Sashe 26
Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ƙarfe 3 daidai jirginsu ya sauƙa a babban Airport ɗin dake Niamey, cikin takunta mai ɗauke da isa izza take sauƙowa daga step ɗin jirgin, wata farar doguwar budurwace mai fama da matashin kyau, idan kaganta sak baturiya domin kuwa yanayinta harma da shigan dake jikinta irin nasu ne, don kuwa ƙananan kayane ajikinta, gawani takalmi me tsananin tsini da ta sanya aƙafafunta, Hassana kenan matashiyar budurwa maiji da kai haɗi da wayewa.
kaitsaye motar da aka turo daga gida don ɗaukarta ta shiga, koda ta isa gida iyayenta suka ganta sun cika da murna ƙwarai wanka kawai tayi inda ta sanja kaya zuwa matsatstsiyar gown, car key ɗinta ta ɗauka, kaitsaye tace tatafi gidan Hussaina don tayi kewarta sosai, cikin zuciyarta kuwa ba kewar Hussaina bace, tsananin ƙauna haɗi da shauƙin da take yiwa mijin ƴar uwartata ne ke damunta.
Zaune suke afalo, inda Adamsy ke zaune akan kujera, Hussaina kuwa kwance take ajikinsa, sai narka masa shagwaɓa takeyi, duban agogo yayi yaga har 4 takusa, daidai lokacin dawowan Ma'azzara daga makaranta kenan.
Cikin kulawa ya dubi matartasa inda ya manna mata kiss akan bakinta, ahankali yace.
"Inasonki Hussainata"
Murmushin jin daɗi Hussaina tayi tare da ƙara narkewa ajikinsa tace
"Nima ina sonka Adamun Hussaina." daidai lokacin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, hakan yasa gaba ɗaya suka kai dubansu ga ƙofan, da sauri hussaina ta miƙe, da wani irin gudu taƙarasa inda ta faɗa jikin Hassana, zuciyarta ɗauke da matsanancin farinciki, rungumeta Hassana tayi nan suka shiga ɗokin ganin juna, cikin matsanancin farinciki Hussaina tace.
"Wow surprise kenen, i miss you so much sister!"
fuska ɗauke da murmushi Hassana tace "miss you too hussy"
Hannunta hussy takamo suka ƙaraso cikin parlon, duban hassana adamsy yayi fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Ƴan mata mu ai munyi fushi dake."
Murmushine sosai ya faɗaɗa akan fuskarta cikin yanayi na wayewa ta tako inda taƙaraso zuwa garesa, cikin yanayin sabo da al'adar turawa tayi hugging ɗinsa, ahankali ta kwantar da kanta akan chest ɗinsa, cikin wata irin murya tace "I miss you dear."
Murmushi Adamsy yayi tare da ɗan janye jikinsa zama yayi akan kujera tare da dubanta idanunsa ya ɗan lumshe ahankali yace "Miss you too"
hannunta Hussy ta kama inda suka zauna akan kujera, cikin kewar juna hussaina ta ƙara rungume ƴar uwartata nan suka shiga ɗan taɓa hira su dukansu, Hassana na rungume da Ummu Saudat, yarinyar ta shiga ranta. ƙasa-ƙasa Hassana ke jifan Adamsy da wani irin kallo, wanda sam cikinsu babu wanda ya kula.
A hankali Ma'azzara ta turo ƙofar falon ta shigo, hannunta ɗauke da jakan makarantar ta.
turus haka taja ta tsaya take kuma sauran sallaman da take yi ya maƙale a maƙoshinta, idanunta ta zaro tana ƙarewa aunty Hussy dakuma wacce tagani agefenta kallo, ganin haka yasa Hussy sakin murmushi, fuska ɗauke da fara'a tace.
"Ma'azzara ya dai kika tsaya shigo mana."
a hankali Ma'azzara ta tako zuwa cikin falon, hannunta Hussaina ta kamo cikin kulawa ta dafa kafaɗan Hassana, duban Ma'azzara tayi tare da cewa.
"Amana ga ƴar uwata nan itace Hassanata"
Mamakine ya bayyana akan fuskar Mu'azzara ahankali tace.
