← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 29

Sashe 24

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Amatuƙar hanzarce Adamcy ya usa gaban Ma'azzara, tana ƙoƙarin zubewa ƙasa ita da Ummu, ya taro su su duka suka faɗa jikinsa,  luuuu haka Ma'azzara tayi tare da lumshe idanunta, wani iri taji a jikinta sakamakon haɗuwar jikinsu waje ɗaya, gefe guda kuwa tuni daddaɗan ƙamshin turarensa ya cika hancinta,  cikin takai cin yanda ta lafe a jikinsa ya tureta tare da ɗaura Ummu Saudat akan wuyansa yana ɗan buga bayanta da hannunsa.
Kwaɓe fuska tayi tare da karyar da wuyanta gefe, ɗan ƙaramin bakinta taɗan turo cikin sangarta tace.
"Am sorry Uncle."
Yana me girgiza Ummu Saudat ajikinsa ya ɗan kalleta tare da watsa mata harara, cikin yanayin haɗe fuska haɗi da tsare gida yace.
"Zaki tafi ki wanke ƙazantar dake jikinki ne ko kuwa zaki tsaya ki kafeni da mayun idanuwanki?." yaƙare maganar babu wasa akan fuskarsa.
Sake turo bakinta gaba tayi, cikin yanayin sanyi tare da tsananin shagwaɓa wanda yinsa ya zame mata jiki ta juya ta nufi hanyar toilet, har takai kusan ƙofar ɗakin ta tsinkayo muryarsa inda yace.
"Idan kin fito Farouq yana jiranki awaje."
Yana gama faɗin haka ya juya yafice daga cikin ɗakin.  Itakuma batare da ta juyo ba ta shige cikin bathroom,  ganin jinin ya ɓatata sosai ya sanya ta cire kayan jikinta, ruwa me ɗan ɗumi ta haɗawa kanta tare dayin wanka, towel ta ɗaura ajikinta kana tafito daga cikin toilet ɗin, shirya kanta tayi cikin wata pink ɗin doguwar riga irin bubu gown ɗinnan, sosai rigar wacce taji adon white stones ta yiwa jikinta kyau,  wani ɗan madaidaicin mayafin rigar ta ɗauka tare da yane kanta dashi, wanda ya sauƙo zuwa shoulder ɗinta,  wani pink flat shoe ta sanya aƙafafunta, turarenta mai sauƙin ƙamshi ta sanya, cikin yanayin ta na sanyi ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice,  a hankali take sauƙowa daga kan step ɗin.

Ƙamshin sassanyar turarenta ne ya ratsa hancinsu, hakan yasa su waigawa zuwa ga inda ƙamshin ke fitowa, idanunsu ne duka suka sauƙa akanta,  ahankali take ci gaba da sauƙowa daga kan step ɗin,  idanunta ne suka sauƙa akansu su duka biyun, da ɗan sauri ta ɗauke kanta daga kallon Uncle ɗin nata ta sauƙe ganinta akan Farouq, ɗan murmushine ya bayyana akan black beauty face ɗinta, shima Adamsy saurin ɗauke kansa daga gareta yayi tare da ɗan taɓe bakinsa, duk da cewa shigar tayi matuƙar yi mata kyau,  ahankali tagama sauƙowa daga kan step ɗin, cikin nutsuwa ta ƙaraso cikin falon tare da yin ƙasa da kanta,  kasan cewar Adamsy da Farouq ɗinne kaɗai zaune acikin falon, don kuwa tuni su Ummee sun da Hussaina sunyi ɗaki, tin bayan tafiyar granny da mijinta. Tana gama ƙarasowa cikin falon, Adamsy ya miƙe tsaye kafaɗarsa ɗauke da Ummu Saudat, duban Farouq yayi tare dayi masa alama akan cewar shi ya wuce, hannu Farouq ya basa sukayi musabaha, nan ya juya ya nufi hanyar bedroom ɗin Hussaina.

