← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 29

Sashe 21

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Adamcy ne ya dukufa aiki yake yi sosai amman wayarsa ta dameshi da ruri wannan tasa ya ɗaga badan yaso ba dan ya share amman ba adaina kira ba, kuma bakuwar number ce, Picking ɗin call ɗin yayi amman sai yaji muryar Halliru ya mas aslm, Adamcy ya amsa ba wai dan ya gane shi bane, nna Halliru ya masa bayanin babban Ma'azzaea ne, inda yake shaida mashi yana so a basu Ma'azzara aure zasu mata.
Adamcy bai ce kome ba ya tsinke kiran ya kifa kansa smaan katon table ɗin ya lumshe idanunsa, dan yaji daɗin neman da suka mata,
shi kam ya godewa Allah da Farouq yace yana san auranta gara a mata auran itama ta kafa iyalinta tasami ƴancinta dan haka ya ɗaho da sauri! Ya danna number Hallirun, bugo ɗaya ya ɗaga, nan ya cewa Hallurun ya bari zasuyi magana yayi hakanne kawai dan bashi da lokacin sa bayaso yana ɓata lokacin sa a irin abubuwa marsa amfani...

Yau kam da wani irin mahaukacin ciwon mara da baya tatashi jitake kamar zata bakunci lahira da sauri Hussy dake jiyo kukanta ta nufi room ɗin Mu azzara, yadda taga bayanta da kugunta ariƙe da hannuwanta ga kuka tanayi jikinta ya jiƙe sharkaf da gumi itama sai ta ruɗe da sauri ta ɗaga wayar hannunta takira Adamcy inda yace" tasanar da get man yasa driver ya fito da mota sutafi Hosptal shima gashi nan zuwa su haɗu acan"

Hussainar kanta duk ta ruɗe haka suka kaita Hospital ɗin da Aunty Hussy ta haihu wato Hospital ɗin Faruq, daidai lokacin ya fito daga parmacy yana ƙoƙarin shiga teater room kawai ya hango car ɗin gidan Adamcy dan ya tabbatar ko suɗinne sai ya ƙara nufarsu yana zuwa kuwa yaga sune da sauri ya isa ganin Ma'azzara na murkususu yasa aka kawo mashi ɗan keken da ake ɗora marasa lafiya... Daidai lokacin Adamcy ya iso ɓai ɓari aka dorata akeken ba ya cicciɓeta ya rungumeta sukayi ciki da ita, inda Farouq yake nuna masa inda zasu shiga, emargency room nan Adamcy ya shiga da ita har gadon da Farouq ya nuna masa, ya kwantar da ita ta ko riƙeshi gam tana kiran "Uncle nah" Adamcy ya damƙe hannunta yana sauke ajiyar zuciya ya kura mata idanu.
Hussy ta rungume Adamcy tana hawaye, Ma'azzara tace"uncle nah kace Aunty tayi shiru uncle Farouq zai kula dani." Hannunsa ya janye cikin na Ma'azzara ya kama Hussy suka fita ya mashi ummu yana jijigawa, yanaɓriƙe da hannun Hussy ɗin.
Nan fa Farouq ya fara binci kar lafiyarta ranar tiyata ɗin da bai shiga ba kennan sai wani ya chanje shi.

Farouq ya jima yana ba Ma'azzara temakon gaggawa ya gano matsalarta inda yake ƙara yiwa Allah godiya dan hanyar mallakarta ta ruwan sanyi ta samu dan kuwa aure ne kawai zai rabata da wannan damuwar ɗin ,Knocking aka fara wanda already yasan Adamcy ne buɗe masa yayi ya shigo kallanta Adamcy yayi ya kalli Farouq yace" Freind meke damunta?"hannunsa ya kama suka fita kasancewar har lokacin barci take upstair's suka hau inda office ɗin Faruq yake takardun gwajin ya bashi, inda Adamcy ya hau dubawa take yagane waccan matsalar dai ce a hankali ya fesar da iska sannan yace "yanzu ya jikinnata?"Farouq yace "da sauƙi sai kuma ta tashi zamu gani" jinjina kai Adamcy yayi murmushi Farouq yayi yace "Freind kubani ita kawai kaga ta huta sai inbata magani shikennan ta rabu da period pain" ɗago kai Adamcy yayi ya kurawa Faoruq margic eyes ɗinsa yace"gaskiya kam hakan za ayi Freind nima in huta da matsalar yan uwanta , amma ka riƙemin ita Amana don girman Allah" ya faɗa yana rumtse idanunsa.