"Aunty dama ke ƴan biyu ce?" murmushi Hussaina tayi tare da cewa "Eh mana"
Murmushin jin daɗi Ma'azzara tayi tare da duban Hassana cikin girmamawa tace.
"Aunty Ina wuni?"
Kafeta da idanu Hassana tayi batare da ta amsa ba, ganin haka yasa Ma'azzara sauƙe idanunta ƙasa, don wani abu na musamman ta hango acikin idanun na Hassana.
Hussaina ce tace da Hassana "Sis Ma'azzara na gaisheki"
Fuska Hassana ta ɓata tare da cewa "Lafiya"
idanu Ma'azzara ta ɗaga inda ta zubawa Uncle ɗinta, sosai yayi mata kyau takuma yi bala'in yin kewarsa, fuska ta shagwaɓe cikin kasala tace.
"Uncle"
Bude idanunsa dake kulle yayi inda ya sauƙesu akanta, cikin wata irin cool voice ɗinsa yace "Ummm Amana ya akayi?"
Kasa ɗauke idanunta akansa tayi, take kuma idanun nata suka ciko da ƙwalla, sake maida idanunsa yayi ya lumshe a hankali yace.
"Waya taɓaki kike ƙoƙarin yi mini kuka?"
Ɗan ƙaramin bakinta ta turo gaba, batare da tace komai ba. Hussaina ne tayi murmushi tare da cewa.
"Ae amana fushi take da kai, kwana biyu kenan bakwa haɗuwa"
Murmushin daya bayyana zallan kyawunsa yayi tare da duban Ma'azzaran, sai a lokacin ta ɗauke ido daga kallonsa, miƙewa tayi tsaye tare da cewa "Bara naje na cire uniform." ta faɗa tana amsar ummu hannun Hassana ta haye sama tana mata wasa.
Harta haura sama Hassana bata ɗauke idanunta akan taba. Adamcy ya miƙe jin ana kiran sallah la'asar. Cikin wani irin tunani Hassana tace.
"Hussaina wace wannan?"
Murmushi Hussaina tayi cikin rashin damuwa tace
"Amanar muce nida Adamsy na"
Idanu Hassana ta juya tare da cewa "Amana kamar ya?"
Babu ɓata lokaci Hussaina ta zayyane mata gaba ɗaya abunda ya faru, da yanda riƙon Ma'azzara yadawo wajen su.
Gyara zama Hassana tayi tare da duban Hussaina cikin matsanancin ɓacin rai tace.
"Hussaina baki da hankali, bakuma ki da tunani, tayaya zaki ɗauko wannan ƙatuwar yarinyar ki aje acikin gidanki?"
Murmushi Hussaina tayi cikin halin ko in kula tace "akwai aibu ayin hakan ne ? Mu'azzara yarinyace babu abun da ta sani, sannan marainiyace, idan ma wani tunanin kikeyi dan Allah Kibari"
Tsuka Hassana tayi cikin takaicin abun dake damunta tace.
"Ko kinsan Yarinyar nan son mijinki take?"
Murmushi Hussy tayi tare da duban ƴar uwartata, cikin nuna mata batasan me takeyi ba tace.
"Dama nasan tunanin da zakiyi kenan dan Allah Hassana karki kawomin tarzoma acikin gidana sam wannan maganan naki ba gaskiya bace"
Murmushi takaici Hassana tayi cikin ƙufula ta miƙe tsaye, duban tsab tayiwa Hussaina, cikin son jaddada mata maganan tace "Nafaɗamiki Yarinyarnan son Adamcy take ko ki yarda ko kada kiyarda wannan badamuwata bace, amma kisa ido zakiyi kallo" tana gama faɗan haka ta ɗauki jakarta tafice daga cikin falon, da kallo kawai Hussaina ta bita tabbas tasan halinsu ya banbanta dana Hassana, domin ita Hassana akwai jinkai ga kuma zafin zuciya, miƙewa itama tayi ta wuce ɗakinta, sam koda wasa batasa zancen Hassanan akanta ba.
