← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 29

Sashe 8

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bangaran Ma'azzara kuwa tana shiga ciki ta fada saman katifa tana juyi ta dora tafin hannunta saman fuskarta tana shakar kamshin uncle dinta, tana lumshe idanunta tana tuno lokacin da yace mata ko kina son zoben ne na baki? Sai ta dan saki murmushi tana gyada kanta, a hankali cikin sanyin muryata ta furta" Eh uncle ina so kazo ka bani uncle karka barni ka kasance da 'yar amanar ka kai da aunty me kirki." Ta karasa maganar tana juyi saman katifa tana sakin murmushi bata ganin komai sai uncle dinta.

Adiya ce ta shigo tana waya ta zauna gefen katifar da Ma'azzara take, Ma'azzara ta kura mata idanu tana murmushi saboda tsantsar kamar Adiya take da Uncle dinta, sai taga kamar shine.
Adiya kuwa bata san abinda Ma'azzara take ba hirata take da Uncle dinta Sufiyanu da yake France karatu ta shagala tana zuba masa sangarta.
Ma'azzara ta matso kusanta ta kwantar da kanta cinyar Adiya ta rik'e hannunta guda ta lumshe idanunta ba jimawa barci ya d'auketa. Adiya kuwa iyayan surutu har taba Sufiyan labarin Ma'azzara yayanta Adamcy an bashi amana wata yarinya bak'a kyakyawa son kowa, haka tayi tayi ta surutunta har ta gama ta janye Ma'azzara ta fito waje tana ba Ummee labarin uncle Sufiyan.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Bangaran Haliru yana siyar da uwar tinkiya ya wari iya kasonsa ya boye ya shiga gari, bai tashi komawa gida ba sai kusan magarib ya nufo gida da sauran kudin yana cicin magani ta yanda baza ka tab'a ganewa ba yayi cuta.
Salamatu tana tsakar gida ita da Harirah suna shirya yanda zasu d'aura mata aure batare da saninta ba ko iyayan rukonta ba, Haririh kuwa dama irin wannan matan ne makwadaita ta bugi cikin Salamatu ne taji kome dan ta sami yan canji ,dan tasan idan ta kai wannan gulmar gidansu Adamcy zata sami kudi. Haliru ne ya shige da sallama yana yatsina fuska, Salamatu ta Washe baki tana amsa sallamar tace" Haliru kasuwa tayi kyau ko? Nasan kudin ya isa muyi sabgar biki har da kayan d'akin amarya?" Haliru ya iso gaban Salamatu yana wani yamutsa fuska ya zaro kudin jaka ashirin da takwas yabata, ya cire jaka shida dan jika talatin da hudu aka saida tinkiyar.

Salamatu ta amsa ta kirga kudin tayi guda tace uwar garke tayi goshi Haliru sannu da k'ok'ari yanzu mu fara shirye-shiryan bikin shegiya bak'ar daga wannan masakin d'an naka mai farfadiya zamu aura mata, ko wanki kashi ta masa idan farfadiyar tashi ta motsa ai mun 'karu da ita."

Haliru ya had'e face yace"Salamatu bana son cin mutumci fa ai Allah ya dora masa ba mutum ba har zaki fara masa gori, wlh zance ma bana so". Salamatu tayi dariya ta ce"Yi hakuri na bari muyi abinda yake gaban mu shegun mutana nan ba zamu bari su tafi da Ma'azzara ko ina ba....." Kiran magariba ne da ake ya katse musu hura tasu Haliru yayi alwalla ya nufi masallaci, Salamatu tace da Harirah "Wai ke baki tafiya gidanki kiyi sallah ne anya kuwa ba da biyu kikazo nan gidan ba kuwa?" Ai Harirah najin haka ta mik'e tayi mata sallama ta fita ta nufi gida tayi sallah daga can ta tafi gidan su Adamcy kai gulma.

******

Da Misalin 8:30 pm gabaki d'aya sun hallara a parlour an shimfida leda saman carpet an jera kulolun abunci, Hussaina tana kusan Ummee zaune Adamcy na 'barinta ummee na hagun Ma'azzara tana kusan Hauwa'u sai susune kai take, Adiya na kusanta Hashim kanin Ummee ne shi da Saratu duk ba garin suke ba sunzo wajan rasuwa ne.

Hussaina tayi serving din kowa aka fara cin abunci cikin nutsuwa Adamcy kuwa yaki ci coffee kawai yake kurba ya jingina kanshi da kafadar Ummee. Ummee ta kai masa duka tace" Bature wai meyasa baka son cin abunci ne? Kai komai na Fawwad bature ka dauka, Adamu ina fad'a maka rink'a cin abunci da dare, ko da kadan ne dan Allah." Fuska ya dan yamutsa ya shafi cikinsa a hankali cikin sanyin muryasa mai dadin sauraro ya fara magana kamar baya so yace" Ummee dan Allah karki saka yaronki yayi tumbi , ko ya zama kato mana haba ni wlh ko Hussainata bana son tanacin abuncin dare Allah kuwa my ummeena." Ya karasa maganar yana kallon Hussaina wacce take yagar cinyar kaza tana korawa da fruit din kankana.
Ya kalli Ma'azzara wacce ko loma d'aya bata yiba ta dai d'auka amma ta kasa kaiwa bakinta, had'e face yace"Ke me kike jira ne da bazaki ci abunci ba?" Ma'azzara a tsorace ta d'ago da kanta tace"Uncle bana son duk wani abunda baka so nima na koshi bazan ciba." Ta idar da maganar tana sakin kuka.