A hankali take juya idanuwanta wanda suka mata nauyi buɗesu take yi kaɗan-kaɗan harta buɗe duka karaf idanuwanta suka faɗa cikin na Farouq gabanta ya faɗi cikin dauriya take ƙoƙarin miƙewa guritan ya isa, ya kamata a hankali ya taimaka mata ta tashi inda kamshin turaransa ya doki ƙofofin hancinta ido ta rufe a hankali ta buɗe duk abinda take yana kallanta, da farko sai yaga kamar ba amshi tayinsa ba amman yanzu yana gaf da ƙaryata zarginsa domin duk saƙon da ya isar agareta yana lura amsa take.
hannu ya miƙa mata alamar tatashi miƙewa kuwa tayi ya kamta, direct toilet ɗin room ɗin suka shiga inda ya isa har gaban sink ɗin ya murza makunnar fanfan saban brch ya miƙa mata bayan ya ɓare amsa tayi tawanke whate teeth ɗinta dashi bayan tagama ya ƙara kamo hannunta suka fito.
Su Adamcy suka gani zaune yana rungume da ummu Hussy ta jingina da kanta kafaɗarsa.
Ma'azzara ta ƙura masu idanu saiɓkuma ta sadda kanta, bakin bed ya nuna mata ta isa ta zauna, Adamcy yace"Amana sannu ya jikin?" can ƙasan maƙoshi tace"da sauƙi Uncle "cikin sanyi murya.
Hussy tace" Sannu baɓynmu ga babynki tayi missing ɗinki jibi muke arba'in fa." Ma'azzara ta miƙe da niyar isa gun Hussy tana murmushin karfin hali, Adamcy yace" No koma zauna kici wani abun se ki amshi baɓynki." ba musu ta zauna tana sunne kai.
Samis ɗin shayin Farouq ya janyo ya zuba mata a cap haɗamata yayi inda yaji madara yana ta kamshin citta da kananfari amman baisa suger da yawaba, miƙewa yayi ya isa tsam kusa da ita ya zauna ya fara bata da farko ƙin amsa tayi saida Aunty Hussy ta mata alamar ta amsa da ido sannan ta amsa shikuma Adamcy saiji wani daɗi yake yayin da yaga dacewar ƴar amanar tasa da Farouq ido suka haɗa Faruq ya mai sigina yasamu shiga shi kuma ya galla masa hararar Wasa Hussy na masu dariya yayin da Ma'azzara hankalinta baya kansu tayi nisa a tunani....

Sorry babu Editing sosai ina busy Gsky😜

*Na kudi Ne kan farashi Nera 200 kacal +22792589446/ +27796515805*

*Daga Alƙalamin Real ladingo Sweet baby* uwa ga Fareesatu😘

*💖BANI DA GATA💖*

*MALLAKIN*
👇🏻
*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻

```Bani da gata ya koma na kudi, ya tashi daga gajeran labari, ya zaman tsayayyan labari, duk wanda ya zageni shida da Allah, ni de na maida bani da gata na kudi bisa wani kwakwaran dalili, idan kina bukata kisaya kisha karatunƙi kiga tsantsayar soyayya me ratsa zuciya, da kuma baɗa ƙala karku manta Hussaina nada ƴar uwa Hassanarta, wacce take egipt tana karatu, karku kuma manta Ma'azzara tayi nisa a son Adamcy wanda bata ma san tana sonshi ba, ga Farouq ya mutu akanta, kai wannan labarin bani da gata fa sai a slow yasin,idan ya miki zaki biya 200N kacal👌🏻 ki karanta ki kwashi karatunki cikin jin dadi da kwanciyar hankali😂😂😂Duk me buƙatar ci gaba zai neme ni ta wannan lambobin```
👉🏻 *+22796515805/ +22792589446* *💃🏻🤣TAKU CE HAR KULLUM REAL LADINGO INA SONKU SON SO FISABILILLAH 🤝🏻😍😂🤣*```kuku ma masu zagi kuyi tayi bani da lokacin ku, kanku akeji nagaba yayi gaba...```⛹🏻‍♀️

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Free Page*

*👉🏻 13*
Chapter 21 · 0% Book details