Sashe 20
Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Adamcy na shiga ya rungume Hussy yana manna mata kiss ta ko ina yana sunsunata yana zuba mata godiya babu iyaka, Hussaina kuwa kumya ta cikata.
Ma'azzara ce shigo amman bata so tayi magana ya mata tsawa zuwa yanzu tsoron sa takeyi,dan baya mata sauƙi ga barazanar maidata gurin su Salamatu da yake yi in tayi mashi lefi, ita kuma batasan maganar komawar.
Doctor Farouq ya shiho yama Hussyn barka inda ita kuma Ma'azzara ta isa da sauri ta rungume Aunty Hussyn tana mata sannu ciki shagwaɓa, jikinta ne yabata ana kallanta ɗago kan da zatayi suka haɗa ido da doctor Farouq wanda tunda ya ganta a Office ɗinsa yake binta da mayen kallo sai a lokacin ma ta lura da jikinta sanye take da riga da siket ɗinkin sitaila kanta yasha ƙananan kitso shaɗe sai takalmi filet a ƙafarta bayan haka bakomi ajikinta domin tana ganin Adamcy ya sungumo Hussy batayi wata wata ba ta biyosu kuma dama shigar dake jikinta kennan sai kallabin data cillar kamar itace keyin nakudar sanda taga fitowarsu, dan sallah da tayi ma Adamcy ne ya amso mata hijab gurin nurse aro tana idarwa ya maida mata, da ƴar kunya ta ƙara shigewa jikin Hussy, Adamcy ya watsa mata mugun kallo, dan sai yanzu ya lura da yanda tazo hospital ɗin, mayafin Hussy gudan ya bata wanda Hadiza me aiki ta kawo, cikin rawar jiki ta masa ta yafa. bayan an kawo ma Hussy hadaddan tea tasha taci farfesun hanta Adamcy bai damu da mamah da kakanni su ba shida kansa ya temaka ma Hussy taba baby nono yana lallashinta, dole mamah ta fita tana murmushi, Ma'azzara kuwa wani irin abu takeji ga zufa na karyo mata duk da tna farin ciki amma wannan abinda Adamcy yake ma Aunty Hussy ya tsaye mata a rai, dole tabar kallonsu.
Sai dare aka sallame su bayan an duba beby da maman beby babu wata damuwa inda nan take aka basu sallama.
Bayan sun koma gida kuma granny lallah ce ta dawo nan gidan dan kula da ita.
masha Allah maijego da baby suna matuƙar samun kulawa daga ɓangarorin duka Adamcy ingari ya waye zaizo ya dau baby ya mata addu'a sannan ya koma kan maman baby ya tsotsi nan ya shafi nan ita kanta Hussyn tana jin daɗin kulawar dayake basu kwarai, tayi ta zuba masa sangarta idan ta kama taotsar bakinsa kuwa sai yaji yana son shiga wani hali yake tsayar da wasan, ganin haka granny lallah ta hanashi shigowa dan ta kamasu suna tsotse-tsotsen, haka kullum gidan cike da mutane yan barka ummee ma tazo.
Ranar suna anyi bajinta iya bajinta dan babu ce kawai ba a rababa agurin kuma kuɗine kawai ba a liƙawa ba pic ɗin beby aka raba amman robobi jakunkuna takalma manshafawa sa ili turare faka dosbin aasu ma ba Adamcyn bane yayi su saidai yagani abokansa sun mashi kara kwarai bama kamar Farouq daya ke jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya saboda tunda yaga Ma'azzara yaji shikam duniyar ga yayi matar aure.
beby tace sunan Ummu Saudat yarinya kyakyawa kamar ƴar larabawa danko su larabawan ba abinda zasu gwadawa bebyn, se Jiddah tayi sati kafin take juyawa Agadez Yaronta mai wayo sun shaƙu da Ma'azzara haka Adamcy duk inda zai shiga yana tare da Na'eem, Ummee tana nan ita ke kula da Hussy sai ta zubda ruwa.
A haka baby da momynta sukaci gaba da wanka Ma'azzara na kula dasu duk da kwana biyu nan mafarkin Adamcy ya adabeta se dai in bata kwanta ba gashi da zaran ta gansu da anty Hussy zataji kunci, abinda ya isheta take tambayar kawarta Nazifatu a school ta zaiyana mata kome akan abinda takeji game da uncle ɗinta, Nazifatu kuwa kasancewar ta girmi Ma'azzara gashi tasan kome akan soyayya sbd karatun novels ɗin hausa da take, nan take ta faɗama Ma'azzara cewar son uncle take ba so kaɗan ba... Ai kuwa ranar sai ɗa aka rabasu harda dambe tace me zatayi da mutumin da yake zaman uba gareta.... kuka ta rinƙa yi harda majina ai kuwa cikin sa'a Adamcy yazo ɗaukarta tana shiga mota ta kece masa da kuka ta rungumeshi ta faɗa masa abinda Nazifatu ta faɗa mata, wai yakai ƙaran Nazifar ta mata sharri kuma suna zuwa gida zata faɗama Aunty Hussy... nan Adamcy ya shiga mugun tashin hankali dan tabbas indai abinda ta faɗa gaskiya ne yo Amana sonsa take ba tare da ta sani ba, amma sai ya dake ya nuna mata karya Nazifa take kuma karta faɗawa antynta kuma karta kuskura ta sake faɗama kowa, da haka ya mata wayo ya lallasheta ya goge mata hawayen fuskarta ya biya ya sai mata ice cream, yana mai mugun jin tausayinta dan yasan abune ba mai yuwa ba...