Adamcy ya zaro idanu yana kallon ikon Allah, Hussaina ta kalli Ma'azzara tana murmushi tace"Babymu 'yar amana kiyi hkr kici karki biya uncle dinki fa, wlh yunwa zata illataka a banza yi shiru kici abunci maza." Adamcy ya ce"Ke bana son shagwab'ar banza ta yaya zaki zauna baki ci abunci ba maza ci ko yanzu na hada kayanki na kai ki gidansu Salamatu...." Ai kuwa Ma'azzara jikinta yana rawa, ta mik'e ta dawo gaban Adamcy ta zube k'asa tana shahsekar kuka tace"Uncle kamun rai na tuba bazan karaba wlh zanci kaji uncle." Ta fadi tana kara sautin kukan.
Hussaina hawaye har sun wanke mata fuska ta ajiye naman hannunta tace"ummee kina kallo Yayana yana saka yar amana kuka." Ummee ta kai masa duka tace"Adamu kafa kiyayeni maza lallasheta kalli kasamin Hussaina kuka kaji a sannu amana ba wasa ba fa."

Adamcy ya kara had'e face ya ce"Ke kiyi shiru ni wasa nake maki ba inda zan bayar dake, maza ci abunci Hauwa'u bani plate din abuncinta."
Hauwa'u tana dariya ta bashi dan diramar na burgeta, Saratu ma dariya take Hashim yace"lallai akwai dirama wannan yar amana akwai rigima Hussaina rigima uban gidansu jiji da kai da tsama, wai." Baki dayan parlon dariya sukayi.
Adamcy ya ajiye plate din abuncin gaban Ma'azzara ya kama hannunta ya saka a cikin abuncin yana wani gintse fuska yace"Oya cinye yanzu ko na 'bata miki rai." Kai ta d'aga ta rik'e hannunsa mai zobuna har uku ajere wanda na tsakar mai farkon sunan Adamcy shine Ma'azzara take so kamar ranta, ta kurama zoben idanu a haka take cin abuncin tana shafa zoben natsakiyar na gold din wanda fad'ar kyansa 'bata lokacine iri daya ne shida Hussauna Adamcy bai mata magana ba ya kauda kansa ya d'auki cup din coffee dinsa yana sha. Hussaina sai dadi takeji Ma'azzara nacin abunci. Ummee tace" Bature kubani diyarku zan rik'eta amana karku tafi Naimey da ita kubar mun ita mu zauna a Agadez...." Adiya tayi caraf tace"Yauwa ummeena kinga munza ma yan biyu tunda yanzu ma tafini girman jiki shekaru zan dan fita...." Adamcy ya saka mata tsawa wacce tasa Ma'azzara taji tsoro ta saki hannun Adamcy taja baya da sauri tayi kan Hussaina ta rungumeta.

Adiya kuwa tayi shiru, Hauwa'u dai dariya take ita da Hashim.
Yace" Ban hanaki babba yana magana kina magana ba?" Adiya ta turo baki ta "Allah ya baka hakuri Hussaina ta turo baki tace"mon trésor ka tsorata ta fa." Harara Adamcy ya watsa mata da sauri ta dauke kanta tana murmushi, dan wannan hatsabiban idanun nasa bata jure kallonsu, tsaki yaja ya mik'e tsaye da cup din coffee dinsa zai bar parlon. Dai-dai lokacin Harirah tayi sallama kofar parlo tana jira a bata izini.
Adamcy ya amsa sallama yay gaba bai tsaya ba, Adiya kuwa ganin jarababban ya gusa yasa tace"Wai wacece da tsowon dare haka lafiya?" Ummee ta ce"kinci gidanku muda akaiwa mutuwa har kashi biyu yan gaisuwa ne, Bismillah shigo." Dab da Adamcy zai shige bedroom din Ummee ya tsinto muryar Harirah tana cewa"Dan Allah da gaske kun yarda na shigo wallahi su Salamatu ne da Haliru zasu d'aurama Ma'azzara aure da mahukaci ba tare da kun saniba wai dan kar ku rik'eta...."

Adamcy ya zaro manyan idanunsa waje, dan shi kamar jiyayi tace sun hadata da mahaukaci yayi ta dukanta ba tare da sun saniba sam baiji tace aure ba, ya juyo yana dafe da kansa ya nufi kofar parlo yana furta"Hasbinallahu wani'imar wakil, wannan masifa ina dalili ni bansan matsala ba sai da yarinyar nan ta shigo rayuwarmu, da safe an gama magana kuma sun bullo da wata mahaukaci ya doketa dan sunsan baza'ayi shari'a da shiba oh my God." Ya fad'a yana dafe da kansa yana isa kofar ya murda ya bude mata yana mata wani mugun kallo cikin daga murya yace"Ki shigo gaban kowa maimaita abinda naji kin fadi mutikar kin fadi gaskiya zan baki jari mai tsoka amma da sharadin zaki daina yawon gulma?" Harirah kuwa Adamcy ya bata tsoro da kawarjini ta yadda ya gano sana'arta gulma.
Cikin rawar mutar tace" Eh... na...yarda..." Adamcy ya kauda kansa ya saki kofar ya juyo ya dawo tsakiyar parlon ya tsaya ya tura hannunsa cikin aljihu wandosa.

Ma'azzara tinda taji muryar Harirah tsoro ya kamata tasan Salamatu ta aikota kawartace.
Chapter 8 · 0% Book details