← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 29

Sashe 23

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Office ɗin Farouq ɗin suka je. Bayan sun zauna ne Farouk yace "ka dai ji duk irin bayanan dana maka wannan shine mafita."
Adamcy yayi sassanyar ajiyar zuciya ya lumshe manyan idanusa, ya bude su tarr akan Farouq yana kal kaɗa ƙafa yana jinjina kai, tamkar baya son yayi magana cikin sanyi maganar sa da amon muryasa me daɗin gaske, da nuna isar sa yace "Ok abokina naji babu damuwa insha Allahu zanyi magana da Ummee idan mu koma gida kasan gobe Hussaina take zubar da ruwa insha Allahu cikin satin nan Ummee zata koma gida sbd Adiya , to insha Allahu za'ayi magana baka da matsala , zamu rankaya mu tafi can tare wajan ɗangi ubanta inya so sai ka biyo mu sai ayi magana , amma fa ba yanzu ba se ta gama jarabawa zan dai ba ummee sako cewar ta sami miji , amma aure kam se ta gama secondary school zan dai baka ita kamu insha Allahu kaine mijinta , wannan ai ba wani abu bane da izinin Allah komi zaiyi dai-dai." ya faɗa yana zuba ma Farouq lumsassun idanunsa.
Faruk cikin farin ciki da jin dadi ya mike ya rungume Adamcy yace "nagode abokina hakika kai aboki na gari ne babu kamar ka bazan manta da kai ba cikin rayuwata ba , amma abokina gama secondary ɗinta da saura fa , kuma tana da larura ta ciwon ciki."
Adamcy ya riƙeshi yana bubuga bayan shi yace"babu komai ka daure kayi hakuri kamar gobe ne insha Allahu , kai de ka nemi so daga gareta ya kasance kafin lokacin babu wani ɗa namiji da take so da kauna bayan kai , amman zan baka amana Ma'azzara amana amana idan kaci amanar ta Allah yaci taka , ka kasance da ita kamata riƙon fiye da wanda nake mata bayan auran ku , marainiya ce gaba da baya bata da uwa bata da uba nine uwarta nine ubanta , bayan na aura maka ita kuma kai ne uwarta kaine ubanta se ni ubanta ni da Hussaina dan haka duk ranar da na aura maka ita , amanarta ta dawo hannunka bawai ina nufin na baka amana gaba ɗaya ba ne na sakar maka ita sai yanda kayi da ita ba , A'a zuwa lokaci-lokaci zan ɗinga sa maka ido duk abinda zai kasance zanyi tsaye tsayin daka na kwatar ma Ma'azzara yacin ta , akan yarinyar nan babu abinda bazan yi ba dan haka mutukar kasan bazaka rike amana ba maganar nan abarta kawai🙅🏻‍♀️."
Da sauri Farouq ya rike bakin shi ya ɗaura hannusa saman bakin shi yana girgiza kai yace "ai kafi karfin haka wlh ka wuce haka insha Allahu komi zai tafi dai-dai da izinin Allah , na yarda na ɗau maka Alkawari ruwa da iska zan rike Ma'azzara amana insha Allahu." ya faɗa yana murmushi.
Adamcy ma murmushi yayi ya buga bayan shi yace "baka da matsala komi zaiyi dai-dai na gode"nan dai suka ɗan taɓa hira kafin suka rankaya suka fito waje. Bayan sun fito suka koma can Ma'azzara tana dai baccin ta.