Mu'azzara kuwa na shiga ɗaki tayi wanka, wani riga marar nauyi tasa, tama ummu wanka ta shiryata tsaf, kai tsaye ta nufi parlo don samawa cikinta abunda zataci.
Adamsy ne zaune akan dinning area sanye yake da wando 3 quater jeans, wa ta farar singlet ya sanya, goran ruwane a hanunsa yana sha da kaɗan kaɗan, gaba ɗaya hankalinsa naga wayarsa,
Cak Ma'azzara ta tsaya tana kallonsa, tana jijiga Ummu, sosai yayi mata kyau hakanan taji shauƙin zuwa garesa ya kamata, nan take taji wani matsanancin feelings ya rufeta, a hankali ta shiga takawa zuwa garesa, tabbas tasa aranta cewa tana zuwa garesa zatayi hugging ɗinsa.
Cikin nutsuwa Hussaina ke takunta tana ƙoƙarin sauƙowa daga sama taku uku kacal yarage taƙaraso zuwa kan step ɗin da zai bayyanar mata komai dake cikin parlon.
Hakama saura taku uku kacal Mu'azzara taƙarasa ga Adamsy don cika burinta na rungume Adamcy ta haɗa da Ummu Saudat dake manne a kirjinta....
(Tofa readers Hussaina zata gaskata maganar Hassana koya? Ya zataji a yanzu idan takama Ma'azzara tayi hugging din Adamsy a bayan idanunta? Lallai akwai chakwakiya)
*Karku manta littafin nan na kudine kan farashi me sauƙi 200N Kacal👌🏻*
```Ni taku har kullum ```
👇🏻
*Real Ladingo😅*
*Sweet Baby💋*
*💖BANI DA GATA💖*
*MALLAKIN*
*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻
*WANNAN BOOK NA KUƊI NE KAN FARASHI ME SAUƘI NERA 200 KACAL, GA DUK ME BUƘATA ZAKU TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBOBIN 👉🏻+22792589444/ +22796515805*
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
*Daga yau Na rufe Pagen kyauta😅*
*Last Free page*
*👉🏻15*
Ahankali take tafiya harta ƙarasa kusa da inda yake.
Jin alamun mutum akusa dashi ya sanya shi ɗago da kansa a hankali, ya watsa mata kyawawan idanunsa, wani irin yarrr haka taji ajikinta, take duk wani tunanin dake kanta ya goge, wani irin abu take ji acikin jikinta wanda har batajin zata iya jurewa, hakan yasa kawai tayi ƙasa da kanta, take ƙwalla suka cika idanunta.
Girgiza kai Adamsy yayi kasancewar yasan bazai wuce shirmenta bane ya motsa, sai dai ganin tayi ƙasa da kai, ya sanya a hankali yace.
"Ma'azzara!."
Wani irin sauti nadaban taji muryarsa ya bada acikin kunnenta hakan yasa ta rumtse idanunta.
"Wani abu na damunki ne?." ya tambaya yana me ɗan kallonta, wani irin kuka ne ya ƙwace mata, take ta tafi da gudu tana riƙe da Ummu ta faɗa cikin jikinsa, Adamcy ya janye Ummu dan kar ta jimata, ganin bata haiyacinta, ya kwantar da ita kusan sa. Ma'azzara ta hannuwanta duka ta sanya ta rungumesa, yayin da ta ɓoye fuskarta acikin faffaɗan ƙirjinsa, sosai take kuka mai sauti, tana ƙara shigewa cikin jikinsa.
Kyawawan fararen idanunsa ya lumshe ahankali ya fesar da wani irin numfashi, cikin sanyin jiki, haɗi da yanayin daya ji kansa aciki, sakamakon rungumar da tayi masa ,ya sanya hannunsa yaɗan jayeta daga jikinsa, duban kyakkyawar fuskarta wanda gaba ɗaya ta ɓaci da hawaye yayi, ahankali cikin cool voice ɗinsa yace.
"Waya taɓaki? ko wani abu naki nayi miki ciwo ne? uhmmmm faɗamin kinji Amana." Yaƙare maganar cikin yanayin sanyi, harma da ɗan lumshe idanunsa.