

Adamcy kuwa Hussaina yake kallo yadda take takawa da kyar ga ƙafafuwanta duk sun fara kumbura tamkar me tsohon ciki, a hankali take takawa yayinda flawer's ɗin harabar gidan suke kaɗawa suna bada wata iska mai daɗi da sallama suka shiga cikin gidan duk da sun tabbata ba kowa a ciki komi na gidan fes gwanin ban sha'awa, baza kace mutanan gidan sun daɗe basa ciki ba, Ma'azzara kuwa ƴar kauye sak takoma domin ita tunda take a rayuwarta bata taɓa kofice gida mai kyau da tsaruwar wannan ba gaba ɗaya tazama bagidajiya, sai mannewa Hussaina take.

Kallo saima da suka shiga tamk'meman parlonsu mai fitar da kamshi Hadiza mai aiki ta gyara komai tsaf, nan ma Ma'azzara sai zaro idanu take tana kallon duniya Hussaina na mata dariya.

Adamcy kuwa direct bedroom ɗinsa ya fice kamshin man body lotion da turaransa tsaf ya kama ɗakin kamar yanzu yasanya ga wani sanyi dake manne a ɗakin kodan ginin tayis ne kokuwa dan na urar dake manne aɗakin wadda ke sanyaya ɗakine wato Air condition to duka dai zasu iya samar da yanayin sanyin.

numfashi ya sauke daidai nan ya zauna bakin gado ya ajiye wayarsa dan kira yake ta amsawa tun zauwarsu kusan 40 minutes.
Ya fara ƙoƙarin cire sock ɗin ƙafarsa daidai nan kuma Hussaina ta shigo da sallama dan daket Ma'azzara ta barta ta gusa bayan ta kaita masaukinta ta nuna mata yanda zatayi wanka, ta fito mata da riga doguwa milk colour me shegen kyau ta barota ta nufo gun mijinta.

Murmushi kwace kan fuskarta wanda tuni tayi wanka ta sanya ƴar amlas dan samu wadatacan iska kasan cewarta mai juna biyu sabo kuma.

ɗagowa yayi yana kallonta cikin yanayi na kauna yace" my dear bebeta har kinyi wanka shine aka ƙikirana tayi bayan kinsan banaso kina wahalar mani da kanki a yanzu tunda bake ɗaya ce nafi so komi in maki kekuma kihuta" ya ƙarasa maganar da shagwaɓa. Cikin ƙara ninkaya a son mijin nata tace" Mon coeur ni dai tashi muje na maka wanka wai me ma kake baka yi wanka ba?" ta ida maganar tana durkusawa gabansa cover ɗin ƙafarsa mai shegen kyau da tsada ta fara cire mashi ita taimaka mashi har ya cire komi nashi haka yake janta da hira sai wani wasa yakeyi da wasu ɓangarori nata inda duk itama ta narke mashi tana murza masa nipples dinsa tana kara shigewa jikinsa, ta kama lips dinsa tana tsotsa suna kallon junansu shiko yana murza mata nonuwanta sai lumshe idanu take tana kara kaima wajan shan bakinsa.

Da kyar suka bar juna ya samu kansa bayan ya d'auketa sun shiga toilet ta masa wanka suka fito.

Kaya ta fiddo mashi marassa nauyi towel a weast ɗinsa yayin da yake guge kansa da wani dan karami, Hussaina kwance a kan katafaran gadonsa inda gajiya ta fara saka gyangyaɗi domin ita in ana tafiya bata iya bacci amman kuma da an sauka sai taji baccin, yauma tayi mamakin baccin da tayi a jirgin.
Chapter 12 · 0% Book details