Hussaina tace,"to yanzu ya za'ayi idan ta tashi za'a sallame mu koko sai ta kara kwana?"
Farouq yace "eh to da sansa mu ne abarta har zuwa gobe a ga karfin jikin nata."
Hussaina tace"to babu komi bari naje gida na dawo Ummee ma tace tana zauwa , nasan ita zata kwana ."
Adamcy ya amshi Ummu ya kama hannun Hussaina suka ma Farouq sallama cewar zasu tafi su dawo, Adamcy yace "amana ka kular mani da ɗiyata kafin naje na dawo."
Farouq yayi murmushi yace "baka da matsala" nan suka fito. Farouq ya raka su farfajiyar asibitin har gun mota, suka shiga mota shi kuma yana tsaye har Adamcy yaja motar cikin nutsuwa suka bar cikin asibitin. Kanin Farouq ya dawo cikin ya duba yaga Ma'azzara tana baccin ta hankali kwance rabin jikinta cinyoyinta duk awaje, sai ya gyara mata kwanciya ya kara lulubeta ya fita zaiyi wani aiki ya janyo kofar sai ya kiro nurse ɗaya ta zauna da ita har yake dawowa.

************** ****** **************

Ma'azzara se washe gari aka salameta, taji sauƙi sosai ta sami kulawa wajan Farouq da ummee da uwayan riƙon ta. Washe garin salamota, ta koma school kuma ranar Hussaina ta zubar da ruwa, tasha kitso da kunshi tayi masifar kyau tasa a kama Ma'azzara ma, kasancewar ta ɗanyi hasken fata kaɗan baƙinta ya washe ba laifi har wani sheƙi take, kunshi ya fito sosai aka mata kitso yari yari a dogon baƙin gashinta masu kyau ta fito sosai.
Da misalin karfe 9:00 pm Zaune suke kan dining kowa nacin abinda yake so.
Ma'azzara sanye da riga da siket yan kanti farare sunyi mata kyau sosai, jelar kitsonta ya zubo har gadon bayanta, saura sun zubo gaba. Adamcy wainar da akayi ta sakada yace a masa farfesun hanji ya haɗa, ita ce yake ɗan ci dan baya cin abunci da dare. Ummee ma ita ce take ci, Hussy kuwa da Ma'azzara tuwon shinkafa da miyar ganye taji busassan kifi da jan nama, kowa se kai komo yake da hannunsa. Ummee tace " Wlh naji dadin wainar sosai wlh Allah yayi albarka dai." Ma'azzara tace"Ummee ai da nan kike kullum sai na miki kinci." ta faɗa tana kallon Hussy, Hussy ta harareta tace" Karya yaushe kika iya waina wannan dai kinsa aikin Hadiza ne da granny..." Sallamar granny ce ita da ɗan tsohon ta, ya katse masu hira sunzo ma Ummee sallama dan jirgin 6 zata shiga gobe. Ummee ta miƙe cikin girmama ta tarbe so Ma'azzara ma ta miƙe da gudunta ta rungume granny tana dariya. Tsoho yace" duk ta shafeki da miya ko?" Dariya Ma'azzara tayi tace" kaji haushi bakai na tara ba dai." ta faɗa tana sakin granny jin ummu da take kwance cikin ɗan gadanta ta tsala ihu, taje da gudu ta ɗauketa tana jijigawa ta nufi kitchen ta wanke hannunta. Adamcy ya rungume tsohon yana jijigashi.
Ummee ta kai masa duka tace"sake shi maza." Hussy tayi dariya ta taso tana cewa"Anzo kwadayi ko to babu rabon ku." nan suka gaisa ta nufi kitchen.
