Sashe 17
Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haleeru ya rinƙa faɗin,"Megari sakeni kar ta iso kaga ba lafiya ba gareta , karta zo ta murkushi ta mani zawayi jiki."
Haba wa me za'ayi in ba dariya ba wuri ya barke da dariya.
Megari yana riƙe da Haliru yama Salamatu tsawa, yace"dan Allah tsaya malama Salamatu ki tsaya anan karki iso mamu nan ki tsaya anan kiyi bayanin ki in Allah ya yarda kome ye za'akawo masalaha , kar ki iso mana dai awannan yanayin da kike ciki dan naga kuda ya fara binki..."
Ai ko Salamatu ranta idan yayi dubu ya bace ta duƙe a nan ta fashe da kuka tace "Yanzu irin tozarcin dazaka mani cikin mutane nice kuɗan kebi? Daman an tara jama'a ne dan a wulakantani , nice kuda yake bi?"
Megari yace,"Allah baki hakuri Salamatu ba haka nan bane , yanzu dai imani bayani miyake tafe dake?"ya kalli Malam Tanimu yace"Malam Tanimu dan Allah dan Annabi wannan shari'a taku mai tsayi ce kabari mu kare da Salamatu gara ni inyi ta Salamatu in salameta ta tafi tabamu guri, ko miye gara in ɗauki nauyin shi."
Ai kuwa kowa ya kama dariya yana su'sunne kai.
Mallam Tanimu da kanshi yace"A'a babu komi a salameta ɗin."
Salamatu tace"megari ba komi bane illa"tanayi tana yatar majina tana shashekar kuka taci gaba da magana, "uwar garke na Haliru ya since ta kuma daga nan ma police zani wlh mai rabani dashi yan sanda ne..."
Megari ya katseta yace,"Subahanallahi Haliru da kanka kayi wannan abu Haliru da gaske ne ka ɓalle ma Salamatu Uwar garke?"
Haliru ya ɗinga cicira ido yana za'zare ido yana irin na munafukai.
Kallo ɗaya mai gari yamashi tin kan yayi magana yace "wlh kai ka ɗauka, kai ka ɗauka ka faɗi mana gaskiya in ba haka ba Salamatu tashi kawai ki kaishi wajan yan sanda shi zaifi.."
Ai kuwa ta zabura ta mike cikin fari ciki tana shasheƙar kuka amman in ka kalle fuskarta kasan akwai mugunta, da ɗaukar fansa tare da ita.
Ai Haliru yana ga Salamatu ta mike ta juya ƙuda na yana biye da ita yace "A'a zan faɗi gaskiya , megari nina balleta amman wlh bankai gacin kuɗin ta ba, yanzu haka tana kara ida za'a saido min ita."
Ai ko Salamatu tana jin haka babu wani tsaye-tsaye a guje tayo kan megari, haba megari yana gani haka ya mike riƙe da hannun Haliru ya maida shi bayansa, yace "dakata-dakata tsaya Salamatu yi hakuri , haba Salamatu haba Salamatu yi hakuri komi zaizo ƙarshe kina ji tumkiyarki bai saida maki ba , bari yanzu insa aje akawo maki kayan ki" ya kalli Haliru yace "kai Haliru gaya mana waka ba saida uwar garke?"
Haleeru yace "Nuhu dillali."
Megari yace "Nuhu dillali kaba?" yace"eh"
Yace ma Malam shehu da yake zaune a kusan shi yace,"Mallam shehu maza a tafi kara ama Nuhu dillali magana, wannan uwar garke wace Haliru ya bashi ya sayar koya sayar ya ba wanda ya saya kuɗin shi a kawo ta nan yanzu-yanzu nike bukatar ta."
Mallam shehu a take yace"Ranka ya dade da girman kujerar ka an gama". A take ko ya mike ya nufi kara.
Salamatu tana jin haka fari ciki ya kamata ta zauna a nan ta hada hannuwanta tace "Nagode mai gari nagode Allah ya kara maka daraja da girma , Allah ubangiji yasa kai zaka ta mulkar mu daga nan har karshan rayuwar mu, Allah ya rabaka da kishiya in Allah ya yarda kai ɗaya ne agarin Audarass babu wani."
Nan ma dai mutane tabasu dariya, shiko mai gari yaji dadi yaban da Salamatu tayi mai, sai kara wura hanci yake ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yana dariya, bayan ya kare dariyar ya hade rai ya nuna Haliru da yatsa yace "Gaskiya Haliru abinda kake baka kyautawa bamu maka kashe ba tin su adamcy suna gari , wata nawa yanzu tsawan wajan wata biyar amman har yanzu baka daina ba? Bamu ce maka karka kuskura ka taɓa mata uwar grke ba? To wlh daga yau idan ka sake maka mancin haka gidan yari za'a kaika babu shaka zaka gidan maza , idan kune yaji jiki ya tsira."
Haliru cikin rawar jiki ya rike kafafu mai gari yace,"wlh wlh insha Allahu na daina daman takaicin wannan kokowar damukayi ta kadani ranar , shine nima nace zan ɗauki fansa akan wannan."