Yau kam baƙo sukayi a gidan Farouq ne da kansa yazo dan gaskiya ya kasa daurewa tunda ya ɗora idanuwansa akan Ma'azzara shi kam ya kasa sukuni, hakan tasa yagayawa Adamcy be ɓoye mashi komi ba a ɓangaran Adamcyn yayi murna sosai dan tinda ya gano mahaukacin son da take masa, mutiƙar bai ɗauki mataki ba akwai matsala, shiyasa yayi gagawar aminta da Farouq dan yasan Farouq zai riƙeta amana kuma yana da komi na rayuwa wanda mace zataji daɗi agurinsa, hakan ma yasa Farouq ɗin tuntiɓar Adamcyn kan cewar yanaso yazo ya fara shigar da kansa inda Afamcy ya tabbatar mashi da cewar yaje dan shi ko baby Ummu zai iya bashi saboda ya yarda da nagartarsa.
To shi nefa yazo taɗin. Zaune take a porlour ta baje uwayan takardu sai home work takeyi bayanta goye da Ummu Saudat wadda masha Allah har sun kusa gama wanka kuma tayi girma fiye da tunanin mai karatu, Ma'azzara kanta tayi wani irin girma ta kara buɗewa tayi wani irin kyau na ban mamaki baƙinta ya washe ta ɗanyi haske.
Ummee ce ta safko take yiwa Ma'azzara magana ta daina goyo tana buduruwa zai cutar da ita ta sauke ta ta dinga saɓata kokuma rungumeta, iyaye mukula mudaina barin yaranmu nayawan yin goyo ya zubda nono kuma hakan na kawowa yaranmu naƙasa agurin maza in sunyi aure.
daidai nan Farouq ya fito daga cikin motarsa camrry 8+1 mai masifar kyau wata shadda ce a jikinshi ruwan zaiba sai walkiya take ɗinkin muhmmad Abacha yayinda yasanya hula itama dai ruwan zaibar zannah Bukar ta auna mashi tayi kyau, kamshin turaransa bag one sai tashi yake yana yawo a duniyar farfajiyar gidan siririn gilas ne a fuskarsa da ka ganshi kasan ya saba sawa, kuma ya dace dashi tafiya yake cikin kuzari da ka ganshi kinsan namijine mai lafiya da kuzari.
Yana isa ya kira Adamcy yace" to yayanmu na iso fa" Adamcy yace"freind gidan baƙonka ne to ?"ido ya lumshe ya ƙara buɗewa yace no. Friend but kasan wannan zuwan ya banbanta da irin wanda nakeyi a can baya yace" kashiga to nayi Hussy bayani." yanaɓfaɗin haka ya tsinke kiran yana lumshe manyan idanunsa masu ruwan zaiba yana tsotsar lips ɗinsa. Cikin farin ciki Farouq ya nufi cikin gidan.
Tunda Aunty Hussyn takira ta ciki dibara tace mata" Ma'azzara kingane doctor Faruq wanda aka kaini Hospital ɗinsa na haihu?" shuru tayi alamar tunani can kuma ta kalli Aunty Hussyn tace"eh Aunty nagane shi" Hussy tace" Ok to yanzu yana nan zuwa kuma gurinki zaizo inya tafi zan maki bayani amman idan yazo ki bashi kulawa kinji kuma banda shirme yanzu kije ki kai kujeru biyu Lambu sannan ki shiga kitchen ki duba abin taɓawa kikai masa ke kuma ki shirya sosai kiyi kwalliya shuru" Ma'azzara tayi inta fahimci Auntyn dai santa yake taɓ ita kam bata sansa. Ganin tayi shuru yasa Auntyn ta sake yi mata magana, da sauri ta tashi ta fita kitchen ta nufa kamar yadda Auntyn tabata umarni komi takai amman batayi kwalliya ba nan ma Aunty Hussyn ta biyo ta ta dinga lallaɓata inda ta zage ta caɓa mata kwalliya sosai cikin duguwar rigar shadda fich tasha blue ɗin aiki mai tsari turaruka ta fesa mata masu dai kamshi, haka Ummee ta mata maganganu da dibara irin wanda uwa keyi ƴarta dan in ganta lamurranta taɗan saki ranta amman dole wai saida Ummu zata gun zancan Ummee take faɗama Hussyn ce tace Ta barta suje tare ai gaskiya yarinyar naji da Ummu batasan rabuwa da ita kokaɗan...
itama bebyn anyi mata wanka da kwalliya cikin wasu lafiyayyun kaya tayi kyau ba ƙarya ga kamshi mai daɗi tana fitarwa .
Da sallama ta isa gurin Farouq ɗin inda tunda daga nesa yake addu'ar Allah sa da rabonsa domin komi da yakeso agurin mace yana hangoshi ga Ma'azzara itama tun daga nesa ta hango shi yayi matuƙar yin kyau a kan kujerar dake ajiye ƙarƙashin flawer's ɗin koba komi ya haɗu sai dai kash ita bataji komi ba game dashi, haka ta ƙarasa da sauri ya tashi ya amshi beby Ummu yana cewa"Sannu da isowa sarauniyar ruhin Umar Faoruq." itama ɗan murmushi ta mashi tana amsawa balefi taɗan yi wayau sunyi hira kamar masoya haka kuma yaya ba da girman Ummu shikam yana matuƙar kaunar Ma'azzara fatan da yake shine Allah mallaka mashi ita a matsayin matarsa ta sunnah, duk yaga akwai sauran yarinta a tare da ita amman zai koya mata sonshi nan kusa, tunta ya samu ɗaurin gindin Adamcy...