Karo Suka ci da Ma'azzara tana fitowa tana ma Ummu wasa. Tayi dariya ta wuce tace" har kin koshi ko?" Ma'azzara tace"Eh Aunty" ta wuce ta nufi bedroom ɗinta. Bayan sun gama gaisawa Aka shiga hira wasa da dariya. Farouq ne yazo da tsaraba niki-niki da ta ummee da ta yan uwan Ma'azzara za'a kai masu. Adamcy yace" Ah lallai abu nayi ne har da su sako." Ummee tace " Masha Allah Farouq Allah ya tabbatar da alkhairi insha Allahu wannan sakon da kaina zan kaishi har Audarass , daga na huta a Agadez zanje lallai akwaita Halliru da Salamatu..." ko me ta tuna se tayi diff. tayi murmushi. Granny tace"Au ashe in Allah yayi da likita bokan turai za'ayi Allah ya sanya alheri." gaba ɗayansu suka amsa da "Ameen. Hussy tana manne jikin ummee tace"Suruki kaje ka kirawo ɗiyar ka mana nasan dai yana son gaisawa da ita." Adamcy ya zabga mata harara yace"Zauna karki kirawota ɗin." ya faɗa yana murmushi. Ummee tace " abun kunya bazaku kirata kenan?" Hussy ta langwaɓe kai tace"Allah ummee shi zaice ni na koshi dayawa." Adamcy ya mata nuni da ido anjima ba barci. Kai ta sunne tana murmushi dan itama a matse take da mijinta, kusan wata biyu. Tsoho yace"Tab kai Farouq tashi ka shiga da kanka ka kirawo ta ku gaisa ɗin tinda haka ake a maraya surukan banza." Adamcy ya miƙe yana murmushi ya harari Hussy ya nufi saman. Ma'azzara kuwa tana zuwa ta zauna ta tisa ummu gaba tana mata wasa se halba ƙafa take tana bata lips ɗinta tana tsotsa, idan ta janye se ta tsala kuka dole ta maida mata tana dariya. Yanzu ma tana tsotsar lips ɗinta taji ya fara zugi ta janye tako fasa kuka, Ma'azzara tace" Allah bazan baki ba zafi labɓana suke zo na girgiza ki, ni bari na goyaki na canza pad." ta faɗa tana saka ummu bayanta ta goyata ta taɓa siket ɗunta taji lema zumburo baki tayi tana cewa"Tab ya akayi ya pad ɗina ta jiƙe haka har ya taɓa kayana , Baby ki kwanta naje nayi wanka da sauri na canza kaya." ta faɗa tana ƙoƙarin sauke ummu taba kofar shigowa baya. Adamcy ya tura kofar ya shigo da sallama. Ma'azzara ta saki ɗan ihu tana cewa "Uncle wlh ni ba ƙazama bace ummu ce take kuka." murmushu ya saki ya zura hanunsa cikin aljihu yana takunsa na isa yace " Ok kawo ummu ɗin..." sauran maganar ta maƙale masa sbd karaf Adamcy idanunsa suka sauka kan farin siket ɗinta da ya ɓaci da jini, da sauri ya rumtse idanunsa ya bude su ya daka mata tsawa!!... Ma'azzara ta gigice ta saki kuka ummu na ƙoƙarin fadowa daga bayanta. Adamcy yay zafin nama yay kanta a guje... 💃🏻Taku ce har kullum Real Ladingo🤝🏻😍🤣🙊```Insha Allahu sauran page 2 na rufe free page.```

*Karku manta BANI DA GATA Ya koma na kudi 200N ga me buƙata A tuntuɓi wannan lambobin 👉🏻+22792589446/ +22796515805/ Se naji ku Real masoya🥰🤝🏻🤣*

  *💖BANI DA GATA💖*

*MALLAKIN*
👇🏻
*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻

*TO MASOYAN BANI DA GATA DANGANE DA KORAFE ƘORAFEN KU, CEWAR BANI DA GATA  A RAGE MASA KUDI DAGA 300N, TI NA AMSA NA SAUKE 100N NA MAI DISHI 200N DAN HAKA DUK ME BUƘATAR BANI DA GATA ME CIKE DA ABUBUWA WNADA BA SAI NA FAƊA BA, TO  HANYA BUƊE TAKE FARASHI ME SAUƘI AKAN NERA 200 KACAL DUK ME BUƘATA ZATA IYA TUNTUBANA TA WANNAN LAMBOBIN 👉🏻+22792589444/ +22796515805*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Free page*

*👉🏻14*
Chapter 23 · 0% Book details