Zama tayi akan kujeran dake facing nasa, cikin nutsuwa ta sunkuyar da kanta ƙasa, cikin sanyin Murya tace dashi "Ina wuni!" 
Shiru yayi yana kallonta, haɗe da sakin murmushi, hakan sanyin da takeyi masa yanzun ke burgesa,  ya fahimci cewa girman budurcin da tayi yasanya taƙarayin hankali, sannan nutsuwa ta soma shigarta sosai.
Jin bai amsata bane yasa ta ɗago idanunta ta kallesa, karaf idanunta suka sauƙa acikin nasa saboda dama kallonta yakeyi,  hakanan taji tanason yin halinnata na shagwaɓa, amma tunowa da tayi cewar  shiɗin ba Uncle ɗinta bane hakan ya sanya tayi shiru,  murmushi Farouq yayi tare da cewa.
"Barka da fitowa sarauniyar mata, wannan shigar tayi miki kyau, har takai ga ina ganinki kamar baƙar balarabiya."
Murmushi tayi kawai batare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba,  ganin kamar kunyar sa take ji ya sanya shi tashi daga inda yake zaune  kusa da ita kaɗan ya zauna, cikin kulawa yace.
"Akullum ƙara kyau kike Ma'azzara, haka kuma kowacce rana soyayyarki ƙara ninkuwa take acikin zuciyata, tun ganina na farko dake soyayyar ki ta kama zuciyata, haƙiƙa ke ta daban ce acikin mata Ma'azzara, komai naki abun sone ga ɗa namiji, bani da wani buri ko fata daya wuce naga kin zamanto Matata ta sunna." Ɗan nisawa yayi   tare da lumshe idanunsa, duban Ma'azzara yayi da kyau cikin son nuna mata ƙauna yace.
"Inasonki Ma'azzara so maitsayawa azuciya, namiki alƙawarin baki duk wata kulawa, zan shayar dake ruwan soyayya, zan jiyar dake duk wani daɗi da mace ke buri da fatan ji acikin gidan aurenta!." sake lumshe idanunsa yayi.
Ɗagowa Ma'azzara tayi ta dubesa da kyawawan idanunta, cikin alaman gamsuwa da maganganunsa tace.
"Nagode ƙwarai da nuna ƙaunarka agareni."
Murmushi yayi, nan suka ɗan taɓa hira dashi irin na masoya, yayin da rabin hiran ya kasance gaba ɗaya shiyake janta da zance.

Adamsy kuwa yana shiga ɗakin Hussy ya sameta kwance akan gado  yayin da ta miƙe ƙafafunta,  tana ganinsa ta saki murmushi, ƙarasawa gaban gadon yayi ahankali ya kwantar da Ummu Saudat kan gadonta, don tuni tayi bacci,  hannunsa ya miƙawa Hussy, tuni itama ta basa nata hannun, jawota yayi gaba ɗaya jikinsa, duka hannuwansa ya ɗaura akan waist ɗinta, tare da mannata da ƙirjinsa,  cikin so da ƙauna take kallon kyakkyawar fuskarsa, hannu tasa taɗan shafi tattausan sajen dake kwance akan fuskarsa, cikin sanyin murya tace.
"I missed you so much mon trésor!"
Fuska yaɗan shagwaɓe mata tare da cewa.
"Miss you too mon bebena, i hope yau kinshirya min tarba me kyau?" ya faɗi maganan yana me kashe mata idanunsa ɗaya.
Murmushin daya bayyana kyawunta tayi, cikin matsanancin ƙaunar da takeyi masa tace.  "Koda yaushe cikin ɗoki da soyayyar ka nake mon tresor, babu wata rana da zan gajiya da kai, musamman ma idan zakana shayar dani daɗinka maisanyawa namanta kaina!." Cikin matsanancin shauƙi taƙare maganan har wani ɗan juya idanunta takeyi saboda, daɗin yau zata kasance da mon trésor ɗinta, don kuwa ba kaɗan ba tayi missing ɗinsa, duk dama time to time yana ɗan romancing ɗinta, amma akoda yaushe tafi son jinsa a cikin jikinta,   hannuwansa ya sanya ya tallafi kumatunta, kiss ya ɗaura akan forehead ɗinta tare da ɗan saketa, agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa ya duba, cikin kulawa yace "Kikulamin da kanki mon bebeta zanje mall bazan jima ba zan dawo."
Itama kiss ta manna masa, kana tace "Adawo lafiya"

Koda ya fito falon bai iske Ma'azzara da Fariuq ba, alaman cewa kenan Farouq ɗin ya tafi.
Kai tsaye compound ɗin gidan ya nufa, nan yashiga cikin haɗaɗɗiyar mercedess benz ɗinsa, inda maigadi ya wangale masa babban gate ɗin gidan ya cilla hancin motarsa waje.

Ma'azzara kuwa tana can ɗakinta, inda ta duƙufa akan exercise book ɗinta tanata karatu, don sam batason zama shiru, kuma a duk sanda tayi karatun yana zama a brain ɗinta sosai.
Chapter 24 · 0% Book details