← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 29

Sashe 18

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sun girma sun kammala karatun su Rukaiyya tayi aure a Naimey, inda ta auri me kuɗin gaske, shekarata biyu da aure Fawwad shima yay aure auran soyayya me zafin gaske shida ummee, sai dai ba a gari suke ba suna can kauyan Agadez Audarass, wanda duk faɗin Agadez ba wanda bai san da suba wajan kudi a kauyen Agadez, ummee macace buzuwa kyakyawa ajin ƙarshe a kyau, gasu da kudi suma ga kyau ita da Fawwad biyu ce ta hadu. Saida suka shekara biyu da aure Allah ya bata ciki, bayan wata tara ta haifo yan biyu kyawawa masu kama da Fawwad sak, turawa sak mace da namiji faɗin murna wajan Muhammed da lallah tamkar ba jikoki ba, liyafa suka haɗa ta musamman, gidansu ummee ma haka abin yake hajja Nini mahaifiyar ummee a can Audarass ta tara jama'a anci an sha.
Bayan shekaru biyar da haihuwar su Adam da Hauwa'u aka saka su A school ta ƴaƴan wane da wane, lokacin shekarun Hassana da Hussaina ƴaƴan Rukaiyya biyu a duniya, kanwar baban su Adamcy, wanda mahaifinsu Mustapah mukutar ya ɗora masu san duniya.

Tin Adamcy na yaro zaka san cewar ba karamin miskili bane na bugawa a jarida, sai de akwai maida hankali wajan karatun islamiyya da boko, saida suka shekara goma cif aka haifi Adiya kanwarsu, me shegen ɓacin tsiya da sangarta, shiyasa Adamcy baya yinta, Jiddah ce kawarsa baya da aboki bare a bokiya, tare suke karatunsu, ajininsu ɗaya ba a taɓa banbanta masu kome ba, sai bayan gama secondry school ɗin su ne yay aboki Farouq to shine abokin sa har yanzu dan tare suka je Naimey suka shiga University wanda a lokacin ne soyayya me karfi ta kullu tsakanin Hussaina da Admcy amma sun maida hankali kan katatunsu ,dan lokacin tana secondry bata gama ba, akayi rashin sa'a Hassanar hussaina duk duniya ba wanda take so bayan Adamcy, sai de ta boye hakan ganin ba ita ake so ba asali ma ita karatu ne gabanta ba kamar Hussaina ba wacce tace tana gama secondry bazata ci gaba ba...

Bayan Adamcy ya gama karatunsa wanda ya karanci fannin Bank da kuma business ya sake tafiya Canada yay shekara ɗaya ya dawo lokacin ya bijiru da maganar auran Hussaina ɗingi sunyi na'am da auran zumunci zai ƙaru Muhammed kakansu yafi kowa murna, duk sunaga Adamcy yayi zafin cewa zaiyi aure, sai de kashhh kana naka Allah na nashi ana gobe ɗaurin aurensu Adamcy da Hauwa'u dan rana ɗaya aka saka auransu, sunce ɗaya bazai aure yabar faya ba, Allah yasa tanada masoyinta..
Fawwad yana fitowa daga wajan aiki sai murna yake gobe zai aurar da yaransa yan biyu, babbar mota tabi kansa yana cikin ƙaramar motarsa yana driving, ai faɗar tashin hankali a garin Agadez ba a cewa kome mutuwar ta girgiza jama'a Admacy kusan hauka yayi dan kwanan sa uku baisan inda kansa yake ba, haka ummee ma lallah da Muhammed sun shiga tashin hankali mafi muni, dole aka ɗaga auran sai da kome ya lafa akayi sadakar arba'in su Hussaina tunda suka zo gun mutuwa basu koma ba sai bayan an ɗaura auran dan ba ayi biki ba Adamcy yace baya buƙata, haka Jiddah ma gidanta kawai aka kaita, haka dai akayi abu ba dadi abin tausayi sun zama marayu sai kakanin su masu sonsu...
Bayan sun koma Naimey Adamcy ya tare a tamfatsetsan gidansa da Fawwad ya gina masa a Plateau suka tare da Hussaina wanda daket ta samu ya sake har ya fara fita aiki lokacin ana tsakiyar gina masa companyn sa ga aikin bank da yake, masha Allahu a sannu a sannu suke zuba soyayya mai tsayawa a zuciya kasancewar Hussaina macace mai nutsuwa da tarbiya da hakuri sona son juna kamar zasu ci juna ɗanye koda yaushe basa gajiya da junasu sai de idan baya gida kawai. Hassana sai bayan mutuwar da wata uku tazo daga Egipt tayi gaisuwa dan suna cikin karatu sosai, ba damar tahowa sai da suka sami hutu watan ta ɗaya ta koma.
Adamcy yana ba Hussaina kulawa sosai duk wata uku sai sunzo duba ummee dasu lallah. Da haka har suka shekara da aure lokacin an gama gina kamfanin Adamcy an kama aiki tuburan kuma lokacin Muhammed da matarsa suka koma Naimey da zama kusan jikokinsu, lokacin ne Hussaina take fama da laulayi dan dai ba sosai ba a kwai lokacin da dole ya zauna ya hakura da fita yay jinyar bebensa, har Allah ya bata ɗan sauƙi ita ce take matsa masa da ya fita ana fa buƙatarsa a wajan aiki, kiyawa yay sai ɗa ya roki lallah tazo tana wuni tikun ya fara fita, cikin ya shiga wata uku ne Nini ta rasu mahaifiyar Ummee shine suka shigo jirgi suka zo Agadez daga nan suka shiga mota suka nufo Audarass wanda suna shigowa suka ci karo da Ma'azzara...