Gaba ɗaya kowa abin sai daya bashi dariya, nan dai aka samu aka sasanta daga can nesa Megari ya hana Salamatu ta matsu kusan su daga can yamasu nasiha ya kwatanta masu sufa yan uwane uwa ɗaya uba ɗaya su haɗa kansu subar tashin hankali, yanzu duk garin Audarass ana nan ana zagin su basa shiri tsakani su haka yaran su ma kananan su lalace, dan Allah su daina haka.
Ana cikin haka sai ga Malam shehu ya iso tare da uwar garke, har da ma Malam Nuhu ana jaye da ita nan aka ba Salamatu ta tana ta ma Megari godiya.
Megari yace taje ankai mata har gida, nan ko ta mike kuɗan nan nabiye da ita ta kama hanyar gida tana cikin fari ciki, megari yace ma Mallam shehu yakai mata tumkiyarta har gida, nan yakai mata har gida shima Haliru nan ya nuna insha Allah ya yarda bazai sake haka ba, kuma bazai sake fada da ita ba taje tayi shirmanta tinda fada da ita ba riba bane tafi karfin shi gashi tana azabtar dashi ta tusa, ha nan fa miza'ayi in ba dariya ba nan dai akayi taro aka watse shi kuma Haliru yaki tafiya har sai da aka ida shari'a kwartayan nan yana zaune..
Salamatu kuwa tana zuwa gida ta ɗauko wasu kayan ta ɗauki ruwa abokiti ta shiga banɗaki tayi wanka ta sauya kaya ta fito. Lokacin har Malam shehu ya kawo uwar garke, ya ɗaure mata taji dadi sosai taje ta shafa uwar garke taje tana da kudi ta ɗauki 1000F taba ɗanta Murtala tace yakai ma Malam shehu shiya ɗauki dari yaba megari dari ɗan yana ta dariya ya fita daga gidan, ya tafi ya kai aiken.
Ita ko ta kama hidumomin gaban ta bayan ta bada an sayo mata magani zawo ta sha tana yan wake-wakan ta ɗan akwai ta da taurin rai dan duk ciwon da Salamatu take ji bai hanata wakar ta da aikin gida, sai de idan ya kwantar da ita..
Bayan magariba ne da Haleeru ya shigo gida ya nemi da suyi sulhu da ƴar uwar shi ya kwatanta mata da cewar wannan abu da suke baida kyau in Allah ya yarda sun daina ta yafe mashi shima bazai kara tsokanar taba.
Nan dai da har ta kiya komi kuma ta tuna tace to shikenan babu komi, nan dai har take ce mashi wlh duk da dai bata san Ma'azzara amman yanzu tayi kewarta tsawan wata shida bataga ɗiyarta ba ɗiyar ɗan uwanta ko da ƙaƙa dai jini su ce.
Nan dai shima Haliru yace gaskiya basu kyauta ba in Allah ya yarda zaije nan wajan su Ummee wajan yan uwanta da suka bari ya tambaya abashi lambar Ummee datake agadez abashi lambar adamcy ya kira yaji ko lfy Ma'azzara take, nan dai suka ci gaba da firar su ta duniya malam musa na jinsu baiyi magana ba...
*A salin su Adamcy*
*Muhammed norènzo* cikeken bature ne haifafan france, maraya ne gaba da baya daket a wahale ya samu yay karatunsa, wanda yake da tsantsar ilimi gwamnati ta ɗauki nauyinsa, bayan ya gama aka turo shi niger cikin garin Agadez bautar ƙasar wata shida, anan ne Allah ya haɗashi da wata mai suna lallah buzuwa, soyayyya me karfi ta shiga tsakanin su iyayanta suka ce baza su ba bature ƴarsu ba, abu kamar wasa Norènzo yace zai musulinta, lallah taji dadi sosai ko uwanyata bata faɗa ma ba, ta kaishi gidan sarki nan aka bashi kalmar shahada bayan an tabbatar zai musulinta ne dimin Allah badan an hanashi auran lallah ba. Ya amshi musulinci, aka bashi sunaye kyawawa na musulinci aka faɗa masa darajar da suke da wajan Allah ya zaɓi Mohammed, daga nan sarkin Agadez ya buƙa ci yaji tarihin sa, nan ya baiyana masa shi marayane bayada uwa bayada uba, ko ƙasarsu gwamnati ce ta ɗauki nauyin karatunsa.
Daga nan sarki ya amshi Muhammed da hannuwa biyu ya zama kamar ɗansa, yake kula da rayuwarsa bayan ya gama bautar ƙasa yace bazai koma turai ba, tunda bayada kowa a can sarki ya saka baki iyayan lallah suka bashi auran lallah, bayan ya masu bayanin kome sarki yay komai a matsyin ubansa ya bashi gida akai biki lfy, soyyaya mai tsafta suke gudanarwa da lallah wacce itama cikakar buzuwace ga kyau ga fari, amma duk da haka Muhammed yafita kyau, nesa ba kusa ba...
Bayan shekaru biyar zuwa lokacin Allah ya a zurtasu da haihuwa, har biyu mace da kuma namiji, kuma zuwa lokacin Allah yay masa buɗi sosai, yaransu kyawawa masu kama da ubansu sak, namijin Fawwad macan Rukaiyya, wanda suka taso cikin gata da kulawa da kuma tarbiyya, ga ilimin addini da na boko kowa sha'awar yaran Muhammed yake, baza ka taɓa cewa tubabe bane ya riƙe musulinci hakkun da gaskiya, ga arzuki Allah ya bashi...