← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 29

Sashe 27

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kasa rage sautin kukan nata tayi, sannan batajin bakinta zai iya kaiwa ga motsi, har ta faɗa masa sirrin zuciyarta.
Ganin taƙicewa komaine ya sanya Adamsy, kamo hannunta, kujeran dake gefe ya jawo zuwa kusa dashi, akan kujeran ya zaunar da ita, cikin tsananin nuna  mata kulawa yace.
"Kidaina kukan nan haka, kin daisan banason yawan sakalci da sangarta ko, ki kalleni ki faɗamin meke damunki?."
Sam Ma'azzara ta kasa tsaida kukanta, domin ayanda takejin zuciyarta kukan ne kaɗai mafita, tana me tir da irin wannan zuciyar tata da addabeta akan uncle.
Ganin taƙi daina kukanne kana taƙi yin bayani, ya sanya Adamsy daka mata tsawa cikin faɗa yace.
"Ba tambayarki nakeyi bane? Meyasa bakya jin magana ne ke? Zakimin shirune ko sai na makeki yanzu anan!."
Jin tsawa da faɗansa yasa Ma'azzara shiga yanayin tsoro, amma hakan da yayi sai ya ƙara jefata acikin shauƙin yin kuka, hakan yasa ta ɗan ja baya da tashi tayi akan kujeran, da gudu ta juya inda take sake sakin sabon kuka ta nufi stairs don komawa ɗaki, gaba ɗaya sautin kukanta ya cika falon, sam ko lura da Hussaina dake tsaye tun ɗazu akan stairs ɗin tana kallo da jinsu batayi ba, gaba ɗaya idanunta sun cika da hawaye ko kallon gabanta sosai bata yi.
Jikin Hussaina ne yayi sanyi, da sauri takai hannu dan kamo Ma'zzara amma ina tuni Ma'azzara tayi mata nisa, don har takai ɗakinta.
Har ta gama haurawa steps din bai ɗauƙe idanunsa daga kanta ba, har saida ya daina ganinta, hannuwansa ya sanya inda ya rufe fuskarsa, sam bayason kukan Ma'azzara ko kaɗan, yana jin kukan nata har acikin zuciyarsa.
Abinci yake da niyar ci, amma hakanan yaji gaba ɗaya abincin yafita daga ran shi, ko yunwar ma yaji ya daina jinta, daman baici na rana ba, miƙewa yayi daga zaunen da yake, da sauri ya ɗauki ummu Saudat ya rungumeta ya nufi bedroom ɗinsa yana shiga ya rufo ƙofar,  da kallon mamaki Hussaina ta bisa, ta fahimci cewa sam baima ganta ba, ahankali ta gama sauƙowa daga kan step ɗin, kaitsaye ɗakinta dake ƙasa ta nufa.

Adamsy na shiga cikin ɗakin ya faɗa kan gado, ya dora ummu kirjinsa, a hankali ya lumshe idanunsa, yana mejin wasu irin abubuwa na yawo ajikinsa, karon farko kenan da yaji wani abu ajikinsa, sakamon rungumarsa da Ma'azzara tayi, sannan hakanan yaji zuciyarsa tayi masa zafi sosai da ganin hawayenta, wani irin haushin kansa ne duk yabi ya lulluɓesa sakamakon tunawa da irin yanda ya ɗaga mata murya,  har yanzun sautin kukanta ne ke yawo acikin kunnensa, rumtse idanunsa yayi da ƙarfi, sakamakon tunawa da yayi cewar itaɗin Amana ce agaresa, sam kome tayi bata cancanci tsawa irin wanda yayi mata ba, wani irin yarrr haka yaji ajikinsa sakamakon tunawa da yanda ta shige cikin jikinsa da yayi, wani irin ɗumi na musamman yaji ajikinsa,  da sauri ya kawar da wannan tunanin daga mine ɗinsa, tashi zaune yayi, ahankali yaji zuciyarsa na tsananta bugawa, yayin da yake jin ƙirjinsa yayi masa nauyi kamar zai faɗo,  lumshe idanunsa yayi tare da sanya hannu ya dafe daidai saitin zuciyarsa,  ko kaɗan baya fatan abun da zai tarwatsa rayuwa da jin daɗinsa, baya son gaskata tunaninsa,  sosai yake jin tsoron sabuwar ƙaddaran dake shirin zuwar masa batare daya shiryawa hakan ba, tabbas idan abunda yakeji azuciyarsa ya zamanto gaskiya baisan ya zaiyi da rayuwarsa ba, menene matsayinsa kenan?   Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya tafukan hannuwansa ya dafe kansa, tabbas yasan SO yakuma san alamominsa, saidai kuma yana jin tsoron Soyayyar Ma'azzara da ta jima tanacin ƙasan zuciyarsa batare daya sani ba, saidai kuma wani lokaci yakan ji cewa ba soyayya bace, kawai tausayinta yake ji domin itaɗin ta kasance Amana ne agareshi.
Duban agogo yayi yaga ƙarfe 6 hadda rabi, hakan yasa shi kwantar da ummu wacce take ta halba ƙafafunta tana zullo harshe waje, ya shiga toilet ya ɗauro alwala,  yana fitowa daga cikin toilet ɗin Hussaina na shigowa, sosai tayi kyau cikin shigar doguwar rigan dake jikinta, dubanta yayi tare da ɗan sakar mata murmushi, itama murmushin tayi masa, ahankali tashiga takowa zuwa garesa, saida ta kawo daf dashi kafun ta tsaya, shagwaɓe fuska tayi tare dayi masa kallon tsantsar so, akasalance tace "Mon trésor masallaci zakajene?."