Wannan shine cikaken tarihin su Adamcy,

*Wacece Ma'azzara*

Sa'ad Sahabi Nazir ould shine cikeken sunan mahaifin Ma'azzara, Sahabi Nazir ould baƙin buzu ne, kyawawa sosai sai de Allah bai masu arziki ba, amma yana ƙoƙarin ya farantama iyalinsa, matansa biyu uwar gida karima sai amarya Agaishina, yaran Sahabi hudu rak a duniya Kabiru wanda ake cema haliru, sai Salamatu sai Fauziyya wacce ta fita daban dan ba ruwanta yarinyar sune ƴaƴan karima, sai Sa'ad auta shine ɗan Agaishina, karima baƙin kishine da ita na masifa, Agaishina tana shan wuya hannunta ga salamatu da shegen baƙin jinin tsiya tin tana karama saboda baƙin halinta irin na uwarta, haka dai tafiyar tayi tafiya har yaran suka girma sukayi aure inda Fauziyya tayi aure a tahoua salamatu kuwa saboda tusar tsiya daket ta sami malam musa ya kwasa.. Bayan auransu da kusan shekaru biyar tikun Sa'ad shima ya sami Sa'adatu ƴar makwabtan su ce suma masu fita neman abinda zasuci ne babanta ya rasu sai mamanta suka kulla soyayya mai tsanani bayan auransu da sati uku mahaifiyar Sa'a ta rasu ta shiga tashin hankali Agaishina ita take kwantar mata da hankali ta kuma riƙeta kamar ƴarta, karima an sami abin habaici da gori amma Agaishina ko kallo bata isheta ba sabgar gabanta take. Bayan shekara ɗaya da auran su Sa'a ta sami ciki murna wajan Sa'ad ba a magana da Agaishina da Sahabi.
Akwana a tashi Allah ya sauketa lafiya ta sami ɗiyarta zankaɗeɗiya kyakywa baƙa mai farin jini abin ba cewa kome Ranar suna taci sunan *Ma'azzara* Ma'azzara ta taso cikin gata da kulawa Sa'ad na ƙoƙarin bata tarbiya sosai, saboda tin daga kanta Sa'a bata kuma haihuwa ba da ta sami ciki sai ya zube. Ma'azzara kyakywace ajin karshe mai diri da surah, ta taso da sangarta akwaita tsokana da faɗa kusan kullum sai an kai iyayanta gidan megari ƙara, karima tayi ta masu gori Sa'a tayi ta mata nasiya tana gaya mata lillar abinda take idan suka mutu wuya zata sha ta bari, da irin wannan nasihar ta mahaifiyarta yasa ta rage rashin ji ta maida hankalinta da karatun islamiyya da boko...

Kwatsam ana cikin haka Sahabi ya kwanta dama, Sa'ad ya shiga tashin hankali shi da Agaishana dan abun kansu zai ƙare.
abinda ya idar da hargitsa gidan baki ɗaya dan bayan Arba'in suka ce ayi rabon gado ɗaki ɗaya suka basu Sa'ad ya ce Agaishana ta zauna shi zai nemi haya da matarsa da ƴarsa, Agaishina taki taje ta siyar da raƙuminta ɗaya da ya rage ta sami dan filinta tasa aka gina mata ɗaki ɗaya da soron kofa guda tace abata Ma'azzara aka bata suke zaune abinsu, idan ba school ko islamiyya tare suke zuwa tallar maganin zafi kuma suna samun kudi sosai suna rufawa kansu a siri har ma dasu Sa'a...

Kwatsam watarana aka aiko surikin Fauziyya ya rasu Sa'ad da karima da Sa'a sune suka tafi Tahoua gun gaisuwa salamatu tace bazata ba kuɗin mota tsada ita matar malam ce ta kira a waya tayi gaisuwa. Haliru kuwa cewa yayi baya da kudi.
Kwanan su uku suka juyo zasu dawo wanda aka cika su da abin arziki anan ne mai afkuwa ta afku Bus ɗin da suka shigo tayi hatsari kusan mutum goma suka rasu ciki harda Sa'a da Sa'ad da Karima dan ko shurawa basu yiba.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!
Wannan mutuwar ta girgiza jama'a Ma'azzara kusan haukacewa tayi Agaishana kuwa ba a cewa kome sai godiyar Allah, salamatu tayi sanyi ta rinƙa saka Ma'azzara ajiki wai tausayinta take yanzu amma kafin ake arbain har ta manta har an koma ƴar gidan jiya, sai kyama da tsamgwama daket Agaishina ta daure akayi arbain suka ɗauki duk wani abu mai ɗan kyau zasu bar gidan su koma can gidan ta, Salamatu da Haliru suka hana suka ce kayan ɗan uwansu ne gaisha tace iya ko da ta haifesa fa nan Ma'azzara tace a barsu da Allah su tafi haka ko suka bar gidan suka koma can gidansu na da...
Chapter 18 · 0% Book details