Kansa ya gyaɗa mata alamar "Eh." murmushi tayi tare da jinjina kanta, so take tayi masa magana akan abun da yayiwa Ma'azzara sam baidace ba, amma kuma wani abu da zuciyarta ke faɗa mata yasanya ta yin shiru, so take tagaskata tunaninta akansa, saboda haka zata ƙyaleshi kawai,  matsowa kusa da ita yayi inda ya manna mata kiss akan goshinta, Ummu ta ɗauko, tana kissing ɗinta Adamcy ya kama hannunta suka fice daga cikin ɗakin,  suna zuwa falo ya saketa, inda ya fice daga gidan gaba ɗaya, itama ɗakinta ta koma danyin nata sallah'n.

Ma'azzara kuwa koda ta koma ɗakinta, kuka ta cigaba dayi mai tsananin taɓa zuciya, tayi kuka sosai har saida taji kanta nayi mata ciwo, lokaci ɗaya idanunta sukayi luhu luhu dasu,  sosai takejin wani irin azababben kewa na game gaba ɗaya ilahirin jikinta, shiga jikinsa da tayi yasa ta shaƙo daddaɗan ƙamshinsa, wanda ako da yaushe ke ƙara hura mata wutar so da sha'awarsa,  sosai tsawan da yayi mata ya taɓa zuciyarta, hakan yasa taƙara narkewa  tare da jin cewa tarasa madafa,  taso ace ya fahimceta amma me yasa yakasa fahimtar ta, tayi alkawali daga yau zata kama kanta, ko mafarkin ma da tanada damar hanashi zuwara mata da tayi, tayi alkawalin ko zata rasa ranta bazata ci Amanar Aunty Hussy ba, ko maza sun ƙara wlh bazata taɓa yarda Hussy taga son mijinta a idanunta ba, ko shi kansa daga yau bazai sake gani ba, sosai yunwa ke ƙwaƙulan cikinta amma hakanan taji abincin ma yafita aranta, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne ya sanyata tashi ta ɗauro alwala, koda tayi sallan magriba bata tashi akan sallayan ba nan tazauna tanajiran aƙira sallan isha tayi....

************** ******** **************
Bayan sati ɗaya

Garin Audarass

Acan garin na Audarass kuwa yau Ummee ta kawo masu ziyara, bayan ta kwashi hutun kwana goma A garin na Agade, ta isa lafiya, inda ta shirya da kanta tanufi gidan Salamatu don isar da saƙon da Farouq ya bata.
Tun daga zauren gidan taketa kwaɗa sallama amman babu wanda ya amsata saima hayaniya da masifan da takeji na tashi acikin gidan, tun daga cikin zauren taji wani irin ƙara irin na tusa marar daɗin ji, tuni ma kafun taƙarasa shigowa gidan masifaffen warin na tusa ya ziyartota, da sauri ta sanya mayafinta ta toshe hancinta, kana ta ƙarasa kutsawa cikin gidan, Salamatu ta hango atsakiyar gidan ita da wata mata sai dakuwa suke, yayinda Halliru da kuma Malam Musa ke ta ƙoƙarin rabasu amma sun kasa, tuni zanin Salamatu ya faɗi ƙasa, babu abun da kake hangowa sai wani macaccen buje wanda yaci uban datti,😹 saboda tsabar dattin dayake dashi har baka iya tantance wani kala gareshi, uwa uba jikinsa kota ina jurwaye ne, ba abun dake tashi ajikin bujen sai tsamin tsiya.🙊
Cikin ƙarfin hali irin na Salamatu ta kamo kan Kaltume me adashe,wanda da itane suke faɗan, duk dan wai akan tazo kan maganar adashe, don ankwana biyu Salamatun batayi zubi ba, shine tabiyo jin dalili daganan kuma faɗa ta kaure tsakaninsu, kasancewar dukansu masifaffun mata ne kuma sam basuda haƙuri. Cikin ƙarfin hali irin na Salamatu ta kada Kaltume mai adashe, nanfa ta ɗale kan Kaltumen inda ta kamo kan Kaltumen ta nannaɗe cikin bujenta,  wani irin ihu haɗi da kururuwan neman taimako Kaltume ta shiga yi, inda take cewa.
"Wayyo Allah Na jama'a kutaimakeni, zata kasheni da wannan fitinannen warin bujen nata, nashiga uku wani irin buje ne wannan?." Tuni maganan Kaltume ya maƙale sakamakon wata ƙatuwar tusa da Salamatu ta sake, wayyo Allah tuni ɗaci yacika maƙoshin Kaltume mai adashe, yayin da warin tusan yakusa zautar da ita, cikin gajiya haɗi da tsananin neman taimako,  tace. "Don girman Allah Malam Musa ka ceceni, zata kasheni wayyo Allah na wannan wani irin masifaffen warine mai kama da guba, wallahi wannan warin na buje da tusan yamafi guba illa." Tarine ya sarƙeta don kuwa tuni cikinta harya fara wuntsulawa, sakamakon wari da tsami.
Chapter 27 · 0% Book details